Showing Archived Posts

Real Madrid Ta Zamo Zakarar Spain A Bana

Posted May 3rd, 2012 at 4:44 am (UTC+0)
Leave a comment

Real Madrid ta zamo zakarar wasannin rukunin lig-lig na kasar Spain, La Liga, a karon farko cikin shekaru 4, ta kawo karshen mulkin babbar abokiyar adawarta FC Barcelona, bayan da ta doke Athletic Bilbao da ci 3-0 laraba. Gonzalo Higuain da Mesut Ozil da kuma Cristiano Ronaldo sune suka jefa kwallaye ukun da suka ba […]

Manchester City, Zakara?

Posted May 1st, 2012 at 5:24 am (UTC+0)
5 comments

Marubucin tamaula Martin Rogers yace ba wai an nada sabon zakaran lig-lig na kasar Ingila ne a karawar da aka yi litinin a tsakanin Manchester City da Manchester United ba, amma duk wanda ya kalli wasan zai ga kamar abinda aka yi ke nan. dalili shi ne wadannan kungiyoyi biyu sune ke sama a rukunin […]

Chelsea ta Yi Waje Rod Da FC Barcelona A Gasar Zakarun Kulob-Kulob Na Turai

Posted April 25th, 2012 at 3:26 am (UTC+0)
3 comments

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi waje-rod da kungiyar dake rike da kofin zakarun kulob-kulob na Turai, FC Barcelona, daga gasar ta bana, ta kuma samu kaiwa ga wasan karshe bayan da suka tashi da ci 2-2 daren talata a filin wasa na Camp Nou dake Barcelona. Duk da cewa an kori dan wasan […]

Fabrice Muamba Yace Bai Ji Zafin Komai Ba A Lokacin Da Ya Fadi Ya Suma, Zuciyarsa Ta daina Bugawa

Posted April 23rd, 2012 at 2:50 am (UTC+0)
Leave a comment

Fabrice Muamba ya bayyana cewa bai ji zafin komai ba a lokacin da zuciyarsa ta tsaya ta daina bugawa lokacin da yake wasa ma kungiyarsa ta Bolton Wanderers a watan da ya shige. An sallami Muamba daga asibiti tun ranar litinin da ta shige, kuma ya fara kokarin murmurewa a bayan da zuciyarsa ta daina […]

Sabon Salo, Sabon Yayi

Posted April 2nd, 2012 at 5:51 am (UTC+0)
15 comments

A ranar asabar 31 Maris 2012 ne kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta yi kaca-kaca da kungiyar Osasuna da ci 5 da 1, a karawarsu ta wasannin lig-lig na Spain. Cristiano Ronaldo dan kasar Portugal shi ya jefa kwallaye biyu daga cikin guda biyar din. Kwallon farko, irin kwallon nan ne da ake kira […]

ban Kwana Da Birgit Prinz

Posted March 27th, 2012 at 7:46 pm (UTC+0)
Leave a comment

A yau talata, 27 Maris 2012 masu sha’awar tamaular mata a duniya suka yi ban kwana da daya daga cikin mashahuran masu buga kwallon mata, Birgit Prinz ta Jamus, wadda sau uku tana zamowa zakarar kwallon kafar duniya ta FIFA. Prinz, mai shekaru 34 da haihuwa, ta lashe kofin duniya na mata har sau biyu […]

Dukkan ‘Yan Kwallo A Turai Sun Karrama Fabrice Muamba

Posted March 24th, 2012 at 6:15 pm (UTC+0)
2 comments

Ba kasafai ake samun abu guda dake hada kan ‘yan wasan Tamaula na Turai baki daya ba, im ban da irin wannan tsautsayi da ya abka kan Fabrice Muamba na kungiyar Bolton Wanderers, mai wasa a Premier League na Ingila. Mahaifin Muamba da wasu ‘yan’uwansa sun bayar da sanarwa su na godewa ‘yan kallo, da […]

Idan Kai Ne Yaya Zaka Yi? Fadi Gaskiya!

Posted March 17th, 2012 at 5:38 pm (UTC+0)
8 comments

Na san watakila mafi yawan masu karanta wannan ba su san wata gasar da ake kira “Coppa Italia Dilettanti” a kasar Italiya ba. Ni ma dai ban sani ba, a gaskiya, sai da na kalli wannan bidiyon. Ita dai gasar, gasa ce ta cin kofin kulob-kulob masu buga kwallo a rukuni na 6 da na […]

Manchester United Ta Yi Tuntube

Posted March 9th, 2012 at 8:42 pm (UTC+0)
2 comments

Kowa ya dauka cewa Manchester United zata doke Athletic Bilbao ta kasar Spain cikin sauki a karawar da suka yi ta gasar cin kofin Lig-Lig na Europa. Musamman da yake a Old Trafford aka buga wasan, inda aka ce kungiyoyi da dama su na fuskantar sanyin jiki idan sun shiga. Kamar sun shiga ramin kura! […]

Ana Farautar Kwadi Sosai A Koriya…A Dalilin Park Ji-sung Na Manchester United

Posted March 7th, 2012 at 5:14 pm (UTC+0)
10 comments

Wai me ya hada dan wasan Manchester United da kashe kwadi da ake yi yanzu sosai a kasar Koriya ta Kudu? Da alama akwai. Tun lokacin da tsohon Kyaftin na Koriya ta Kudu, kuma dan wasan tsakiya na Manchester United, Park Ji-sung, ya rubuta cikin littafin tarihin rayuwarsa a 2006 cewa lokacin da yake yaro, […]

About

Shafin Tamaular Duniya

Dandalin wadanda ke sha’awa, kuma suka san abinda zasu iya fada kan kwallon kafa. Yaro ba ya wargi!!

Categories

Calendar

April 2024
M T W T F S S
« Feb    
1234567
891011121314
15161718192021
22232425262728
2930