Allah Ya Jikan Rashid Yekini, Mun Yi Rashi

Posted May 7th, 2012 at 4:22 am (UTC+0)
20 comments

Rashid Yekini, lokacin da ya jefa ma Najeriya kwallonta na farko a gasar cin kofin duniya a 1994.

Rashid Yekini, lokacin da ya jefa ma Najeriya kwallonta na farko a gasar cin kofin duniya a 1994.


Duk wani masoyin Najeriya da kwallon kafa a Najeriya da Afirka, ba zai taba mantawa da Rashid Yekini ba.
Rashid Yekini, ya rasu ranar jumma’a a Ibadan, yana da shekaru 48 da haihuwa.
Babu wani dan kwallon da ya taba jefa ma Najeriya kwallaye kamarsa, inda a cikin wasanni 58 da ya buga ma kungiyar Super Eagles, ya jefa kwallaye har 37.
Amma babban abinda mutane suka fi tunawa a game da Rashid Yekini, wanda aka haifa ranar 23 ga watan Oktoba, 1963 a Kaduna, shi ne irin rugawa da gudun da yayi ya shiga cikin ragar ‘yan kasar Bulgariya, ya rike raga yana ihu da iyakar karfinsa, a bayan da ya jefa ma Najeriya kwallonta na farko a gasar cin kofin kwallon kafar duniya a 1994 a Amurka.
haka kuma, Rashid Yekini, shi ne dan Najeriya na farko da aka taba zaba a matsayin zakaran kwallon kafa na nahiyar Afirka a 1993, kuma shekara daya bayan wannan, ya taimakawa ‘yan Super Eagles na Najeriya suka ciwo kofin zakarun kasashen Afirka.
Shi ne dan wasan da ya fi jefa kwallaye cikin raga a wasannin lig-lig na kasar Portugal a 1993-1994 a lokacin da yake buga wasa ma kungiyar Vitoria Setubal. A shekaru 4 da yayi a wannan kulob, Rashid Yekini ya jefa kwallaye 90 cikin raga.
Yayi wasa a kasashe da dama kafin ya zo yayi ritaya a kungiyar Julius Berger ta Najeriya a 2003.
A bayan fage, Rashid Yekini mutum ne mai shiru-shiru, wanda bai cika shiga harkar da ba tasa ba. Abin koyi ga kowa.
Allah Ya jikan Rashid Yekini, Ya sa mutuwa hutu ne gare shi, amin summa amin.
Marigayi Rashid Yekini

Marigayi Rashid Yekini

20 responses to “Allah Ya Jikan Rashid Yekini, Mun Yi Rashi”

  1. Sharif Ahmad Liman Giwa Kaduna Nig. says:

    Kaji wadanda suka bautawa kasarsu bilhaqqi da gaskiya saboda kishi bawai don kudiba sabanin yan wasan mu nayanzu marasa kishi kwadayayyu shiyasa bazamu taba mantawa da irin su rashidi yekini ba Allah yaji kansa ameen.

    • Ibrahim Alfa Ahmed says:

      Wannan magana ta ka gaskiya ce Sharif. Kaicon ‘yan wasanmu na yanzu, wadanda idan sun je fili ma sai sun yi lada da officials kafin su buga kwallon, sai sun ji abinda za a ba su!!!

  2. ALLAHU AKBAR! ALLAHU AKBAR!! ALLAHU AKBAR!!!
    ALLAH YA JIKAN GWARZO! MUNYI RASHIN JAGORA,SHUGABA,ABIN KOYI.
    RASHIDI YAKINI MUTUM NE HAZIKI,MAI NEMAN MA SHUWA GABANINSA DA KASARSA SUNA BADON KANSA KAWAI BA,SE DON ALUMMAR SA DA KASARSA BAKI DAYA.
    SHI MUTUM NE HAZIKI, BA MAI YAWAN NEMAN DUKIYABA,SABANIN YAN KWALLON YANZU MASU NEMAN TARA ABIN DUNIA KAWAI.
    ALLAH YA JIKAN GWARZO NA.
    YAN BAYA,AN BAR MAKU ABIN KOYI.
    WASSALAM.

  3. Kulllu nafsin, za`i katil nafsi.Allah ya jikan Rashid yakeni.Mu kuma Allah ya kyauta namu zuwan. Amin suma amin.

  4. Abdulwahid Labbo says:

    The contribution he gave in Nigerian foot ball will ever remain in hitory, May Soul of Rashid rest in perfects peace witrh all his sins forgiven,ameen.

  5. Allah jikan Rashid yakini Allah bamu wadanda zasu maye gurbin shi. Suyi dan kishin kasa badan kansuba ameen.

  6. Wannan shaharren dan wasa an dai riga an rasashi,kuma baza a taba maye gurbinsaba.yan wasan mu nayanzu allah wadaranku ya sauya mana ku da irin su marigayi rashid ba irinku rubabbu ba marasa kishin kasarsu.

  7. abba says:

    allah ya jikan sa

  8. HASSAN YUSUF says:

    ALLAH YAJIKAN KA YA GAFARTAR MAKA AMEEN YAN KISHI BA YAN CIN KUDI DA KISTO BA SAI KACE MATA

  9. ALLAH YAKJIKAN ALLAH YASADASHI DA RAHAMA

    • Abubakar Danlami says:

      Allah yajikan musulmai yakuma gafartamana Ameen Summa Ameen,
      Allah yakuma bamu irin RASHIDI YAKINI AMEEN.

  10. Nasirudeen M.Baba says:

    Allah ya jikansa yasa ya huta

  11. Allah ya ga far tawa rashid yakini amin.

  12. Rashin maza baza abin bakin cikine allah jikan maza

  13. Aminu salisu nadama, Gusau says:

    Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un. KULLI NAFSIN ZA’IKATUL MAUT. Ubangiji allah jikanshi kuma allah masa rahama ameen. Mu kuma idan tamu tazo allah sa mu cika da imani da kalmar shahada amen summa amen.

  14. Allah yasa yanzu yakini Yana cikin aljannar firdausi Amin.

  15. Good says:

    Masuyi dan yankasarsuba

Leave a Reply to Nasirudeen M.Baba Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

About

Shafin Tamaular Duniya

Dandalin wadanda ke sha’awa, kuma suka san abinda zasu iya fada kan kwallon kafa. Yaro ba ya wargi!!

Categories

Calendar

May 2012
M T W T F S S
« Apr   Jun »
 123456
78910111213
14151617181920
21222324252627
28293031