Older: Robin van Persie Ya Harbe ‘Yan Liverpool | Newer: Ana Farautar Kwadi Sosai A Koriya…A Dalilin Park Ji-sung Na Manchester United |
Chelsea Ta Kori Andre Villas-Boas
Posted March 4th, 2012 at 4:23 pm (UTC+0)
Ina cire hula ta ma Mohammed Dan Indiya, domin tun ranar da na fara rubutu a wannan dandalin, yayi mini hasashen cewa Chelsea zata kori Andre Villas-Boas.
Yau ina tashi ke nan sai na yi ta ganin sakonnin cewa a karshenta dai Roman Abramovich ya kori Villas-Boas, kuma ya maye gurbinsa da mataimakin manaja Roberto Di matteo, tsohon dan wasan ita Chelsea din, wanda zai jagoranci kungiyar har zuwa karshen shekara.
Tun lokacin da Abramovich dan kasar Rasha ya sayi Chelsea a shekarar 2003, kungiyar ta lashe Premier sau 3, ta lashe kofin FA (kalubalenka na Ingila) sau 3, ta kuma lashe lig-lig na Turai sau biyu.
Amma ba ta taba lashe kofin Zakarun Kulob-Kulob na Turai ba, kofin da aka ce shi mai kulob din ya fi kwadayin lashewa a kan komai.
Babban abinda ya kara fusata Ambramovich shi ne cewa yanzu Chelsea ta koma ta 5 a teburin Premier bayanda ta West Bromwich Albion ta doke ta jiya asabar, kuma a karon farko tun 1979.
Wannan shi ne karo na 8 cikin shekaru 9 da kulob din Chelsea zata shiga cikin kasuwar neman manaja.
Older: Robin van Persie Ya Harbe ‘Yan Liverpool | Newer: Ana Farautar Kwadi Sosai A Koriya…A Dalilin Park Ji-sung Na Manchester United |
2 responses to “Chelsea Ta Kori Andre Villas-Boas”
Haka ya ke AVB ya zama tarihi a Chelsea sai dai ya tafi ya bar kungiyar cikin rikita-rikita wanda gara ma Avram Grant da shi tunda Grant ya buga akalla final na Champions league da Carling cup,sannan kuma ya zama na biyu a gasar premier kafin a kore shi.Su kam su Mourinho da Ancelotti na san da za a bude zuciyar Abamovic sai an ga ta na cewa mai ya sa na kore wa’dannan kocinan.Idan Di Matteo ya yi sa’a ya yi iya bakin kokarin sa mai yuwa ya zarce.Idan ko ba haka ba sai a shiga neman sabon koci!su Rafael Benitez dama kwanan baya har an fara jita-jiatan cewar manajan sa ya fara tattaunawa da kungiyar.Ko ma yaya ta kaya dai Chelsea ta samu koma bayan da dole ne sai an sake komawa drawing boad a dubi menene matsalolin kafin samun bakin zaren…..
wani aiki sai mourenho…
Amma wani hanzari ba gudu ba, ya kamata chelsea su sayarda yan wasa kamar haka
1. Molouda.
2. Kalou.
3. Lampard.
4. Alex.
5. Obi.
Sai su shiga neman garaken yan wasa kuma coach