Manchester City, Zakara?

Posted May 1st, 2012 at 5:24 am (UTC+0)
5 comments

Magoya bayan kungiyar Manchester City sanye da kalar kungiyarsu a lokacin karawar da ta yi da abokiyar adawarta Manchester United, litinin 30 Afrilu 2012 a filin wasa na Etihad dake birnin Manchester. City ta lashe wasan da ci 1-0.

Magoya bayan kungiyar Manchester City sanye da kalar kungiyarsu a lokacin karawar da ta yi da abokiyar adawarta Manchester United, litinin 30 Afrilu 2012 a filin wasa na Etihad dake birnin Manchester. City ta lashe wasan da ci 1-0.


Marubucin tamaula Martin Rogers yace ba wai an nada sabon zakaran lig-lig na kasar Ingila ne a karawar da aka yi litinin a tsakanin Manchester City da Manchester United ba, amma duk wanda ya kalli wasan zai ga kamar abinda aka yi ke nan.
dalili shi ne wadannan kungiyoyi biyu sune ke sama a rukunin na Premier League na Ingila.
Nasarar da Manchester City ta samu da ci 1 da babu a kan Manchester United, tamkar wata ni’ima ce babba ga dubban magoya bayanta a wannan birni wadanda suka shafe shekaru aru-aru su na ganin yadda abokan adawarsu a United su na cin karensu babu babbaka. Ga shi kuma idan City zata dage ta lashe sauran wasanninta biyu, ita zata dauki kofin Premier League na bana a Ingila.
Kwallon da Vincent Kompany ya jefa ana dab da tafiya hutun rabin lokaci, shi ya ba City nasara a kan United, amma kuma, amma kuma wannan rana ce da ‘yan wasan City suka mike tsaye suka nunawa duniya cewa su fa ba kanwar lasa ba ce.
An shiga wasan United tana gaba da maki 3 a saboda haka idan da United ce ta lashe wasan, to kusan za a ce ta lashe Premier League ta bana ke nan.
Amma yanzu su na da maki 83 kowaccensu, sai dai Manchester City ce a kan gaba a bambancin rarar kwallayen da ta jefa a raga guda 8. Ma’ana: idan har City zata doke Newcastle da Queens Park Rangers a sauran wasanninta biyu da suka rage, ita ce Zakara a bana.
Irin bukukuwan murnar da ‘yan Manchester City suka yi a filin wasan na Etihad a Manchester babu kama hannun yaro.
Mutane da yawa sun yi imani da cewa bana dai, shekarar ‘yan Manchester City ce a wasannin lig-lig na Premier na kasar Ingila.
Magoya bayan Manchester City

Magoya bayan Manchester City

5 responses to “Manchester City, Zakara?”

  1. Bala Dahiru Hassan says:

    Mu yan Man u munanan sai munga abunda yature wa buzu nadi kuma kusane bazamu MT ba

  2. haruna irani m/fashi says:

    muyan manchester united bagudu baja da baya sai mundauki kofin ko makiya naso ko basuso

  3. Mahjamm says:

    Mttswww! Winning de0s n0t mean bcm d highest just l00k 4 future

  4. Salisu hd says:

    fatandamukai kenan city sudoke man u saboda adawar da sukayimana ranar laraba Up madrid

Leave a Reply to Salisu hd Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

About

Shafin Tamaular Duniya

Dandalin wadanda ke sha’awa, kuma suka san abinda zasu iya fada kan kwallon kafa. Yaro ba ya wargi!!

Categories

Calendar

May 2012
M T W T F S S
« Apr   Jun »
 123456
78910111213
14151617181920
21222324252627
28293031