Older: ban Kwana Da Birgit Prinz | Newer: Fabrice Muamba Yace Bai Ji Zafin Komai Ba A Lokacin Da Ya Fadi Ya Suma, Zuciyarsa Ta daina Bugawa |
Sabon Salo, Sabon Yayi
Posted April 2nd, 2012 at 5:51 am (UTC+0)
A ranar asabar 31 Maris 2012 ne kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta yi kaca-kaca da kungiyar Osasuna da ci 5 da 1, a karawarsu ta wasannin lig-lig na Spain. Cristiano Ronaldo dan kasar Portugal shi ya jefa kwallaye biyu daga cikin guda biyar din.
Kwallon farko, irin kwallon nan ne da ake kira “Makami mai cin dogon zango” domin tun daga nesa ya sako ta har cikin raga.
Amma babban abinda ya fi burge jama’a ‘yan kallo da sauran ‘yan wasa shi ne a lokacin da shi Ronaldo yake murnar jefa wannan kwallo, sai ya ja wandonsa sama, yana nuna ma jama’a cinyarsa, watau kamar yana fadin cewa irin karfin dake jikin cinyar tasa ta shige misali.
Wannan abu ya burge sauran ‘yan wasan Real Madrid, domin kamar yadda za a gani cikin bidiyo dake kasa, a bencinsu ma sai sauran ‘yan wasan suka fara kwaikwayon wannan abu da Ronaldo yayi, su na nuna cinyarsu domin fadawa duniya cewa su fa ba kanwar lasa ba ne.
Older: ban Kwana Da Birgit Prinz | Newer: Fabrice Muamba Yace Bai Ji Zafin Komai Ba A Lokacin Da Ya Fadi Ya Suma, Zuciyarsa Ta daina Bugawa |
15 responses to “Sabon Salo, Sabon Yayi”
Duk yagama tsalla tsallansa messi zaiyi scorer a spain in Allah ya yarda up Barca
Dan sun ci Osasuna ba birgewa ba ce. Ya bari sai ya ci Barcelona sannan sai ya yi kurin.
kamashi messi yafara kori harma yana neman yayi tsirara up man u
kamashi messi yafara kuri daga cin kwallo biyu naima yake yayi tsirara
daga cin kwallo biyu yafara kuri harma yana neman yayi tsirara kamashi messi
Cr7, sarkine kuma shine dankali sha kushe, gashi marincin bisa kan dutsi bai fito ba sai da ya shirya, gadangaren baki tulu……. Gabadai gabadai cr7
habadai to kokarinmi kayi.
habadai.
hahaha.
Ay wanda bayasonka ko ka cika mashi tankar ruwa da cokali a hamadar sahara , ba ka taba burgeshi.
Ay wanda bayasonka ko ka cika mashi tankar ruwa da cokali a hamadar sahara , ba ka taba burgeshi. Gabadai! Gabadai! Na maganin gaba. Na special one!
Hahaha
Cr7 sai ma ranar
gaskiyane Ronaldo, domin wanda ya’iya shi ga salo
Haba yan uwa munga NASA kurin sauran Naku ba girin girin ba dai tai mai