blank

Inside VOA | Tuntube Mu

05/21/2012Laifin Bayern Munich Ne – Ba Gwanintar Chelsea Ba

Anatoliy Tymoshchuk na Bayern Munich, a tsakiya, tare da sauran 'yan kungiyar cike da bakin ciki a bayan da Didier Drogba ya buga fenaritin da ya ba Chelsea kofin zakarun kulob-kulob na Turai a Munich, asabar 19 Mayu 2012.

Anatoliy Tymoshchuk na Bayern Munich, a tsakiya, tare da sauran 'yan kungiyar cike da bakin ciki a bayan da Didier Drogba ya buga fenaritin da ya ba Chelsea kofin zakarun kulob-kulob na Turai a Munich, asabar 19 Mayu 2012.


Dan tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa zai buga.
Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta kasar Jamus ita ta jefa kanta cikin ukubar bakin ciki da radadin zuciya, bayan da ta watsar da babbar damar da ta samu ta yin abin tarihi a gasar cin kofin zakarun Turai, kuma a cikin filin wasanta, a gaban magoya bayanta.
Bayern ta yi sakaci ta bar Chelsea ta rama kwallo ana saura minti biyu rak a tashi, sannan ta jefar da bugun fenariti a lokacin da aka yi karin lokaci, ta kuma zo ta jefar da wasu fenaritin guda biyu, ta bar kofin ya sulale daga hannunta.
Wannan lamarin ya faru ne a filin wasan ‘yan Bayern Munich, watau Allianz Arena, wanda aka zaba don buga wannan wasa fiye da shekara guda da ta shige, tun ma ba a san ko su wanene zasu buga ba. Idan da Bayern ta yi nasara, to da ta zamo kungiyar farko da zata lashe kofin zakarun kulob na Turai a cikin filin wasanta. Tun da aka kirkiro wannan gasa shekaru 20 da suka shige, babu kungiyar da ta taba yi.
Roberto Di Matteo na Chelsea yace, “idan wasa yayi zafi, komai na iya faruwa, tilas ka matsa lamba a kan abokiyar karawarku don ka ga abinda zai faru.”
Kowa ya san kungiyoyin kasar Jamus a zaman babu wanda ya kai su juriya da daukar matsi ba tare da nuna zafin kai ba. Kai, ba a taba doke kungiyar kwallon kafa ta kasar Jamus a bugun fenariti ba yau fiye da shekaru 30.
Amma ‘yan kungiyar Bayern sun karaya a lokacin da bai kamata su karaya ba. Kada a mance kungiyar ta yi hasarar kofin wasannin lig-lig na Bundesliga, da kuma kofin kalubalenka na kasar jamus. Ga na Turai ma ya sullube mata, a gaban magoya bayanta, a filinta, a garinta, kuma a kasarta.
'Yan wasan Chelsea su na fareti, yayin da Didier drogba ke rike da kofin zakarun kulob-kulob na Turai, bayan da suka doke Bayern Munich ranar asabar.

'Yan wasan Chelsea su na fareti, yayin da Didier drogba ke rike da kofin zakarun kulob-kulob na Turai, bayan da suka doke Bayern Munich ranar asabar.


ba dai zan cika ku da surutu ba. A karshe, haka ‘yan wasan Bayern suka zube a kasa, su na cikin tsananin bakin ciki da kukar zuci, ganin yadda wannan kofi ya shiga hannunsu ya sullube tun kafin su rike shi.

05/13/2012Manchester City Ta Tsamo Kitse A Wuta

'Yan wasan Manchester City su na murna dauke da kofin zakarun wasannin lig-lig na kasar Ingila, bayan da suka doke Queens Park Rangers, yau lahadi 13 Mayu 2012.

'Yan wasan Manchester City su na murna dauke da kofin zakarun wasannin lig-lig na kasar Ingila, bayan da suka doke Queens Park Rangers, yau lahadi 13 Mayu 2012.


