Showing Archived Posts

Wace Manchester Eden Hazard Zai Zaba?

Posted May 28th, 2012 at 1:45 am (UTC+0)
Leave a comment

Har yanzu Eden Hazard na kungiyar Lille dake neman sabon kulob bai bayyana inda ya fi so ya dosa ba, amma masu zawarcinsa sun yi yawa, cikinsu har da kungiyoyin kwallon kafa guda biyu dake birnin Manchester: City da United. Ita ma sabuwar zakarar tamaula ta nahiyar Turai, Chelsea ta Ingila, tana cikin masu zawarcin […]

Laifin Bayern Munich Ne – Ba Gwanintar Chelsea Ba

Posted May 21st, 2012 at 5:47 am (UTC+0)
4 comments

Dan tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa zai buga. Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta kasar Jamus ita ta jefa kanta cikin ukubar bakin ciki da radadin zuciya, bayan da ta watsar da babbar damar da ta samu ta yin abin tarihi a gasar cin kofin zakarun Turai, kuma a cikin filin wasanta, […]

Manchester City Ta Tsamo Kitse A Wuta

Posted May 13th, 2012 at 11:16 pm (UTC+0)
1 comment

Magoya bayan kungiyar Manchester City sun fara kuka, duniya ta rikice musu ana dab da tashi daga wasan da suka yi da Queens Park Rangers a filin wasa na Etihad dake birnin Manchester. A can Sunderland kuwa, magoya bayan Manchester United sai murna suke yi, ‘yan wasansu kuma har sun fara layi su na jiran […]

Up Yaya Toure – Sir Alex Ferguson Ma Ya Mika Wuya, Ko Kusan Hakan

Posted May 8th, 2012 at 1:36 am (UTC+0)
2 comments

Idan ba wata kaddara daga Ubangiji ba, babu abinda zai hana Manchester City doke Manchester United wajen lashe kofin wasannin lig-lig na bana a kasar Ingila. Shi kansa manajan United, Sir Alex Ferguson, cewa yayi, “watakila hannayensu biyu na kan wannan kofi a yanzu haka.” Tauraron ‘yan wasan Manchester City shi ne Yaya Toure, wanda […]

Allah Ya Jikan Rashid Yekini, Mun Yi Rashi

Posted May 7th, 2012 at 4:22 am (UTC+0)
20 comments

Duk wani masoyin Najeriya da kwallon kafa a Najeriya da Afirka, ba zai taba mantawa da Rashid Yekini ba. Rashid Yekini, ya rasu ranar jumma’a a Ibadan, yana da shekaru 48 da haihuwa. Babu wani dan kwallon da ya taba jefa ma Najeriya kwallaye kamarsa, inda a cikin wasanni 58 da ya buga ma kungiyar […]

Real Madrid Ta Zamo Zakarar Spain A Bana

Posted May 3rd, 2012 at 4:44 am (UTC+0)
Leave a comment

Real Madrid ta zamo zakarar wasannin rukunin lig-lig na kasar Spain, La Liga, a karon farko cikin shekaru 4, ta kawo karshen mulkin babbar abokiyar adawarta FC Barcelona, bayan da ta doke Athletic Bilbao da ci 3-0 laraba. Gonzalo Higuain da Mesut Ozil da kuma Cristiano Ronaldo sune suka jefa kwallaye ukun da suka ba […]

Manchester City, Zakara?

Posted May 1st, 2012 at 5:24 am (UTC+0)
5 comments

Marubucin tamaula Martin Rogers yace ba wai an nada sabon zakaran lig-lig na kasar Ingila ne a karawar da aka yi litinin a tsakanin Manchester City da Manchester United ba, amma duk wanda ya kalli wasan zai ga kamar abinda aka yi ke nan. dalili shi ne wadannan kungiyoyi biyu sune ke sama a rukunin […]

About

Shafin Tamaular Duniya

Dandalin wadanda ke sha’awa, kuma suka san abinda zasu iya fada kan kwallon kafa. Yaro ba ya wargi!!

Categories

Calendar

May 2012
M T W T F S S
« Apr   Jun »
 123456
78910111213
14151617181920
21222324252627
28293031