Older: Up Yaya Toure – Sir Alex Ferguson Ma Ya Mika Wuya, Ko Kusan Hakan | Newer: Laifin Bayern Munich Ne – Ba Gwanintar Chelsea Ba |
Manchester City Ta Tsamo Kitse A Wuta
Posted May 13th, 2012 at 11:16 pm (UTC+0)
Magoya bayan kungiyar Manchester City sun fara kuka, duniya ta rikice musu ana dab da tashi daga wasan da suka yi da Queens Park Rangers a filin wasa na Etihad dake birnin Manchester.
A can Sunderland kuwa, magoya bayan Manchester United sai murna suke yi, ‘yan wasansu kuma har sun fara layi su na jiran a zo a mika musu kofin zakarun wasannin lig-lig na Premier.
A daidai lokacin, kungiyar Queens Park Rangers tana gaban Manchester City da ci 2-1. Kuma idan aka tashi a haka, mafarkin Manchester City na lashe kofin lig a bana, sai dai a mafarkin kawai.
Amma mutum yana nasa, Allah Yana nasa. Babu wanda ya san cewa a she a cikin mintoci 5 da aka kara na bata lokaci, manchester City zata jefa kwallaye har guda biyu, zata lashe wannan wasa, kuma reshe zai juya da mujiya: magoya bayanta za su barke da murna, yayin da magoya bayan United za su shiga cikin bakin ciki.
Da farko dai Edin Dzeko ya jefa kwallo da kai a lokacin bugun kwana, daga nan kuma ana saura dakikoki kadan a hura tashi baki daya sai Sergio Aguero, surukin Maradona, ya jefa kwallon da watakila a duk rayuwarsa bai taba jefa mai muhimmancin wannan ba. Ga ‘yan City dai wannan kwallon ya fiye musu komai a duniya a yau din nan.
Jefa wannan kwallo ke da wuya sai aka hura tashi, fili ya rikice, duniya ta koma fari fat ga ‘yan City, yayin da ta yi duhu wuluk ga ‘yan United har ma da ‘yan wasan United da manajansu Sir Alex Ferguson, wadanda shirinsu na amsar wannan kofi ya koma mamaki mai tsanani na yadda aka yi har City ta komo ta lashe wannan kwallo nata da QPR.
Wannan shi ne karon farko da City ta lashe kofin wasannin lig-lig na Ingila a cikin shekaru 44. Tun ma da wasannin suka koma Premier League, ba ta taba lashewa ba, kullum sai dai ta kalli makwabtanta ‘yan United su na murna.
Wannan rana ce mai muhimmanci ga manajan ‘yan Manchester City, Roberto Mancini, wanda aka yi ta rade-radin cewa masu kungiyar larabawa zasu kore shi idan ba su lashe kofin nan ba. Dalili shi ne irin makudan kudaden da suka kashe kan kungiyar domin farfado da ita.
Da ma kwararru suka ce lashe kofin farko shi ne mawuyaci, kamar yadda ‘yan City suka gani. Watakila na biyu da na ukun su na iya zuwa da sauki fiye da yadda suka gani a bana.
Older: Up Yaya Toure – Sir Alex Ferguson Ma Ya Mika Wuya, Ko Kusan Hakan | Newer: Laifin Bayern Munich Ne – Ba Gwanintar Chelsea Ba |
One response to “Manchester City Ta Tsamo Kitse A Wuta”
allah ya taimaka ameen.