Magoya bayan kungiyar Manchester City sun fara kuka, duniya ta rikice musu ana dab da tashi daga wasan da suka yi da Queens Park Rangers a filin wasa na Etihad dake birnin Manchester.
A can Sunderland kuwa, magoya bayan Manchester United sai murna suke yi, ‘yan wasansu kuma har sun fara layi su na jiran a zo a mika musu kofin zakarun wasannin lig-lig na Premier.
A daidai lokacin, kungiyar Queens Park Rangers tana gaban Manchester City da ci 2-1. Kuma idan aka tashi a haka, mafarkin Manchester City na lashe kofin lig a bana, sai dai a mafarkin kawai.
Amma mutum yana nasa, Allah Yana nasa. Babu wanda ya san cewa a she a cikin mintoci 5 da aka kara na bata lokaci, manchester City zata jefa kwallaye har guda biyu, zata lashe wannan wasa, kuma reshe zai juya da mujiya: magoya bayanta za su barke da murna, yayin da magoya bayan United za su shiga cikin bakin ciki.
Da farko dai Edin Dzeko ya jefa kwallo da kai a lokacin bugun kwana, daga nan kuma ana saura dakikoki kadan a hura tashi baki daya sai Sergio Aguero, surukin Maradona, ya jefa kwallon da watakila a duk rayuwarsa bai taba jefa mai muhimmancin wannan ba. Ga ‘yan City dai wannan kwallon ya fiye musu komai a duniya a yau din nan.
Jefa wannan kwallo ke da wuya sai aka hura tashi, fili ya rikice, duniya ta koma fari fat ga ‘yan City, yayin da ta yi duhu wuluk ga ‘yan United har ma da ‘yan wasan United da manajansu Sir Alex Ferguson, wadanda shirinsu na amsar wannan kofi ya koma mamaki mai tsanani na yadda aka yi har City ta komo ta lashe wannan kwallo nata da QPR.
Wannan shi ne karon farko da City ta lashe kofin wasannin lig-lig na Ingila a cikin shekaru 44. Tun ma da wasannin suka koma Premier League, ba ta taba lashewa ba, kullum sai dai ta kalli makwabtanta ‘yan United su na murna.

Wannan rana ce mai muhimmanci ga manajan ‘yan Manchester City, Roberto Mancini, wanda aka yi ta rade-radin cewa masu kungiyar larabawa zasu kore shi idan ba su lashe kofin nan ba. Dalili shi ne irin makudan kudaden da suka kashe kan kungiyar domin farfado da ita.
Da ma kwararru suka ce lashe kofin farko shi ne mawuyaci, kamar yadda ‘yan City suka gani. Watakila na biyu da na ukun su na iya zuwa da sauki fiye da yadda suka gani a bana.
Manajan Manchester City, Roberto Mancini, rike da kofin zakarun wasannin lig-lig na English Premier da 'yan wasansa suka lashe yau lahadi, 13 Mayu 2012 a filin wasa na Etihad dake Manchester.

Manajan Manchester City, Roberto Mancini, rike da kofin zakarun wasannin lig-lig na English Premier da 'yan wasansa suka lashe yau lahadi, 13 Mayu 2012 a filin wasa na Etihad dake Manchester.

05/ 8/2012Up Yaya Toure – Sir Alex Ferguson Ma Ya Mika Wuya, Ko Kusan Hakan

Yaya Toure na Manchester City yana murnar daya daga cikin kwallaye biyu da ya jefa a ragar 'yan wasan Newcastle United a wasan da suka buga ranar lahadi, 6 Mayu, 2012 a filin wasa na Sports Direct Arena, Newcastle, wanda ya gusar da City ga lashe kofin lig-lig na EPL na 2012.

Yaya Toure na Manchester City yana murnar daya daga cikin kwallaye biyu da ya jefa a ragar 'yan wasan Newcastle United a wasan da suka buga ranar lahadi, 6 Mayu, 2012 a filin wasa na Sports Direct Arena, Newcastle, wanda ya gusar da City ga lashe kofin lig-lig na EPL na 2012.

