A bayan da ta shafe shekaru har 19 tana fafutukar neman kofin zakarun kasashen Afirka, hakar Najeriya ta cimma ruwa a bayan da ta doke Burkina Faso da ci daya da babu a wasan karshe na gasar a kasar Afirka ta Kudu. Sunday Mba, shi ne ya jefa ma Najeriya kwallonta a minti na 40 […]
Chelsea Ta Zamo Kulob Din Turai Ta Wannan Shekara
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta Ingila ta sake cin moriyar lashe kofin zakarun kolob-kulob na Turaoi da ta yi kwanakin baya. A wannan karon, Gamayyar Kungiyoyin Kwallon Kafar Kasashen Turai, ta zabi Chelsea a zaman Kulob Din Turai Ta Wannan Shekara. Roberto Di Matteo ya jagoranci ‘yan wasan nasa zuwa ga nasara kan Bayern […]
Manchester United Ce Ta Daya A Duk Fadin Duniya
Kamar yadda duk mai karanta wannan zai iya sani, kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta yi hasarar kambun Premier League na wannan shekara a ranar karshe ta wasannin lig-lig na Ingila, a lokacin da abokiyar hamayyarta Manchester City ta tsamo kitse a wuta a kan ‘yan wasan Queens Park Rangers a watan Mayu. Amma […]
Zinedine Zidane Zai Koyar Da ‘Yan Wasan Faransa?
Shugaban Hukumar Kwallon kafa ta Faransa yace Zinedine Zidane yana daya daga cikin mutanen da watan watarana zasu koyar da kungiyar kwallon kafa ta kasar, amma dai a yanzu kam ba shi zai maye gurbin Laurent Blanc wanda ya ajiye wannan mukami kwanakin baya ba. Zidane yana daya daga cikin ‘yan wasan Tamaula da Faransawa […]
Wariyar Launin Fata – Ingila Ta Ce Zata Janye Daga Wasa Idan Aka Ci Mutuncin ‘Yan Wasanta Bakaken Fata
Kyaftin na kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila, Steven Gerrard, yace lallai idan har ‘yan kallo ko ‘yan wasan kasa suka kuskura suka nemi cin mutuncin ‘yan wasansu bakar fata, to ko ana tsakiyar wasa ne zai sa ‘yan kungiyar su fita su bar fili a wajen gasar cin kofin kasashen Turai, EURO 2012. Kasashen […]
Wace Manchester Eden Hazard Zai Zaba?
Har yanzu Eden Hazard na kungiyar Lille dake neman sabon kulob bai bayyana inda ya fi so ya dosa ba, amma masu zawarcinsa sun yi yawa, cikinsu har da kungiyoyin kwallon kafa guda biyu dake birnin Manchester: City da United. Ita ma sabuwar zakarar tamaula ta nahiyar Turai, Chelsea ta Ingila, tana cikin masu zawarcin […]
Laifin Bayern Munich Ne – Ba Gwanintar Chelsea Ba
Dan tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa zai buga. Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta kasar Jamus ita ta jefa kanta cikin ukubar bakin ciki da radadin zuciya, bayan da ta watsar da babbar damar da ta samu ta yin abin tarihi a gasar cin kofin zakarun Turai, kuma a cikin filin wasanta, […]
Manchester City Ta Tsamo Kitse A Wuta
Magoya bayan kungiyar Manchester City sun fara kuka, duniya ta rikice musu ana dab da tashi daga wasan da suka yi da Queens Park Rangers a filin wasa na Etihad dake birnin Manchester. A can Sunderland kuwa, magoya bayan Manchester United sai murna suke yi, ‘yan wasansu kuma har sun fara layi su na jiran […]
Up Yaya Toure – Sir Alex Ferguson Ma Ya Mika Wuya, Ko Kusan Hakan
Idan ba wata kaddara daga Ubangiji ba, babu abinda zai hana Manchester City doke Manchester United wajen lashe kofin wasannin lig-lig na bana a kasar Ingila. Shi kansa manajan United, Sir Alex Ferguson, cewa yayi, “watakila hannayensu biyu na kan wannan kofi a yanzu haka.” Tauraron ‘yan wasan Manchester City shi ne Yaya Toure, wanda […]
Allah Ya Jikan Rashid Yekini, Mun Yi Rashi
Duk wani masoyin Najeriya da kwallon kafa a Najeriya da Afirka, ba zai taba mantawa da Rashid Yekini ba. Rashid Yekini, ya rasu ranar jumma’a a Ibadan, yana da shekaru 48 da haihuwa. Babu wani dan kwallon da ya taba jefa ma Najeriya kwallaye kamarsa, inda a cikin wasanni 58 da ya buga ma kungiyar […]