
Rashid Yekini, lokacin da ya jefa ma Najeriya kwallonta na farko a gasar cin kofin duniya a 1994.
Duk wani masoyin Najeriya da kwallon kafa a Najeriya da Afirka, ba zai taba mantawa da Rashid Yekini ba.
Rashid Yekini, ya rasu ranar jumma’a a Ibadan, yana da shekaru 48 da haihuwa.
Babu wani dan kwallon da ya taba jefa ma Najeriya kwallaye kamarsa, inda a cikin wasanni 58 da ya buga ma kungiyar Super Eagles, ya jefa kwallaye har 37.
Amma babban abinda mutane suka fi tunawa a game da Rashid Yekini, wanda aka haifa ranar 23 ga watan Oktoba, 1963 a Kaduna, shi ne irin rugawa da gudun da yayi ya shiga cikin ragar ‘yan kasar Bulgariya, ya rike raga yana ihu da iyakar karfinsa, a bayan da ya jefa ma Najeriya kwallonta na farko a gasar cin kofin kwallon kafar duniya a 1994 a Amurka.
haka kuma, Rashid Yekini, shi ne dan Najeriya na farko da aka taba zaba a matsayin zakaran kwallon kafa na nahiyar Afirka a 1993, kuma shekara daya bayan wannan, ya taimakawa ‘yan Super Eagles na Najeriya suka ciwo kofin zakarun kasashen Afirka.
Shi ne dan wasan da ya fi jefa kwallaye cikin raga a wasannin lig-lig na kasar Portugal a 1993-1994 a lokacin da yake buga wasa ma kungiyar Vitoria Setubal. A shekaru 4 da yayi a wannan kulob, Rashid Yekini ya jefa kwallaye 90 cikin raga.
Yayi wasa a kasashe da dama kafin ya zo yayi ritaya a kungiyar Julius Berger ta Najeriya a 2003.
A bayan fage, Rashid Yekini mutum ne mai shiru-shiru, wanda bai cika shiga harkar da ba tasa ba. Abin koyi ga kowa.
Allah Ya jikan Rashid Yekini, Ya sa mutuwa hutu ne gare shi, amin summa amin.

Marigayi Rashid Yekini
20 responses to “Allah Ya Jikan Rashid Yekini, Mun Yi Rashi”
Kaji wadanda suka bautawa kasarsu bilhaqqi da gaskiya saboda kishi bawai don kudiba sabanin yan wasan mu nayanzu marasa kishi kwadayayyu shiyasa bazamu taba mantawa da irin su rashidi yekini ba Allah yaji kansa ameen.
Wannan magana ta ka gaskiya ce Sharif. Kaicon ‘yan wasanmu na yanzu, wadanda idan sun je fili ma sai sun yi lada da officials kafin su buga kwallon, sai sun ji abinda za a ba su!!!
ALLAHU AKBAR! ALLAHU AKBAR!! ALLAHU AKBAR!!!
ALLAH YA JIKAN GWARZO! MUNYI RASHIN JAGORA,SHUGABA,ABIN KOYI.
RASHIDI YAKINI MUTUM NE HAZIKI,MAI NEMAN MA SHUWA GABANINSA DA KASARSA SUNA BADON KANSA KAWAI BA,SE DON ALUMMAR SA DA KASARSA BAKI DAYA.
SHI MUTUM NE HAZIKI, BA MAI YAWAN NEMAN DUKIYABA,SABANIN YAN KWALLON YANZU MASU NEMAN TARA ABIN DUNIA KAWAI.
ALLAH YA JIKAN GWARZO NA.
YAN BAYA,AN BAR MAKU ABIN KOYI.
WASSALAM.
Kulllu nafsin, za`i katil nafsi.Allah ya jikan Rashid yakeni.Mu kuma Allah ya kyauta namu zuwan. Amin suma amin.
The contribution he gave in Nigerian foot ball will ever remain in hitory, May Soul of Rashid rest in perfects peace witrh all his sins forgiven,ameen.
Allah jikan Rashid yakini Allah bamu wadanda zasu maye gurbin shi. Suyi dan kishin kasa badan kansuba ameen.
Wannan shaharren dan wasa an dai riga an rasashi,kuma baza a taba maye gurbinsaba.yan wasan mu nayanzu allah wadaranku ya sauya mana ku da irin su marigayi rashid ba irinku rubabbu ba marasa kishin kasarsu.
Allah ya ba mu irinsu Rashid Yekini masu yi domin kishin kasarsu!
allah ya jikan sa
ALLAH YAJIKAN KA YA GAFARTAR MAKA AMEEN YAN KISHI BA YAN CIN KUDI DA KISTO BA SAI KACE MATA
ALLAH YAKJIKAN ALLAH YASADASHI DA RAHAMA
Allah yajikan musulmai yakuma gafartamana Ameen Summa Ameen,
Allah yakuma bamu irin RASHIDI YAKINI AMEEN.
Allah ya jikansa yasa ya huta
Allah ya ga far tawa rashid yakini amin.
Rashin maza baza abin bakin cikine allah jikan maza
Gaskiya Nigeria tayi baban rashin Jarumi Mai kishin Kasa, ALLAH YAJIKANSHI DA RAHAMA!
Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un. KULLI NAFSIN ZA’IKATUL MAUT. Ubangiji allah jikanshi kuma allah masa rahama ameen. Mu kuma idan tamu tazo allah sa mu cika da imani da kalmar shahada amen summa amen.
Allah ya jikanshi
Allah yasa yanzu yakini Yana cikin aljannar firdausi Amin.
Masuyi dan yankasarsuba