Idan ba wata kaddara daga Ubangiji ba, babu abinda zai hana Manchester City doke Manchester United wajen lashe kofin wasannin lig-lig na bana a kasar Ingila.
Shi kansa manajan United, Sir Alex Ferguson, cewa yayi, “watakila hannayensu biyu na kan wannan kofi a yanzu haka.”
Tauraron ‘yan wasan Manchester City shi ne Yaya Toure, wanda a ranar lahadi 6 Mayu 2012, ya jefa kwallaye har biyu a ragar ‘yan wasan kungiyar Newcastle United, ya kawar da duk wata tababar da ake yi cewa bana taurarin City ne suke haskakawa.
Yanzu abinda ya rage kawai shi ne City ta doke kungiyar Queens Park Rangers wadda ke can baya a wasan karshe da zata buga ranar lahadi mai zuwa. Idan ta yi haka, zata lashe kofinta na farko tun 1968.
Idan City ta doke QPR, to United zata bukaci lashe wasanta na karshe da ‘yan Sunderland da ci 9 da babu, domin ta kawar da yawan kwallayen da City ke da shi a ragar abokan karawarta, abinda ake ganin zai yi wuya.
Hausawa suka ce ba a san ma ci tuwo ba sai miya ta kare.

 

05/ 7/2012Allah Ya Jikan Rashid Yekini, Mun Yi Rashi

Rashid Yekini, lokacin da ya jefa ma Najeriya kwallonta na farko a gasar cin kofin duniya a 1994.

Rashid Yekini, lokacin da ya jefa ma Najeriya kwallonta na farko a gasar cin kofin duniya a 1994.


Duk wani masoyin Najeriya da kwallon kafa a Najeriya da Afirka, ba zai taba mantawa da Rashid Yekini ba.
Rashid Yekini, ya rasu ranar jumma’a a Ibadan, yana da shekaru 48 da haihuwa.
Babu wani dan kwallon da ya taba jefa ma Najeriya kwallaye kamarsa, inda a cikin wasanni 58 da ya buga ma kungiyar Super Eagles, ya jefa kwallaye har 37.
Amma babban abinda mutane suka fi tunawa a game da Rashid Yekini, wanda aka haifa ranar 23 ga watan Oktoba, 1963 a Kaduna, shi ne irin rugawa da gudun da yayi ya shiga cikin ragar ‘yan kasar Bulgariya, ya rike raga yana ihu da iyakar karfinsa, a bayan da ya jefa ma Najeriya kwallonta na farko a gasar cin kofin kwallon kafar duniya a 1994 a Amurka.
haka kuma, Rashid Yekini, shi ne dan Najeriya na farko da aka taba zaba a matsayin zakaran kwallon kafa na nahiyar Afirka a 1993, kuma shekara daya bayan wannan, ya taimakawa ‘yan Super Eagles na Najeriya suka ciwo kofin zakarun kasashen Afirka.
Shi ne dan wasan da ya fi jefa kwallaye cikin raga a wasannin lig-lig na kasar Portugal a 1993-1994 a lokacin da yake buga wasa ma kungiyar Vitoria Setubal. A shekaru 4 da yayi a wannan kulob, Rashid Yekini ya jefa kwallaye 90 cikin raga.
Yayi wasa a kasashe da dama kafin ya zo yayi ritaya a kungiyar Julius Berger ta Najeriya a 2003.
A bayan fage, Rashid Yekini mutum ne mai shiru-shiru, wanda bai cika shiga harkar da ba tasa ba. Abin koyi ga kowa.
Allah Ya jikan Rashid Yekini, Ya sa mutuwa hutu ne gare shi, amin summa amin.
Marigayi Rashid Yekini

Marigayi Rashid Yekini

05/ 3/2012Real Madrid Ta Zamo Zakarar Spain A Bana

Wani mai goyon bayan kungiyar Real Madrid dauke da kyalle mai cewa "Zakarun 2011-2012" a bayan da kungiyarsa ta zamo zakarar rukunin lig-lig na kasar Spain, La Liga, bayan ta doke Athletic Bilbao a filin wasa na San Mames dake Bilbao, laraba 2 Mayu 2012.

