Ana Farautar Kwadi Sosai A Koriya…A Dalilin Park Ji-sung Na Manchester United

Posted March 7th, 2012 at 5:14 pm (UTC+0)
10 comments

Tsohon kyaftin na kasar Koriya ta Kudu, kuma dan wasan tsakiya na Manchester United, Park Ji-Sung

Tsohon kyaftin na kasar Koriya ta Kudu, kuma dan wasan tsakiya na Manchester United, Park Ji-Sung


Wai me ya hada dan wasan Manchester United da kashe kwadi da ake yi yanzu sosai a kasar Koriya ta Kudu?
Da alama akwai.
Tun lokacin da tsohon Kyaftin na Koriya ta Kudu, kuma dan wasan tsakiya na Manchester United, Park Ji-sung, ya rubuta cikin littafin tarihin rayuwarsa a 2006 cewa lokacin da yake yaro, mahaifinsa yana kamo kwadi ya tatse masa ruwansu yana sha domin ya samu kuzari a filin kwallo, yanzu kwadi sun fara karewa a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Yonhap na Koriya, ya ambaci wani jami’in kungiyar kare kwadi mai suna “Frogs Friends”, Park Wan-hee, yana fadin cewa sun lura da cewa daga lokacin da gwarzon dan wasan ya fadi wannan kalami, an fara samun masu farautar kwadi a boye cikin kasar.
Abin har ta kai ma kungiyar “Frogs Friends” ta fito tana kira ga dan kwallon da ya fito yayi tur da shan romon kwadi, ko mutane zasu komo cikin hayacinsu su daina farautarsu.
Dabara dai ta rage ga mai shiga rijiya.

10 responses to “Ana Farautar Kwadi Sosai A Koriya…A Dalilin Park Ji-sung Na Manchester United”

 1. Umar Isah Idris Shanono says:

  E lallai kuwa ! Allah daya gari ban ban, su zo nan Nigeria musamman a lokacin damuna, sai sun dibi kwadi har sun kasa dauka.

 2. ALI DANLADI says:

  TO KO SHI YASA YAN HADEJIA SUKE DA KUZARI NE DOMIN NAGA SUMA BASA BARI?

 3. Sageer isa mangelo kofar mata says:

  Wannan ai hannunka mai sanda suke yiwa yan nigeria domin mu ya kamata mu fita farauta sauraye domin rage mana kuzari da sauron yake tare da kashe mana mata kai yan nigeria ku fito mubi sahun yan korea domin mu kau da zazzabin cizon sauro

 4. ALI DANLADI says:

  KWADI DAI KAM TO, A KAI KASUWA

 5. Usman Muhammad Maidamma says:

  Hehehe, Allah da iko yake, to ai ganin nayi tunda dai har yana ganin ta hanyar shan romon kwadi ne ya samu wannan nasara. To ai kamata yayi ya buɗe kamfanin renon kwadi. Domin kar su kare

 6. Abubakar Yusuf Maradun says:

  Allah sarki ! Abin mamaki baya karewa duniya. Yau gashi kwadi sun zama abin farauta.

 7. Kamata yayi mutanen Nigeria su fara kiwon kwadi don su kai koria da china. Hanya ce ta samun kudi.

 8. musa kutama says:

  Ina gayyatar dan wasan kungiyar tawa yazo Niger-Delta har sai yaci yasha ya batse na jinjina maka Park, Hadejawa ga dangi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

About

Shafin Tamaular Duniya

Dandalin wadanda ke sha’awa, kuma suka san abinda zasu iya fada kan kwallon kafa. Yaro ba ya wargi!!

Categories

Calendar

March 2012
M T W T F S S
« Feb   Apr »
 1234
567891011
12131415161718
19202122232425
262728293031