Laifin Bayern Munich Ne – Ba Gwanintar Chelsea Ba

Posted May 21st, 2012 at 5:47 am (UTC+0)
4 comments

Anatoliy Tymoshchuk na Bayern Munich, a tsakiya, tare da sauran 'yan kungiyar cike da bakin ciki a bayan da Didier Drogba ya buga fenaritin da ya ba Chelsea kofin zakarun kulob-kulob na Turai a Munich, asabar 19 Mayu 2012.

Anatoliy Tymoshchuk na Bayern Munich, a tsakiya, tare da sauran 'yan kungiyar cike da bakin ciki a bayan da Didier Drogba ya buga fenaritin da ya ba Chelsea kofin zakarun kulob-kulob na Turai a Munich, asabar 19 Mayu 2012.


Dan tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa zai buga.
Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta kasar Jamus ita ta jefa kanta cikin ukubar bakin ciki da radadin zuciya, bayan da ta watsar da babbar damar da ta samu ta yin abin tarihi a gasar cin kofin zakarun Turai, kuma a cikin filin wasanta, a gaban magoya bayanta.
Bayern ta yi sakaci ta bar Chelsea ta rama kwallo ana saura minti biyu rak a tashi, sannan ta jefar da bugun fenariti a lokacin da aka yi karin lokaci, ta kuma zo ta jefar da wasu fenaritin guda biyu, ta bar kofin ya sulale daga hannunta.
Wannan lamarin ya faru ne a filin wasan ‘yan Bayern Munich, watau Allianz Arena, wanda aka zaba don buga wannan wasa fiye da shekara guda da ta shige, tun ma ba a san ko su wanene zasu buga ba. Idan da Bayern ta yi nasara, to da ta zamo kungiyar farko da zata lashe kofin zakarun kulob na Turai a cikin filin wasanta. Tun da aka kirkiro wannan gasa shekaru 20 da suka shige, babu kungiyar da ta taba yi.
Roberto Di Matteo na Chelsea yace, “idan wasa yayi zafi, komai na iya faruwa, tilas ka matsa lamba a kan abokiyar karawarku don ka ga abinda zai faru.”
Kowa ya san kungiyoyin kasar Jamus a zaman babu wanda ya kai su juriya da daukar matsi ba tare da nuna zafin kai ba. Kai, ba a taba doke kungiyar kwallon kafa ta kasar Jamus a bugun fenariti ba yau fiye da shekaru 30.
Amma ‘yan kungiyar Bayern sun karaya a lokacin da bai kamata su karaya ba. Kada a mance kungiyar ta yi hasarar kofin wasannin lig-lig na Bundesliga, da kuma kofin kalubalenka na kasar jamus. Ga na Turai ma ya sullube mata, a gaban magoya bayanta, a filinta, a garinta, kuma a kasarta.
'Yan wasan Chelsea su na fareti, yayin da Didier drogba ke rike da kofin zakarun kulob-kulob na Turai, bayan da suka doke Bayern Munich ranar asabar.

'Yan wasan Chelsea su na fareti, yayin da Didier drogba ke rike da kofin zakarun kulob-kulob na Turai, bayan da suka doke Bayern Munich ranar asabar.


ba dai zan cika ku da surutu ba. A karshe, haka ‘yan wasan Bayern suka zube a kasa, su na cikin tsananin bakin ciki da kukar zuci, ganin yadda wannan kofi ya shiga hannunsu ya sullube tun kafin su rike shi.

4 responses to “Laifin Bayern Munich Ne – Ba Gwanintar Chelsea Ba”

  1. naseer shuaibu says:

    we tnx god for the victory which every team in the world need up chelseafc the pride of london ooops i mean the pride of england.

  2. lawal garba says:

    ba gaskiya bane, in kun san chelsea tun lokacin jose morinho ya gina team dinne don winin ba bata lokaciba a cikin fili[sakamako kawai]sobada haka fadin cewa ba gwanjntar su bace ba daidai bane.bayern sunaso bayern naso su burge yan kallo su kuma chelsea na neman sakamako.sabo da haka sanin bukatun wasa ya jawo masu nasara.

  3. abdullahi says:

    inna tausayawa bayarn sai su dangana sai wata shekaran su bada himma ko allaha zai basu sa,a.

  4. Aliyu Bala says:

    Ina mai matukar taya kulob din Chelsea farin cikin sa’an da kuma nasasan da Allah ya basu a wannan kakar wasan da ta wuce.

    ‘Yan-adawa sai hakuri ta Allah ba taku ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

About

Shafin Tamaular Duniya

Dandalin wadanda ke sha’awa, kuma suka san abinda zasu iya fada kan kwallon kafa. Yaro ba ya wargi!!

Categories

Calendar

May 2012
M T W T F S S
« Apr   Jun »
 123456
78910111213
14151617181920
21222324252627
28293031