Wani mai goyon bayan kungiyar Real Madrid dauke da kyalle mai cewa "Zakarun 2011-2012" a bayan da kungiyarsa ta zamo zakarar rukunin lig-lig na kasar Spain, La Liga, bayan ta doke Athletic Bilbao a filin wasa na San Mames dake Bilbao, laraba 2 Mayu 2012.


Real Madrid ta zamo zakarar wasannin rukunin lig-lig na kasar Spain, La Liga, a karon farko cikin shekaru 4, ta kawo karshen mulkin babbar abokiyar adawarta FC Barcelona, bayan da ta doke Athletic Bilbao da ci 3-0 laraba.
Gonzalo Higuain da Mesut Ozil da kuma Cristiano Ronaldo sune suka jefa kwallaye ukun da suka ba kwac na Real, Jose Mourinho, damar lashe kambi har guda hudu a kasashe dabam-dabam har guda hudu, abinda babu wani manajan da ya taba yi.
Real Madrid ta samu nasarar ce duk da cewa har yanzu da sauran wasanni biyu kafin a kawo karshen kakar wasannin lig na bana.
Wannan shi ne kambin farko da Mourinho ya lashe a kasar Spain a shekararsa ta biyu a Real Madrid, kuma shi ya kawo karshen mulkin shekaru uku da FC Barcelona take yi da wannan kambi.
A bayan wasan na jiya laraba, ‘yan wasa da masu koyar da su, ciki har da Mourinho, sun tattaru a filin wasa na San Mames su na murna. Mutanen Bilbabo ba su taba ganin baki sun zo daga wani wuri sun yi murnar lashe rukunin lig-lig na Spain a filin wasansu ba.
Kyaftin na Real madrid, Iker Casillas, ya fada bayan da aka hura tashi daga wasa cewa, “Wannan kakar kwallo doguwa ce, amma daga karshe mun samu nasara. Ina fata wannan shi ne karon farko da zamu dauki wannan kofi da ‘yan wasanmu matasa na yanzu….”
Kwach na Real Madrid, Jose Mourinho, da 'yan wasansa su na murna a filin wasa na Athletic Bilbao a bayan da suka zamo zakarun wasannin lig-lig na kasar Spain na bana.

Kwach na Real Madrid, Jose Mourinho, da 'yan wasansa su na murna a filin wasa na Athletic Bilbao a bayan da suka zamo zakarun wasannin lig-lig na kasar Spain na bana.


“Wannan gagarumin kambi en a gare mu, domin babu wanda ya dauka zamu yi wani abu duk tsawon shekara, duk abinda muka samu, sai da muka tashi muka nemo da kanmu, ‘yan wasanmu sun yi kokari ainun, kuma sun cancanci wannan,” in ji Mourinho.
Ya ci gaba da cewa, “na lashe irin wannan kambi a can baya a Portugal, da Italiya da Ingila, amma wannan ya fi duk sauran wahala. Ina jin cewa ko su ‘yan Barca (FC Barcelona) sun san cewa mun cancanci lashe wannan kambi a bana.”

05/ 1/2012Manchester City, Zakara?

Magoya bayan kungiyar Manchester City sanye da kalar kungiyarsu a lokacin karawar da ta yi da abokiyar adawarta Manchester United, litinin 30 Afrilu 2012 a filin wasa na Etihad dake birnin Manchester. City ta lashe wasan da ci 1-0.

Magoya bayan kungiyar Manchester City sanye da kalar kungiyarsu a lokacin karawar da ta yi da abokiyar adawarta Manchester United, litinin 30 Afrilu 2012 a filin wasa na Etihad dake birnin Manchester. City ta lashe wasan da ci 1-0.


