Showing Archived Posts

Chelsea Ta Kori Andre Villas-Boas

Posted March 4th, 2012 at 4:23 pm (UTC+0)
2 comments

Ina cire hula ta ma Mohammed Dan Indiya, domin tun ranar da na fara rubutu a wannan dandalin, yayi mini hasashen cewa Chelsea zata kori Andre Villas-Boas. Yau ina tashi ke nan sai na yi ta ganin sakonnin cewa a karshenta dai Roman Abramovich ya kori Villas-Boas, kuma ya maye gurbinsa da mataimakin manaja Roberto […]

Robin van Persie Ya Harbe ‘Yan Liverpool

Posted March 3rd, 2012 at 4:12 pm (UTC+0)
3 comments

‘Yan Liverpool sai dai kuyi hakuri yau kam, amma a gaskiya kyaftin na ‘yan Arsenal, Robin van Persie, ya burge yau, domin ya tsame musu kitse a wuta a karawar da suka yi a gidan ‘yan Liverpool din. Da farko, Laurent Koscielny yayi kuskuren jefa kwallo a ragarsu a bayan da mai tsaron gida na […]

Real Madrid ko FC Barcelona?

Posted March 1st, 2012 at 8:00 pm (UTC+0)
25 comments

Maki 10 cur kungiyar Real Madrid ta ba FC Barcelona a wasannin lig-lig na Primera Division a kasar Spain. Za ka yi zaton cewa ‘yan wasan Barcelona su na cike da haushin Real Madrid, amma a ranar talatar nan an ga Fabregas yana rubutu a jikin rigar dan wasan Real Madrid! Abin kamar almara. Wasu […]

Kaico, Rwanda Ta Gagari ‘Yan Super Eagles

Posted February 29th, 2012 at 5:46 pm (UTC+0)
4 comments

Anya kuwa abinda ya faru game da gasar cin kofin kasashen Afirka ta Cup of Nations da aka kammala kwanakin baya, ba zai sake faruwa ga Najeriya ba a gasa ta gaba a 2013 ba? Duk da cewa an buga wannan wasa ne a Kigali, babban birnin Rwanda, zaton kowa ne cewa Najeriya zata yi […]

Manchester City ko Manchester United?

Posted February 24th, 2012 at 9:22 pm (UTC+0)
5 comments

Maki biyu kadai ya raba tsakanin kungiyoyin kwallon kafa guda biyu dake sama a wasannin Premier League na Ingila, makwabtan juna kuma ‘yan gari guda Manchester City da Manchester United. Ga shi an riga an buga kimanin kashi biyu cikin uku na wasannin. A zane a takarda, sai mutum ya ga kamar Manchester United ba […]

Me Naira Miliyan 62 Zai Yi Maka?

Posted February 22nd, 2012 at 6:31 pm (UTC+0)
10 comments

Zai iya gina maka tankin kifi, idan kai ne Thiery Henry. Idan da ni ne nake da wannan kudi haka, to da abinda zan fara yi shi ne in yi ritaya daga aikin jarida, in fara noma ko in kafa wata masana’anta inda mutane masu yawa za su samu aikin yi. Amma wannan ba shi […]

Zakarun Kulob-Kulob Na Turai

Posted February 21st, 2012 at 4:09 pm (UTC+0)
13 comments

Yau da gobe sai Allah in ji Hausawa. A yau talata, Chelsea da Napoli, sai kuma Real Madrid da CSKA Moscow. Gobe laraba, Inter Milan da Marseille sai kuma Bayern Munich da Basel. Ga abinda na ji wasu kwararru su na fada: Napoli zata ci wasan yau talata da yake a gidanta ake yi, amma […]

Maraba Da Zuwa Dandalin Tamaula

Posted February 20th, 2012 at 4:07 pm (UTC+0)
29 comments

Ba tare da dogon sutrutu ba, kuma ba tare da na cika ku da surkulle ba, ina son in yi muku marhabin zuwa ga wannan sabon dandalin, inda ni da ku za mu rika musanyar miyau kan tamaula. Tamaula kama daga kan kananan kulob-kulob namu a gida Najeriya, har zuwa Premier League na Najeriya zuwa […]

About

Shafin Tamaular Duniya

Dandalin wadanda ke sha’awa, kuma suka san abinda zasu iya fada kan kwallon kafa. Yaro ba ya wargi!!

Categories

Calendar

April 2024
M T W T F S S
« Feb    
1234567
891011121314
15161718192021
22232425262728
2930