Older: Manchester City ko Manchester United? | Newer: Real Madrid ko FC Barcelona? |
Kaico, Rwanda Ta Gagari ‘Yan Super Eagles
Posted February 29th, 2012 at 5:46 pm (UTC+0)
Anya kuwa abinda ya faru game da gasar cin kofin kasashen Afirka ta Cup of Nations da aka kammala kwanakin baya, ba zai sake faruwa ga Najeriya ba a gasa ta gaba a 2013 ba?
Duk da cewa an buga wannan wasa ne a Kigali, babban birnin Rwanda, zaton kowa ne cewa Najeriya zata yi kaca-kaca da ‘yan wasan Rwanda wadanda ake kira WASP. Amma abin sam bai yiwu ba.
Wannan kuma shi ne karon farko da Stephen Keshi yake jagorancin kungiyar ta Super Eagles zuwa wata gasa ta zahiri.
Wai shin menene ra’ayinku a game da wannan abin kaico? A rubuta mana ra’ayi a kasa.
Older: Manchester City ko Manchester United? | Newer: Real Madrid ko FC Barcelona? |
4 responses to “Kaico, Rwanda Ta Gagari ‘Yan Super Eagles”
Stehen Keshi ya yi alwashin samar da Super Eagles Sabuwa fil tare da daina dogara da ‘yan wasa masu taka leda a Turai,amma kuma sai ga shi yawancin ‘yan wasan da ya gayyato su din ne dai tsoffin ‘yan wasan masu taka leda a kasashen Turai wadanda a baya su ka kasa tabukawa kungiyar wani abin kirki.Mu dai na mu mu musu fatan alheri duk da cewar har yanzu da alama ba ta sake zani ba……
yan wasan najeriya ba sa kishin kasar su ne, kan su kawai suke kishi. saboda haka yana da wuya su iya yin wani abun kirki. Kamata yayi keshi ya sake yan wasa gaba daya.
idan har a haka za a yi ta tafiya to najeriya kam babu inda za mu je a harkar wasanni. saboda an mayar da abin bangarenci da kishin yare fiye da kishin kasar.
gaskiya keshi ba zai iya rike super engle saboda jama’a da zatayi kyau tun daga laraba ake ganewa idan kai la’akari da wasan daya buga da ruwanda alamu ne nagazawa kawai ane mo coach