Marubucin tamaula Martin Rogers yace ba wai an nada sabon zakaran lig-lig na kasar Ingila ne a karawar da aka yi litinin a tsakanin Manchester City da Manchester United ba, amma duk wanda ya kalli wasan zai ga kamar abinda aka yi ke nan.
dalili shi ne wadannan kungiyoyi biyu sune ke sama a rukunin na Premier League na Ingila.
Nasarar da Manchester City ta samu da ci 1 da babu a kan Manchester United, tamkar wata ni’ima ce babba ga dubban magoya bayanta a wannan birni wadanda suka shafe shekaru aru-aru su na ganin yadda abokan adawarsu a United su na cin karensu babu babbaka. Ga shi kuma idan City zata dage ta lashe sauran wasanninta biyu, ita zata dauki kofin Premier League na bana a Ingila.
Kwallon da Vincent Kompany ya jefa ana dab da tafiya hutun rabin lokaci, shi ya ba City nasara a kan United, amma kuma, amma kuma wannan rana ce da ‘yan wasan City suka mike tsaye suka nunawa duniya cewa su fa ba kanwar lasa ba ce.
An shiga wasan United tana gaba da maki 3 a saboda haka idan da United ce ta lashe wasan, to kusan za a ce ta lashe Premier League ta bana ke nan.
Amma yanzu su na da maki 83 kowaccensu, sai dai Manchester City ce a kan gaba a bambancin rarar kwallayen da ta jefa a raga guda 8. Ma’ana: idan har City zata doke Newcastle da Queens Park Rangers a sauran wasanninta biyu da suka rage, ita ce Zakara a bana.
Irin bukukuwan murnar da ‘yan Manchester City suka yi a filin wasan na Etihad a Manchester babu kama hannun yaro.
Mutane da yawa sun yi imani da cewa bana dai, shekarar ‘yan Manchester City ce a wasannin lig-lig na Premier na kasar Ingila.
Magoya bayan Manchester City

Magoya bayan Manchester City

04/25/2012Chelsea ta Yi Waje Rod Da FC Barcelona A Gasar Zakarun Kulob-Kulob Na Turai

Didier Drogba dan kasar Ivory Coast yana murna tare da sauran 'yan kungiyarsu ta Chelsea bayan da suka yi kunnen dokin da ya ba su nasara a kan kungiyar FC Barcelona, talata 24 Afrilu, 2012 a filin wasa na Camp Nou, a Barcelona, kasar Spain.

Didier Drogba dan kasar Ivory Coast yana murna tare da sauran 'yan kungiyarsu ta Chelsea bayan da suka yi kunnen dokin da ya ba su nasara a kan kungiyar FC Barcelona, talata 24 Afrilu, 2012 a filin wasa na Camp Nou, a Barcelona, kasar Spain.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi waje-rod da kungiyar dake rike da kofin zakarun kulob-kulob na Turai, FC Barcelona, daga gasar ta bana, ta kuma samu kaiwa ga wasan karshe bayan da suka tashi da ci 2-2 daren talata a filin wasa na Camp Nou dake Barcelona. Duk da cewa an kori dan wasan Chelsea daga filin, suka rage saura 10 kawai.
Wannan ya sa Chelsea zata wuce da ci 3-2 idan an hada da nasarar da ta samu a karawarsu ta farko.
Da farko, kamar FC Barcelona zata kai labari a bayan da Sergio Busquets ya jefa mata kwallo a minti na 35 da fara wasa, sannan Andres Iniesta ya kara na biyu a minti na 44.
A minti na 37 da fara wasa, an kori dan wasan Chelsea John Terry daga fili saboda ketar da alkalin wasa yace yayi ma dan wasan FC Barcelona mai suna Alexis Sanchez.
Ramires ya ramawa Chelsea kwallo daya ana dab da zuwa hutun rabin lokaci.
An ba dan wasan Barcelona Lionel Messi bugun fenariti, amma sai ya kasa sakawa cikin raga a bayan da Didier Drogba yayi keta ma Cesc Fabregas.
Fernando Torres ya tabbatrwa da ‘yan Chelsea nasara a wannan karawa a lokacin da ya jefa kwallo na biyu a minti na 90 da wasa.
Chelsea, wadda ba ta taba lashe gasar zakarun kulob-kulob na Turai ba, zata jira wadda zata yi nasara a karawar da za a yi larabar nan a tsakanin Real Madrid da Bayern Munich.
Za a yi karawar karshe ranar 19 ga watan Mayu a birnin Munich na kasar Jamus.

