Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi waje-rod da kungiyar dake rike da kofin zakarun kulob-kulob na Turai, FC Barcelona, daga gasar ta bana, ta kuma samu kaiwa ga wasan karshe bayan da suka tashi da ci 2-2 daren talata a filin wasa na Camp Nou dake Barcelona. Duk da cewa an kori dan wasan Chelsea daga filin, suka rage saura 10 kawai.
Wannan ya sa Chelsea zata wuce da ci 3-2 idan an hada da nasarar da ta samu a karawarsu ta farko.
Da farko, kamar FC Barcelona zata kai labari a bayan da Sergio Busquets ya jefa mata kwallo a minti na 35 da fara wasa, sannan Andres Iniesta ya kara na biyu a minti na 44.
A minti na 37 da fara wasa, an kori dan wasan Chelsea John Terry daga fili saboda ketar da alkalin wasa yace yayi ma dan wasan FC Barcelona mai suna Alexis Sanchez.
Ramires ya ramawa Chelsea kwallo daya ana dab da zuwa hutun rabin lokaci.
An ba dan wasan Barcelona Lionel Messi bugun fenariti, amma sai ya kasa sakawa cikin raga a bayan da Didier Drogba yayi keta ma Cesc Fabregas.
Fernando Torres ya tabbatrwa da ‘yan Chelsea nasara a wannan karawa a lokacin da ya jefa kwallo na biyu a minti na 90 da wasa.
Chelsea, wadda ba ta taba lashe gasar zakarun kulob-kulob na Turai ba, zata jira wadda zata yi nasara a karawar da za a yi larabar nan a tsakanin Real Madrid da Bayern Munich.
Za a yi karawar karshe ranar 19 ga watan Mayu a birnin Munich na kasar Jamus.
Older: Fabrice Muamba Yace Bai Ji Zafin Komai Ba A Lokacin Da Ya Fadi Ya Suma, Zuciyarsa Ta daina Bugawa | Newer: Manchester City, Zakara? |
Chelsea ta Yi Waje Rod Da FC Barcelona A Gasar Zakarun Kulob-Kulob Na Turai
Posted April 25th, 2012 at 3:26 am (UTC+0)
Older: Fabrice Muamba Yace Bai Ji Zafin Komai Ba A Lokacin Da Ya Fadi Ya Suma, Zuciyarsa Ta daina Bugawa | Newer: Manchester City, Zakara? |
3 responses to “Chelsea ta Yi Waje Rod Da FC Barcelona A Gasar Zakarun Kulob-Kulob Na Turai”
Datz Gud. Keep it up chelsea.
mu real madrid muna sarai zamuci bayen munchen 3 da 1
Salisu, abin sai hakuri. Reshe ya juya da mujiya!!!