
Birgit Prinz ta Jamus tana ban kwana da 'yan kallo a bayan wasanta na karshe na ban kwana yau talata, 27 maris 2012 a tsakanin kulob dinta FFC Frankfurt da kungiyar kwallon kafar mata ta kasar Jamus. Sau uku Birgit Prinz tana zamowa zakarar kwallon kafar mata ta duniya.
A yau talata, 27 Maris 2012 masu sha’awar tamaular mata a duniya suka yi ban kwana da daya daga cikin mashahuran masu buga kwallon mata, Birgit Prinz ta Jamus, wadda sau uku tana zamowa zakarar kwallon kafar duniya ta FIFA.
Prinz, mai shekaru 34 da haihuwa, ta lashe kofin duniya na mata har sau biyu a kungiyar kwallon kafar mata ta Jamus.
Dubban jama’a, cikinsu har da shugaban hukumar kwallon kafa ta Jamus, suka cika filin wasa na Frankfurt a yau talata, a lokacin da Prinz ta yi wasanta na karshe. Gaba daya filin ya mike tsaye ana tafa mata, lokacin da ta bar wasa ana kusa da tashi.
Prinz ta samu zuwa gasar cin kofin duniya har sau biyar, inda ta jefa kwallaye har 14. Marta ta kasar Brazil ce kadai macen da ita ma ta jefa kwallaye 14 a raga lokacin gasar cin kofin duniya.
A wasanni har 214 da Prinz ta buga ma kasar Jamus, ta saka kwallaye 128 a raga.
Har ila yau, ta taimakawa kasar Jamus wajen lashe kofin zakarun Mata na Turai sau biyar, tare da lambobin Tagulla 3 a wasannin Olympics.

Birgit Prinz rike da furannin da aka ba ta jim kadan kafin wasanta na karshe yau talata, 27 Maris 2012 a Frankfurt