04/23/2012Fabrice Muamba Yace Bai Ji Zafin Komai Ba A Lokacin Da Ya Fadi Ya Suma, Zuciyarsa Ta daina Bugawa

Dr Andrew Deaner, a hagu, Fabrice Muamba na kungiyar BoltoN a tsakiya, sai kuma Dr. Sam Mohiddin (Dama) wanda ya jagoranci likitocin da suka kula da Muamba a lokacin da yake kwance a asibiti yana jinyar ciwon zuciya. Dr. Deaner dake hagu, shi ne likitan da ya garzaya cikin filin wasa a lokacin da Muamba ya fadi a filin White Heart Lane lokacin da kungiyarsa ke kwallo da Tottenham.

Dr Andrew Deaner, a hagu, Fabrice Muamba na kungiyar BoltoN a tsakiya, sai kuma Dr. Sam Mohiddin (Dama) wanda ya jagoranci likitocin da suka kula da Muamba a lokacin da yake kwance a asibiti yana jinyar ciwon zuciya. Dr. Deaner dake hagu, shi ne likitan da ya garzaya cikin filin wasa a lokacin da Muamba ya fadi a filin White Heart Lane lokacin da kungiyarsa ke kwallo da Tottenham.


Fabrice Muamba ya bayyana cewa bai ji zafin komai ba a lokacin da zuciyarsa ta tsaya ta daina bugawa lokacin da yake wasa ma kungiyarsa ta Bolton Wanderers a watan da ya shige.
An sallami Muamba daga asibiti tun ranar litinin da ta shige, kuma ya fara kokarin murmurewa a bayan da zuciyarsa ta daina bugawa har na tsawon minti 78 lokacin da suke gwabzawa da kungiyar Tottenham.
Muamba ya fadawa jaridar “The Sun on Sunday” cewa, “ban ji zafin komai ba, ban kama kirji na ba, haka kuma ban ji kirjin nawa ya daure kamar yadda muka saba gani a cikin fim idan mutum ya samu ciwon tsayuwar zuciya ba. Na ji jiri, amma ba irin jirin da ak saba ji ba, sai na ji kamar ina gudu a cikin jikin wani mutum dabam. Daga nan sai na fara ganin abubuwa su na zamowa bibbiyu, kamar dai a mafarki. Na hangi ‘yan wasan (Tottenham) Spurs su na gudu a can nesa, sai na ga Scott Parker ya zamo mutum biyu, haka ma Luka Modrics.”
“Abu na karshe da na ji, shi ne mai tsaron bayanmu Dedryck Boyata yana ta yi mini ihun cewa in yi sauri in koma baya in taimakawa masu tsaron baya. Bai san abinda ke faruwa da ni a lokacin ba, kamar yadda ni ma ban sani ba. Haka kawai sai na ji ina yin kasa zan fadi, sai na ji kara har sau biyu a lokacin da kai na ya fadi ya bugi kasa, daga nan sai duhu kawai, ban sake jin komai ba…”
Muamba ya shafe fiye da makonni 4 a asibiti, amma har aka sallame shi ba a san abinda ya sa zuciyarsa ta daina bugawa ba.
A yanzu an sallame shi a bayan da akab sanya masa wata karamar na’urar da zata maido da bugawar zuciyarsa idan har ta sake tsayawa nan gaba.
“Ido na biyu a lokacin da aka dasa mini wannan na’ura,” in ji Muamba mai shekaru 24 da haihuwa. Na’urar ba zata bukaci sauyin batur ba sai bayan shekaru 10.
“Abin da ya faru gare ni, wata mu’ujiza ce. Koda na rayu, ana tsammanin kwakwalwa ta zata samu illa. Ina fata zan samu sukunin sake buga kwallo a nan gaba. Amma abinda ya fi duka wadannan shi ne na rayu, kuma in ci gaba da nuna kauna da soyayya ga iyali na. babu shakka, na yi babbar sa’a.” In ji Fabrice Muamba

04/ 2/2012Sabon Salo, Sabon Yayi

Cristiano Ronaldo na Real Madrid yana nuna cinyarsa a bayan da ya jefa kwallo a ragar 'yan wasan kungiyar Osasuna ranar asabar 31 Maris, 2012, abinda ya sa har sauran 'yan wasan Real Madrid suka rika kwaikwayon wannan sabon salo ko yayi nasa.

