Idan ba wata kaddara daga Ubangiji ba, babu abinda zai hana Manchester City doke Manchester United wajen lashe kofin wasannin lig-lig na bana a kasar Ingila.
Shi kansa manajan United, Sir Alex Ferguson, cewa yayi, “watakila hannayensu biyu na kan wannan kofi a yanzu haka.”
Tauraron ‘yan wasan Manchester City shi ne Yaya Toure, wanda a ranar lahadi 6 Mayu 2012, ya jefa kwallaye har biyu a ragar ‘yan wasan kungiyar Newcastle United, ya kawar da duk wata tababar da ake yi cewa bana taurarin City ne suke haskakawa.
Yanzu abinda ya rage kawai shi ne City ta doke kungiyar Queens Park Rangers wadda ke can baya a wasan karshe da zata buga ranar lahadi mai zuwa. Idan ta yi haka, zata lashe kofinta na farko tun 1968.
Idan City ta doke QPR, to United zata bukaci lashe wasanta na karshe da ‘yan Sunderland da ci 9 da babu, domin ta kawar da yawan kwallayen da City ke da shi a ragar abokan karawarta, abinda ake ganin zai yi wuya.
Hausawa suka ce ba a san ma ci tuwo ba sai miya ta kare.
2 responses to “Up Yaya Toure – Sir Alex Ferguson Ma Ya Mika Wuya, Ko Kusan Hakan”
Wannan hakane,aman kungiyar da manchester united zata kara wasan karshe,Sunderlan ce
Godiya buhu-buhu Ameen. Watakila tunanin Ipswich ya sanya na sa sunanta a cikin wannan labarin, duk da cewa ba ta ma cikin EPL. Nagode kwarai da wannan gyara naka, na kuma gyara!!