Older: Real Madrid ko FC Barcelona? | Newer: Chelsea Ta Kori Andre Villas-Boas |
Robin van Persie Ya Harbe ‘Yan Liverpool
Posted March 3rd, 2012 at 4:12 pm (UTC+0)
‘Yan Liverpool sai dai kuyi hakuri yau kam, amma a gaskiya kyaftin na ‘yan Arsenal, Robin van Persie, ya burge yau, domin ya tsame musu kitse a wuta a karawar da suka yi a gidan ‘yan Liverpool din.
Da farko, Laurent Koscielny yayi kuskuren jefa kwallo a ragarsu a bayan da mai tsaron gida na Arsenal ya burge ta hanyar tsare bugun fenariti na Dirk Kuyt.
Robin van Persie ya ramo wannan kwallon guda.
Ana dab da tashi kuma, sai kyaftin din dan asalin kasar Netherlands ya jefa kwallo na biyu, ya ba kungiyarsa nasara da ci 2-1.
Wannan nasara tana nufin cewa a yanzu Arsenal tana bayan Tottenham Hotspur da maki hudu ne kawai a matsayi na 4 (Hotspur tana matsayi na uku a Premier).
Gobe lahadi, Tottenham kuma zata kara da kungiyar dake gabanta a rukunin na Premier, Manchester United.
Tags: anfiled, arsenal, barclays premier league, epl, gunners, liverpool, manchester united, robin van persie, tottenham hotspurs
Posted in Uncategorized
Older: Real Madrid ko FC Barcelona? | Newer: Chelsea Ta Kori Andre Villas-Boas |
3 responses to “Robin van Persie Ya Harbe ‘Yan Liverpool”
himn ana biki a gidan su kare yace mugani akasa, rovin an persie kazama zaki sai kai mushen kura ka wuci allah sarki abi ahankali melaya yakiyayi mai zamani up arsenal.
Hahaha
wannan gaskiya kafadi vanpasie ikon allah ta babban mahaukaci duk duniya.