Zakarun Kulob-Kulob Na Turai

Posted February 21st, 2012 at 4:09 pm (UTC+0)
13 comments

Yaya Toure

Yaya Toure

Yau da gobe sai Allah in ji Hausawa.
A yau talata, Chelsea da Napoli, sai kuma Real Madrid da CSKA Moscow.
Gobe laraba, Inter Milan da Marseille sai kuma Bayern Munich da Basel.
Ga abinda na ji wasu kwararru su na fada:
Napoli zata ci wasan yau talata da yake a gidanta ake yi, amma Chelsea zata ci zagaye na biyu kuma ita zata haye zuwa gaba.
Real Madrid zata lashe wasanta na yau duk da cewa a Moscow ake wasan a gidan ‘yan CSKA, kuma zata wuce zuwa gaba.
Inter Milan zata kashi gobe laraba a hannun ‘yan Marseille, kuma ba zata kai labari ba, ‘yan Marseille su zasu zarce.
Bayern Munich zata doke Basel na Switzerland a yau da kuma zagaye na gaba, ta wuce zuwa ga wasanni na gaba.
Ni dai a taya ni duba hanya, wai makaho na son yin tsegumi. Na dai san tun da aka fara gasar zakarun kolb-kulob na Turai na bana, kwallaye biyu kawai aka jefa a ragar ‘yan Real Madrid a lokacin da ake rukuni-rukuni.
Babu wanda aka fi neman kassarawa a fili lokacin wasannin kamar Franck Ribery na Bayern Munich wanda aka yi ma (foul) har sau 23.
Daga cikin kungiyoyi 16 da suka rage, Chelsea ce kawai ba ta aikata laifi da yawa ba a zagayen rukuni-rukuni na gasar, inda aka hura mata wusur na laifi (foul) sau 61 kawai.
Ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare. Akwai wanda zai yi mini karin haske kan wannan gasar?

13 responses to “Zakarun Kulob-Kulob Na Turai”

 1. Ahmed Mohammed says:

  Real Madrid 1 – 1 CSKA Moscow.

 2. Hamisu Ahmad says:

  Nayi matuqar murna da karanta wannan labarin kuma nayi murna, saidai banji kunce komai ba game da Man. United da Arsenal. Sannan ina batun gidan Rina wato Liverpool?

  • Ibrahim Alfa Ahmed says:

   Ai dole mu ce Man U ko Arsenal ko Liverpool. Wasanninsu na tafe, amma idan kana da ta cewa game da su yanzu, mun kasa kunne. Watau dai ka ce Liverpool gidan Rina ce ko? Kana jin za su kai labari bana ne a Gasar Zakarun Turai ko Premier League?

 3. yusufshuaib says:

  Bani kallon kwallo amma chelsea tayi min

 4. yo malam ahmed yaya akayi banji kon tabo batun gwarzayen duniya wato Fc Barcelona?

 5. mu dai kam yan barcelona muna sa ran mu zamu lashe gasar incha allahu

 6. Mohammed 'Dan India says:

  Wannan hasashe a na iya cewa ya yi daidai sai dai abin da ba’a ‘dan rasa ba.Gara da a ke cewa hasashe domin ko Sarkin hasashe ba bbc Mark Lawrenson tare da Gari Liniker na sha ganin sun yi hasashe sau ya fi a kirga amma sai daga baya ka ga akasin hakan.Kamar yadda ka ce ba’a san maci tuwo ba sai miya ta kare wannan ko sahkka babu.To ni bisa ga hangen da na yi duk da cewar Inter Milan ta yi rauni kwarai idan a ka duba record din wasannin da ta buga a baya bayan nan inda a wasanni 12 da su ka shige ta sha kashi har sau 5,ta samu nasara 4,ta buga kunnen doki 1,yayin da Marseiles ta samu nasara 8 a wasanni 12,ta buga kunnen doki 3,ta sha kashi sau 1 tal,abin da ke nufin ta na in foam fiye da Inter.To amma fa ba nan gizo ke saka ba musamman idan an duba record din kungiyoyin 2 a wasannin Interclub 6 da su ka buga a baya in da za’a tarar ko wannen su ta yi nasara ne har sau 2 a waje,yayin da ta sha kashi sau 2 a gidan ta,ta kuma buga kunnen doki sau 1 a waje,ta kuma samu nasara sau 1 tak a gidan ta.Wato idan an duba wadannan alkaluma za’a ga cewar cikin kungiyoyin 2 babu wacce ta sha kashi a wajen gidan ta ,amma fa dole ne a yi la’akari da koma bayan da Inter ta samu bayan tafiyar Mourinho Madrid.A sauran hasashen kuma tun ba’a je ko ina ba ga Madrid ta buga kunnen doki duk da cewar kowa ya yi imanin ita za ta yi nasara a Rasha.Sai kuma Bayern wace ita ma za ta haye,amma kuma a nawa ra’ayin akwai alamar tambaya ko Chelsea za ta iya hayewa zuwa zagaye na gaba ganin irin koma bayan da kungiyar ke fuskanta kuma ga advantage na kwallaye 2 abin da ke nufin dole sai ta zura wa Napoli kwallaye 2 babu martani kafin ta samu hayewa…..

 7. CSKA.Idan sukashago babar stardiom wato santiago to anan zasu gane kurens kuma zasusan awancan wasan kyalesuakayi barima iyi hasashe.RM.4KO3. CSKA.0 KOKUMA.1

 8. Bala dahiru hassan says:

  Ashe ba’a Nigeria kadai ake bada home advantage ba harda karashen turawa domin jiya munga alkalin da ya hura wasan chelsea da napolli yafito karara bayasan napoli domin suna away yahanasu motsi afili duk abunda aka musu baya hurawa sukuma idan sunyi abu kadan sai kaji yahura musu dahaka dahaka har aka cisu 4-1
  saboda haka chelsea kusani akwai mazaje agabanku wanda basai na fadi sunan suba sunanan suna jiranko baruwansu da home advantage cinku zasuyi ajuri zuwa rafi da tulu.

 9. inaga shekararda chelsea zasu dauki champions leage tazo. don munga alamu.

Leave a Reply to Hamisu Ahmad Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

About

Shafin Tamaular Duniya

Dandalin wadanda ke sha’awa, kuma suka san abinda zasu iya fada kan kwallon kafa. Yaro ba ya wargi!!

Categories

Calendar

February 2012
M T W T F S S
    Mar »
 12345
6789101112
13141516171819
20212223242526
272829