Older: Idan Kai Ne Yaya Zaka Yi? Fadi Gaskiya! | Newer: ban Kwana Da Birgit Prinz |
Dukkan ‘Yan Kwallo A Turai Sun Karrama Fabrice Muamba
Posted March 24th, 2012 at 6:15 pm (UTC+0)
Ba kasafai ake samun abu guda dake hada kan ‘yan wasan Tamaula na Turai baki daya ba, im ban da irin wannan tsautsayi da ya abka kan Fabrice Muamba na kungiyar Bolton Wanderers, mai wasa a Premier League na Ingila.
Mahaifin Muamba da wasu ‘yan’uwansa sun bayar da sanarwa su na godewa ‘yan kallo, da ‘yan wasan Tamaula da ma’aikatan asibiti a saboda tallafi da goyon bayan da suka nuna musu. Muamba ya fadi kasa haka kwatsam kafin a tafi hutun rabin lokaci a yayin da Bolton ta ke buga wasan kwata fainal na kofin kalubalenka da Tottenham ranar asabar da ta shige.
Har yanzu tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafar Ingila ta ‘yan kasa da shekara 21 yana cikin matsanancin hali a Asibitin Kirji na London. An ce sai da ma’aikatan jinya suka shafe mintoci 78 su na aiki a kansa da injin sake tayar da zuciya kafin zuciyar tasa ta sake bugawa da kanta. An ce yayi magana da likitoci ranar litinin.
Mahaifinsa, Marcel Muamba, yace Muamba yana murmurewa duk ad cewa har yanzu yana cikin matsanancin hali, kuma ya roki jama’a da su ci gaba da yi masa addu’a.
A duk fadin nahiyar Turai, ‘yan wasan Tamaula sun sanya rigunan nuna jimami ga Muamba wadanda a jiki aka rubuta “Allah Kawo Sauki Fabrice” ko kuma “Get Well Soon fabrice” a turance.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tana cikin wadanda suka ware lokaci musamman domin jimamin wannan abu da ya samu Muamba. Shi ma shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, Sepp Blatter, yayi magana da shugaban kungiyar Bolton, ya kuma nemi da a rika sanar da shi halin da Muamba yake ciki.
Kungiyar Bolton ta ce irin sakonnin fatar alherin da ta rika samu, ta ke kuma kan samu daga magoya bayan kungiyoyi dabam-dabam a fadin duniya, abin ya shige misali.
Older: Idan Kai Ne Yaya Zaka Yi? Fadi Gaskiya! | Newer: ban Kwana Da Birgit Prinz |
2 responses to “Dukkan ‘Yan Kwallo A Turai Sun Karrama Fabrice Muamba”
Kaga turai inda anka san darajjar dan Adam kuma dan kwallo, Gaskiya ina tausaya masa game da irin halin da yashiga
get well soon muamba