Maki 10 cur kungiyar Real Madrid ta ba FC Barcelona a wasannin lig-lig na Primera Division a kasar Spain. Za ka yi zaton cewa ‘yan wasan Barcelona su na cike da haushin Real Madrid, amma a ranar talatar nan an ga Fabregas yana rubutu a jikin rigar dan wasan Real Madrid!
Abin kamar almara. Wasu ‘yan kallo a Malaga a kasar Spain suka tare ‘yan wasan kasar su na neman su buga musu hatimi (signature) domin su ajiye saboda tarihi. ‘Yan wasan Spain su na can ne domin buga wasan sada zumunci da ‘yan Venezuela.
Daga cikin ‘yan wasan har da Cesc Fabregas, dan wasan tsakiya na Barcelona, wanda wani dan kallo ya mika masa rigar dan wasan Real Madrid Mesut Ozil, amma maimakon yace ya mika wani abu ya sanya masa hannu a kai, sai kawai ya buga hatimin nasa a jikin rigar dan Real Madrid, kamar su ba kishiyoyi ba.
Watakila kunya yake ji, ko kuma ba ya son bata ma wannan yaro rai, amma ai kowa ya san cewa Barcelona tana cikin jinin Fabregas. Ko kuma dai bai karanta abinda ke jikin rigar ba ce, wallahu ya alamun.
Wani mai sharhi, Brooks Peck ma cewa yayi watakila bai karanta jikin rigar ya gani ba, domin kuwa da yana karance-karance da yawa, to da ba abinda zai taba kai shi birnin London a kasar Ingila.
Hmmm, wa ya sani!!
Older: Kaico, Rwanda Ta Gagari ‘Yan Super Eagles | Newer: Robin van Persie Ya Harbe ‘Yan Liverpool |
Real Madrid ko FC Barcelona?
Posted March 1st, 2012 at 8:00 pm (UTC+0)
Posted in Uncategorized
Older: Kaico, Rwanda Ta Gagari ‘Yan Super Eagles | Newer: Robin van Persie Ya Harbe ‘Yan Liverpool |
25 responses to “Real Madrid ko FC Barcelona?”
Wannan yanuna chewar wasa ba fada bane hada zumunchine shiyasa yarike rigar ozil
Gaskiya ni a gani na a wannan zamani dai ba wani can na daban ba Barca ta shiga gaban kowa dan kuwa sun zama ciwon ido sai hakuri. Tausayawa madrid sukayi shiyasa suka bar musu dan su dan samu kofin shan shayi tunda bazasu iya ba.
Hahahahahaha, abinda kake son mutane su yarda da shi ke nan?
Ina gani baya son batawa yoron rai, kuma ni naji dadi dayayi hakan,hakan zai nuna babu babbanci a wasan kollom kafa
Aminu, amma dai kowa ya san ra’ayin Fabregas game da abokiyar adawarsu Real Madrid.
To ni aganina baya zama illah, domin agidan tamaula yasan abokin gabarka kan iya zama abokin wasanka kuma a kulub daya, tamaula kenan.
Gaskiyar magana wannan na nuna cewar harkar wasa ba ffada bane domin yasan akwai jikakka tsakanin kungiyoyin biyu amma yayi sign a jersey mai dauke da sunan ozil.wannan darasine ga sauran yan wasa.
GAba dai gaba dai duniya(barca) wanda ya iya ya huta baruwansa da adawa ko bakin ciki don haka kowa nasune.
Kai!! Ni aganina babba yayi gaba yaro sai labari, yasan cewa ozil ya kafa tarihi, don haka shima fabregas yasan tun tashinsa yaji ana kiran sunan madrid a fagen nasarar tamaula. Don haka yasan cewa kafa tarihine ace kana bugawa madrid kwallo, bama ace ka fito daga spain….Don haka yanason nan gaba madrid ta kirashi domin yakafa tarihin cewa ya bugawa madrid kwallo. Ka matsa yaro!!
Ai ansan babba bai tabba kishin nakasa gareshiba , a wannan lokacin shi kanshi ozil abin alfahari ne gareshi cesc ya sa hannu a rigarsa domin ya san kowanene cesc, dawowar shi a barca cikin watanin da basu yi shekara daya ba , ya chika burin da korabinshi ozil baisamu ba tun zuwanshi real(ai idan zaki ya hangi barewa , ya daga mata hannu har ya shafa kanta ai yai mata adalci domin ta san ko darajar kafar sa daya batayiba) albarkacin kaza kadangare ke iske ruwa yashasu har ya shake cikinsa yasan ba don shi ankazuba ba
Hahahaha Bashir, wanene zaki a tsakaninsu, kuma wacece barewar?
Hahaha duk ba haka bane cecs yana kora kunya da haukane kawe saboda bana bazai samu biyan bukatarsaba mu Arsenal duk wanda yabarmu sai yagane kurensa
Haba yasani kawai yasan yanxu munfi karfinsu ne. Ha ha ha ha Real Madrid basani basabo yanzu..
Tabbas wannan ya nu mana cewa sufa suna kasuwancin sune ba gababa
@ibrahim alfa, ai ozil ne zaki shikuma fabregas yazamo bera kokuma barewar da bashir yace.
wannan shike nuna babu kyau kayi gaba da abokin gabanka don shi kanshi fabregas yasan da haka lokacin da yana Arsenal anbashi gesin barca yakama kyamarta amma yanzu gashi ya zama dan wasansu kaga gabarda ya nuna masu bataimai amfaniba
Ni aganina real madrid itace club da tafi ko wacce club a duniya sai dai tarasa ingantacen mai rorarda yanwasantane.
Alh ibrahim Fabregas ne zaki mana shi ku ma ozil barewa
fabregas=world cup winner,(world club winner,super cup winner,laliga winner) chikin shekara daya
ozil=spanish kings cup winner kuma chikin shekara biyu da rabi
Komai na da na sa dalilin!!ni a nawa ganin ba ya son ya bata wa Yaron rai ne ba wai bai ga rigar ba ne.Kuma ka san Turawa da rarrashi da son Yara kankana da kuma dabbobi.A wani bangaren kuma kada a manta cewar shi fa ‘Dan wasa kasuwa ne a ko da yaushe akwai kararrawa a kan sa,wato kada ka yi mamakin wata rana ka ga Fabregas a Madrid ko Ronaldo a Barcelona dan shi ‘Dan wasa inda riba da kazamin kudi ya ke nan ne wajen yada zangon sa..Zancen maki 10 da Madrid ta baiwa Sarakan duniya kuwa mu har mun cire rai kan gasar la liga duk da cewar ba’a san maci tuwo ba sai miya ta kare.Da Champions da copa del rey da World Club cup wannan a wajen Madrid Garin dadi na nesa ne,ungulu ta leka masayi..Nan gani,nan bari,farar tumfafiya…..MES QUE EN CLUB……..
Madara madara madara kai a daiyi hakuri nagaba yayi gaba na baya sai kuran mota ai fabregas bai taba daukar kopin laliga ba kuma yagane cewa bana daikam sai hakuri up madrd.
ai ba’a adawa da wanda yafika iyawa.wannan na nuni cewa yasan ozil yafishi,kuma yana nunawa masu gaba akan kwallan kafa cewa ba sa gaba da juna.
wannan na nufin ba’a adawa da wanda yafika iyawa,shi fabregas yasa ozil yafi,sannan yana nufin masu gaba aka ball ball ai ba gaba bace.
Hmmmm
koba komai barca tafi karfin madrid
nidai nazabi barca