Cristiano Ronaldo na Real Madrid yana nuna cinyarsa a bayan da ya jefa kwallo a ragar 'yan wasan kungiyar Osasuna ranar asabar 31 Maris, 2012, abinda ya sa har sauran 'yan wasan Real Madrid suka rika kwaikwayon wannan sabon salo ko yayi nasa.


A ranar asabar 31 Maris 2012 ne kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta yi kaca-kaca da kungiyar Osasuna da ci 5 da 1, a karawarsu ta wasannin lig-lig na Spain. Cristiano Ronaldo dan kasar Portugal shi ya jefa kwallaye biyu daga cikin guda biyar din.
Kwallon farko, irin kwallon nan ne da ake kira “Makami mai cin dogon zango” domin tun daga nesa ya sako ta har cikin raga.
Amma babban abinda ya fi burge jama’a ‘yan kallo da sauran ‘yan wasa shi ne a lokacin da shi Ronaldo yake murnar jefa wannan kwallo, sai ya ja wandonsa sama, yana nuna ma jama’a cinyarsa, watau kamar yana fadin cewa irin karfin dake jikin cinyar tasa ta shige misali.
Wannan abu ya burge sauran ‘yan wasan Real Madrid, domin kamar yadda za a gani cikin bidiyo dake kasa, a bencinsu ma sai sauran ‘yan wasan suka fara kwaikwayon wannan abu da Ronaldo yayi, su na nuna cinyarsu domin fadawa duniya cewa su fa ba kanwar lasa ba ne.

03/27/2012ban Kwana Da Birgit Prinz

Birgit Prinz ta Jamus tana ban kwana da 'yan kallo a bayan wasanta na karshe na ban kwana yau talata, 27 maris 2012 a tsakanin kulob dinta FFC Frankfurt da kungiyar kwallon kafar mata ta kasar Jamus. Sau uku Birgit Prinz tana zamowa zakarar kwallon kafar mata ta duniya.

Birgit Prinz ta Jamus tana ban kwana da 'yan kallo a bayan wasanta na karshe na ban kwana yau talata, 27 maris 2012 a tsakanin kulob dinta FFC Frankfurt da kungiyar kwallon kafar mata ta kasar Jamus. Sau uku Birgit Prinz tana zamowa zakarar kwallon kafar mata ta duniya.


A yau talata, 27 Maris 2012 masu sha’awar tamaular mata a duniya suka yi ban kwana da daya daga cikin mashahuran masu buga kwallon mata, Birgit Prinz ta Jamus, wadda sau uku tana zamowa zakarar kwallon kafar duniya ta FIFA.
Prinz, mai shekaru 34 da haihuwa, ta lashe kofin duniya na mata har sau biyu a kungiyar kwallon kafar mata ta Jamus.
Dubban jama’a, cikinsu har da shugaban hukumar kwallon kafa ta Jamus, suka cika filin wasa na Frankfurt a yau talata, a lokacin da Prinz ta yi wasanta na karshe. Gaba daya filin ya mike tsaye ana tafa mata, lokacin da ta bar wasa ana kusa da tashi.
Prinz ta samu zuwa gasar cin kofin duniya har sau biyar, inda ta jefa kwallaye har 14. Marta ta kasar Brazil ce kadai macen da ita ma ta jefa kwallaye 14 a raga lokacin gasar cin kofin duniya.
A wasanni har 214 da Prinz ta buga ma kasar Jamus, ta saka kwallaye 128 a raga.
Har ila yau, ta taimakawa kasar Jamus wajen lashe kofin zakarun Mata na Turai sau biyar, tare da lambobin Tagulla 3 a wasannin Olympics.
Birgit Prinz rike da furannin da aka ba ta jim kadan kafin wasanta na karshe yau talata, 27 Maris 2012 a Frankfurt

Birgit Prinz rike da furannin da aka ba ta jim kadan kafin wasanta na karshe yau talata, 27 Maris 2012 a Frankfurt

Featuring WPMU Bloglist Widget by YD