
‘Yan wasan Najeriya rike da kofin zakarun Afirka da suka lashe bayan da suka doke Burkina Faso da ci daya da babu, ranar lahadi, 10 Fabrairu a Afirka ta Kudu.
A bayan da ta shafe shekaru har 19 tana fafutukar neman kofin zakarun kasashen Afirka, hakar Najeriya ta cimma ruwa a bayan da ta doke Burkina Faso da ci daya da babu a wasan karshe na gasar a kasar Afirka ta Kudu.
Sunday Mba, shi ne ya jefa ma Najeriya kwallonta a minti na 40 da fara wasan nan.
Rabon da Najeriya ta lashe wannan kofi tun 1994.
A lokacin da aka hura tashi daga wannan wasa, dubban ‘yan Najeriya, kama daga Lagos har zuwa Abuja, Enugu, Kaduna da Calabar, sun kwarara kan tituna su na murnar wannan nasara.
A Lagos, jama’a bdake murna sun yi ta harba irin kayan wasan wutar nan da ake kira Knockout.

Magoya bayan Najeriya su na murnar doke Burkina Faso da ta yi