A yau talata, 27 Maris 2012 masu sha’awar tamaular mata a duniya suka yi ban kwana da daya daga cikin mashahuran masu buga kwallon mata, Birgit Prinz ta Jamus, wadda sau uku tana zamowa zakarar kwallon kafar duniya ta FIFA. Prinz, mai shekaru 34 da haihuwa, ta lashe kofin duniya na mata har sau biyu […]
Dukkan ‘Yan Kwallo A Turai Sun Karrama Fabrice Muamba
Ba kasafai ake samun abu guda dake hada kan ‘yan wasan Tamaula na Turai baki daya ba, im ban da irin wannan tsautsayi da ya abka kan Fabrice Muamba na kungiyar Bolton Wanderers, mai wasa a Premier League na Ingila. Mahaifin Muamba da wasu ‘yan’uwansa sun bayar da sanarwa su na godewa ‘yan kallo, da […]
Idan Kai Ne Yaya Zaka Yi? Fadi Gaskiya!
Na san watakila mafi yawan masu karanta wannan ba su san wata gasar da ake kira “Coppa Italia Dilettanti” a kasar Italiya ba. Ni ma dai ban sani ba, a gaskiya, sai da na kalli wannan bidiyon. Ita dai gasar, gasa ce ta cin kofin kulob-kulob masu buga kwallo a rukuni na 6 da na […]
Manchester United Ta Yi Tuntube
Kowa ya dauka cewa Manchester United zata doke Athletic Bilbao ta kasar Spain cikin sauki a karawar da suka yi ta gasar cin kofin Lig-Lig na Europa. Musamman da yake a Old Trafford aka buga wasan, inda aka ce kungiyoyi da dama su na fuskantar sanyin jiki idan sun shiga. Kamar sun shiga ramin kura! […]
Ana Farautar Kwadi Sosai A Koriya…A Dalilin Park Ji-sung Na Manchester United
Wai me ya hada dan wasan Manchester United da kashe kwadi da ake yi yanzu sosai a kasar Koriya ta Kudu? Da alama akwai. Tun lokacin da tsohon Kyaftin na Koriya ta Kudu, kuma dan wasan tsakiya na Manchester United, Park Ji-sung, ya rubuta cikin littafin tarihin rayuwarsa a 2006 cewa lokacin da yake yaro, […]
Chelsea Ta Kori Andre Villas-Boas
Ina cire hula ta ma Mohammed Dan Indiya, domin tun ranar da na fara rubutu a wannan dandalin, yayi mini hasashen cewa Chelsea zata kori Andre Villas-Boas. Yau ina tashi ke nan sai na yi ta ganin sakonnin cewa a karshenta dai Roman Abramovich ya kori Villas-Boas, kuma ya maye gurbinsa da mataimakin manaja Roberto […]