Idan Kai Ne Yaya Zaka Yi? Fadi Gaskiya!

Posted March 17th, 2012 at 5:38 pm (UTC+0)
8 comments


Na san watakila mafi yawan masu karanta wannan ba su san wata gasar da ake kira “Coppa Italia Dilettanti” a kasar Italiya ba. Ni ma dai ban sani ba, a gaskiya, sai da na kalli wannan bidiyon.
Ita dai gasar, gasa ce ta cin kofin kulob-kulob masu buga kwallo a rukuni na 6 da na 7 a kasar Italiya, watau rukunonin Amatuwa.
A cikin wannan bidiyo ana karawa ne a tsakanin kungiyar Torres da Termoli. Ana dab da tashi daga wasan, sai alkalin wasa ya ba ‘yaa Termoli bugun fenariti a lokacin da dan wasanta Vittorio Esposito ya fadi a cikin shatin yadi 18. Shi kuma da ya ga cewa ba taba shi aka yi ya fadi ba, sai kunya ta kama shi, da aka ba shi bugun fenariti sai kawai ya je ya buga ta can wani wurin dabam, bai ma yi kokarin jefawa a raga ba.
‘Yan Torres sun yi murnar wannan, amma kuma sun yi bakin cikin cewa duk da haka an cire su a wannan gasar ta bana.
A karawarsu ta farko ma, Termoli ta yi wani abin ban dariya ga ‘yan kallo a lokacin da dan wasanta Fabio Cifani ya lura cewa mai tsaron gida na Torres ya fito, saboda haka tun daga kusa da tsakiyar fili sai ya auna kwallo sama ta je ta shiga ragar ‘yan Torres, kamar yadda yake a bidiyo na kasa.
Wai shin idan kai ne yaya zaka yi da bugun fenaritin nan? A yi mana sharhi a kasa, ko a gefe daga dama.

8 responses to “Idan Kai Ne Yaya Zaka Yi? Fadi Gaskiya!”

 1. Adam says:

  Abinda dan wasan yayi ya dace.

 2. Ni kam xan maida hankali nasha, saboda ai dama kwallon kafa ilmine da dabara ba karfi ba

 3. Fahad Madobs says:

  Agaskiya in nine zan yi kokarin sakata araga. Amma abinda danwan yayi daidai kuma zan iya koyi dashi yanzu.

 4. Aliyu says:

  Mhm!wannan dan wasa yana bukatar yaga likita.

 5. Alkalan wasa basu da gaskiya says:

  An gano alkalan wasa basuda gaskiya

 6. galadima says:

  Ni kan ga gani na baiyi dai-dai ba saboda umfanin dara kasawa

 7. haruna irani m/fashi says:

  koma waye zaiji badadi sabida yankallo masu raayina da masuson kulub din zasuji kabata masu rai bayan haka farin jininka awajen mutane zai iya raguwa dole kaji badadi

 8. agaskiya hakan mafi da cewa yayi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

About

Shafin Tamaular Duniya

Dandalin wadanda ke sha’awa, kuma suka san abinda zasu iya fada kan kwallon kafa. Yaro ba ya wargi!!

Categories

Calendar

March 2012
M T W T F S S
« Feb   Apr »
 1234
567891011
12131415161718
19202122232425
262728293031