Me Naira Miliyan 62 Zai Yi Maka?

Posted February 22nd, 2012 at 6:31 pm (UTC+0)
10 comments

Thiery Henry


Zai iya gina maka tankin kifi, idan kai ne Thiery Henry.
Idan da ni ne nake da wannan kudi haka, to da abinda zan fara yi shi ne in yi ritaya daga aikin jarida, in fara noma ko in kafa wata masana’anta inda mutane masu yawa za su samu aikin yi.
Amma wannan ba shi ne tunanin shahararren dan kwallon nan na Faransa, Thiery Henry ba, domin ya ware wannan kudi ne za a gina masa tankin ajiye kifi na kallo a cikin gidansa.
Jaridar “The Daily Mail” ce ta ke cewa Henry zai gina sabon gida, mai hawa 4, kuma daya daga cikin sabbin abubuwan da za a yi masa, shi ne wani tankin gilashi na ajiye kifi, mai tsawon kafa arba’in daga kasa zuwa sama, kuma mai fadin kafa 15.
Watau tankin kifin zai taso tun daga hawan farko har zuwa hawa na hudu a wannan gida.
Kudinsa, Dala dubu 400, ko Naira Miliyan 62!! Cafdi
A bayan Naira Miliyan 62 na gina wannan tanki, Henry zai rika kashe sama da Naira miliyan 3 a kowace shekara wajen kula da wannan tankin kifi da kuma kifaye guda 300 da tankin zai iya dauka. Hmmm
Kudi na gwamna masu gida rana.
Idan da kai ne, me za ka yi da wannan kudi Naira miliyan 62?

10 responses to “Me Naira Miliyan 62 Zai Yi Maka?”

  1. A gaskiya da nine a garinmu Aliero akwai babbar kasuwar Albasa amma manoma basu taba cin gajiyarta ba sai inyi kokarin gina musu wata masa’anta wadda ta shafi kayan lambu musamman Albasa

  2. umarunazare says:

    idan nine zanyi ritaya daga aikin haraji, na sayi tifa 5, babban fili, saura kuma na sayi siminti, na bude gidan buga bulo da sayar da yashi, a kalla zan tallafawa sama da mutum 20, su samu aikin yi, ni kuma na samu riba

    • Ibrahim Alfa Ahmed says:

      Hahahaha, lallai riba kam zaka samu. Jarin miliyan 62, ai ko a banki ka ajiye su kawai ribar ta ishe ka shan miya mai maiko.

  3. Mohd mohd says:

    Ai idan na sami wannan mazan kudin to insha ALLAHU bayan noma ma harda kiwo. sannan kuma zan ware wani abu in taimakawa al’ummar Annabi.

  4. Kwarai kuwa ake noman Albasa Aliero kamar kasa take saidai kudi idan kanada tirela ashirin kakawo cikin kwana hudu ancika ma su da albasa kayi kudancin Najeriya da ita cikin sati biyu tazama kudi

  5. Za gina makarantu da asibiti kyauta don taimakawa mara sa galihu

  6. Inni zansam wannan, zancire miliyan biyu inyi gida insaye mota inkuma yi aure. Saura insamu wani kasuwancin da wasu zasu anfanu dani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

About

Shafin Tamaular Duniya

Dandalin wadanda ke sha’awa, kuma suka san abinda zasu iya fada kan kwallon kafa. Yaro ba ya wargi!!

Categories

Calendar

February 2012
M T W T F S S
    Mar »
 12345
6789101112
13141516171819
20212223242526
272829