Wariyar Launin Fata – Ingila Ta Ce Zata Janye Daga Wasa Idan Aka Ci Mutuncin ‘Yan Wasanta Bakaken Fata

Posted June 11th, 2012 at 6:54 am (UTC+0)
2 comments

'Yan wasan Ingila su na motsa jiki a Donetzk, Ukraine, kafin wasan da zasu buga da Faransa litinin da maraice

'Yan wasan Ingila su na motsa jiki a Donetzk, Ukraine, kafin wasan da zasu buga da Faransa litinin da maraice


Kyaftin na kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila, Steven Gerrard, yace lallai idan har ‘yan kallo ko ‘yan wasan kasa suka kuskura suka nemi cin mutuncin ‘yan wasansu bakar fata, to ko ana tsakiyar wasa ne zai sa ‘yan kungiyar su fita su bar fili a wajen gasar cin kofin kasashen Turai, EURO 2012.
Kasashen dake daukar bakuncin wannan gasa, Poland da Ukraine, duk sun yi kaurin suna a saboda rahotannin cin mutuncin wasu jinsuna da nuna zunzurutun wariyar launin fata.
A lokacin da ‘yan wasan kasar Netherlands suke motsa jiki kafin wasansu na farko a wurin wannan gasa, an yi ta zagin bakaken fata a cikin ‘yan wasansu ana ce musu birai.
A ranar asabar ma, dan wasa daya tak bakar fata dake cikin ‘yan wasan kasar Czech, Theodor Gebre Selaisse, an yi ta muzanta shi a lokacin da suek bugawa da kasar Rasha.
Ingila ta ce ba zata yarda da wannan. Babban abinda ya fi damunta ma shi ne daga cikin ‘yan wasan kasar su 23, guda 8 bakar fata ne. Iyalansu da dama sun ki tafiya wurin kallon wasan saboda rahotannin cewa ana muzantawa wasu jinsuna a kasashen da ake gudanar da wannan gasa.
A yau litinin, Ingila zata kara da Faransa a Donetsk a kasar Ukraine, kuma kyaftin na Ingila Gerrard yace sun zauna sun tattauna matakan da zasu dauka idan aka nuna musu wariyar launin fata.
Kyaftin na kungiyar kwallon kafa ta Ingila, Steven Gerrard, wanda yace idan aka kuskura aka muzantawa 'yan wasansu bakar fata a gasar cin kofin kasashen Turai, EURO 2012, to zasu fita su bar filin wasa domin kasashen dake daukar nauyin gasar, Ukraine da Poland sun yi kaurin suna wajen cin mutuncin wasu jinsuna a fagen tamaula.

Kyaftin na kungiyar kwallon kafa ta Ingila, Steven Gerrard, wanda yace idan aka kuskura aka muzantawa 'yan wasansu bakar fata a gasar cin kofin kasashen Turai, EURO 2012, to zasu fita su bar filin wasa domin kasashen dake daukar nauyin gasar, Ukraine da Poland sun yi kaurin suna wajen cin mutuncin wasu jinsuna a fagen tamaula.


Gerrard yace idan har suka ga irin wannan muzanci, abinda zasu fara yi shi ne zasu tsayar da wasa su yi magana da alkalin wasan a kai. Idan ba su gamsu ba zasu fice daga filin.
Wasu shahararrun wasan Tamaula ma, kamar Ruud Gullit, tauraron kwallon kafa dan kasar Netherland wanda ya lashe kofin na Euro ma kasarsa a 1988, ya tofa albarkacin baki yana mai cewa, “Idan haka ya faru, bai kamata ‘yan wasa su rufe baki su ci gaba da wasa kamar yadda ya faru a zamaninmu ba. Idan har aka ci mutuncin wani saboda jinsinsa ko launin fatar jikinsa, wannan dan wasa yana da ikon ficewa daga cikin filin.”
Shi ma wani babban dan siyasa na Ingila, Douglas Alexander, yayi kira ga Gerrard da ‘yan wasan na Ingila da kada su ji tsoron tsayar da wasa, kuma in sun ga ficewa daga fili ita ce mafi a’ala, to ya kamata a goyi bayansu idan sun yi.”
Amma kuma babban abinda aka fi tsoro shi ne cewa irin wannan cin zarafi na wariyar launin fata watakila sai idan an zo wasa a tsakanin Ingila da mai masaukin baki Ukraine a wasa na karshe na rukuninsu.
Ingila ma ta tura karin kwararru kan harkokin tsaro domin tabbatar da lafiyar ‘yan wasanta, bakake da farare.

2 responses to “Wariyar Launin Fata – Ingila Ta Ce Zata Janye Daga Wasa Idan Aka Ci Mutuncin ‘Yan Wasanta Bakaken Fata”

  1. Bala Dahiru says:

    Nima ina goyon bayan duk wanda aka nuna masa wariyan launin fata ya fice daga filin wasa

  2. kassim says:

    am also against the segregation.means if the discrimination happens between the players because of the colour ,let the fifa take action against any racisst either the players or the spectators.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

About

Shafin Tamaular Duniya

Dandalin wadanda ke sha’awa, kuma suka san abinda zasu iya fada kan kwallon kafa. Yaro ba ya wargi!!

Categories

Calendar

June 2012
M T W T F S S
« May   Jul »
 123
45678910
11121314151617
18192021222324
252627282930