Older: Ana Farautar Kwadi Sosai A Koriya…A Dalilin Park Ji-sung Na Manchester United | Newer: Idan Kai Ne Yaya Zaka Yi? Fadi Gaskiya! |
Manchester United Ta Yi Tuntube
Posted March 9th, 2012 at 8:42 pm (UTC+0)
Kowa ya dauka cewa Manchester United zata doke Athletic Bilbao ta kasar Spain cikin sauki a karawar da suka yi ta gasar cin kofin Lig-Lig na Europa.
Musamman da yake a Old Trafford aka buga wasan, inda aka ce kungiyoyi da dama su na fuskantar sanyin jiki idan sun shiga. Kamar sun shiga ramin kura!
‘Yan wasan Athletic Bilbao sun yi kaca-kaca da ‘yan wasan baya masu kare gidan Man U, ba kamar yadda kungiyoyi suke zuwa wannan fili da sanyin jiki ba.
Wayne Rooney dai ya burge ‘yan Man U, domin shi ya jefa musu dukkan kwallayensu biyu. Kuma an ce a kullum kafarsa tana dada sajewa da ta Chicarito Hernandez, wadanda Sir Alex Ferguson ya fara sanyawa tare a gaba.
yanzu wasa zai koma kasar Spain a ranar 15 ga watan nan. Anya Manchester United zata kai labari? Idan ‘yan wasan Athletic Bilbao suka ga dama, zasu rika yin wasan neman a tashi kunnen doki ne kawai.
Anya kuwa Man U zata iya hayewa a wannan kofin na Europa wanda idan suka lashe zasu sa Sir Alex Ferguson ya zamo ya taba lashe dukkan manyan kofunan Turai guda uku?
Ina ra’ayinku kan wanna?
Older: Ana Farautar Kwadi Sosai A Koriya…A Dalilin Park Ji-sung Na Manchester United | Newer: Idan Kai Ne Yaya Zaka Yi? Fadi Gaskiya! |
2 responses to “Manchester United Ta Yi Tuntube”
haba man u ai kashinku ya bushe bacan ba nan ba premire, kuma zasu shigo spain din lokacin nema bilbao zasuyi wasan kura dasu mudai yen kallo ne awannan lokacin.
muyan man united ko dubu zaacimu munfi karfin arsenal