Older: Wariyar Launin Fata – Ingila Ta Ce Zata Janye Daga Wasa Idan Aka Ci Mutuncin ‘Yan Wasanta Bakaken Fata | Newer: Manchester United Ce Ta Daya A Duk Fadin Duniya |
Zinedine Zidane Zai Koyar Da ‘Yan Wasan Faransa?
Posted July 4th, 2012 at 4:52 am (UTC+0)
Leave a comment
Shugaban Hukumar Kwallon kafa ta Faransa yace Zinedine Zidane yana daya daga cikin mutanen da watan watarana zasu koyar da kungiyar kwallon kafa ta kasar, amma dai a yanzu kam ba shi zai maye gurbin Laurent Blanc wanda ya ajiye wannan mukami kwanakin baya ba.
Zidane yana daya daga cikin ‘yan wasan Tamaula da Faransawa suka fi karramawa, kasancewarsa yana cikin kungiyar kasar da ta lashe kofin duniya a 1998 da kuma kofin kasashen Turai na Euro a 2000. Yanzu dai shi ne darektan wasanni na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.
Zidane mai shekaru 40 da haihuwa, yana karatun difloma kan gudanar da harkokin wasanni a makarantar koyar da harkokin wasanni dake Limoges.
Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa, Noel Le Graet, yace yayi imani Zidane yana da kwarewa da hazakar zamowa mai koyar da wasanni na kungiyar kwallon kafar Faransa a nan gaba.
Le Graet, ya ci gaba da cewa, “babban abu ne cewa Zinedine Zidane ya bayyana sha’awar yin aiki tare da kungiyar kwallon kafa ta kasa ta Faransa a nan gaba, kuma idan hakan ba zai yiwu yanzu ba, yana kwadayin koyar da kungiyar ta kasa ko da nan da shekara goma ne.”
A yanzu dai kungiyar kwallon kafa ta Faransa, wadda aka fi sani da sunan Les Bleus ba ta da mai koyar da wasa a bayan da Laurent Blanc yayi murabus daga kan wannan mukami a karshen mako na sama. Ga shi kuma an fara shirye-shiryen gudanar da wasannin share fage na zuwa gasar cin kofin duniyar da za a yi a Brazil a 2014.
Older: Wariyar Launin Fata – Ingila Ta Ce Zata Janye Daga Wasa Idan Aka Ci Mutuncin ‘Yan Wasanta Bakaken Fata | Newer: Manchester United Ce Ta Daya A Duk Fadin Duniya |