Real Madrid Ta Zamo Zakarar Spain A Bana

Posted May 3rd, 2012 at 4:44 am (UTC+0)
Leave a comment

Wani mai goyon bayan kungiyar Real Madrid dauke da kyalle mai cewa "Zakarun 2011-2012" a bayan da kungiyarsa ta zamo zakarar rukunin lig-lig na kasar Spain, La Liga, bayan ta doke Athletic Bilbao a filin wasa na San Mames dake Bilbao, laraba 2 Mayu 2012.
Real Madrid ta zamo zakarar wasannin rukunin lig-lig na kasar Spain, La Liga, a karon farko cikin shekaru 4, ta kawo karshen mulkin babbar abokiyar adawarta FC Barcelona, bayan da ta doke Athletic Bilbao da ci 3-0 laraba.
Gonzalo Higuain da Mesut Ozil da kuma Cristiano Ronaldo sune suka jefa kwallaye ukun da suka ba kwac na Real, Jose Mourinho, damar lashe kambi har guda hudu a kasashe dabam-dabam har guda hudu, abinda babu wani manajan da ya taba yi.
Real Madrid ta samu nasarar ce duk da cewa har yanzu da sauran wasanni biyu kafin a kawo karshen kakar wasannin lig na bana.
Wannan shi ne kambin farko da Mourinho ya lashe a kasar Spain a shekararsa ta biyu a Real Madrid, kuma shi ya kawo karshen mulkin shekaru uku da FC Barcelona take yi da wannan kambi.
A bayan wasan na jiya laraba, ‘yan wasa da masu koyar da su, ciki har da Mourinho, sun tattaru a filin wasa na San Mames su na murna. Mutanen Bilbabo ba su taba ganin baki sun zo daga wani wuri sun yi murnar lashe rukunin lig-lig na Spain a filin wasansu ba.
Kyaftin na Real madrid, Iker Casillas, ya fada bayan da aka hura tashi daga wasa cewa, “Wannan kakar kwallo doguwa ce, amma daga karshe mun samu nasara. Ina fata wannan shi ne karon farko da zamu dauki wannan kofi da ‘yan wasanmu matasa na yanzu….”

Kwach na Real Madrid, Jose Mourinho, da 'yan wasansa su na murna a filin wasa na Athletic Bilbao a bayan da suka zamo zakarun wasannin lig-lig na kasar Spain na bana.

Kwach na Real Madrid, Jose Mourinho, da 'yan wasansa su na murna a filin wasa na Athletic Bilbao a bayan da suka zamo zakarun wasannin lig-lig na kasar Spain na bana.


“Wannan gagarumin kambi en a gare mu, domin babu wanda ya dauka zamu yi wani abu duk tsawon shekara, duk abinda muka samu, sai da muka tashi muka nemo da kanmu, ‘yan wasanmu sun yi kokari ainun, kuma sun cancanci wannan,” in ji Mourinho.
Ya ci gaba da cewa, “na lashe irin wannan kambi a can baya a Portugal, da Italiya da Ingila, amma wannan ya fi duk sauran wahala. Ina jin cewa ko su ‘yan Barca (FC Barcelona) sun san cewa mun cancanci lashe wannan kambi a bana.”

Manchester City, Zakara?

Posted May 1st, 2012 at 5:24 am (UTC+0)
5 comments

Magoya bayan kungiyar Manchester City sanye da kalar kungiyarsu a lokacin karawar da ta yi da abokiyar adawarta Manchester United, litinin 30 Afrilu 2012 a filin wasa na Etihad dake birnin Manchester. City ta lashe wasan da ci 1-0.

Magoya bayan kungiyar Manchester City sanye da kalar kungiyarsu a lokacin karawar da ta yi da abokiyar adawarta Manchester United, litinin 30 Afrilu 2012 a filin wasa na Etihad dake birnin Manchester. City ta lashe wasan da ci 1-0.


Marubucin tamaula Martin Rogers yace ba wai an nada sabon zakaran lig-lig na kasar Ingila ne a karawar da aka yi litinin a tsakanin Manchester City da Manchester United ba, amma duk wanda ya kalli wasan zai ga kamar abinda aka yi ke nan.
dalili shi ne wadannan kungiyoyi biyu sune ke sama a rukunin na Premier League na Ingila.
Nasarar da Manchester City ta samu da ci 1 da babu a kan Manchester United, tamkar wata ni’ima ce babba ga dubban magoya bayanta a wannan birni wadanda suka shafe shekaru aru-aru su na ganin yadda abokan adawarsu a United su na cin karensu babu babbaka. Ga shi kuma idan City zata dage ta lashe sauran wasanninta biyu, ita zata dauki kofin Premier League na bana a Ingila.
Kwallon da Vincent Kompany ya jefa ana dab da tafiya hutun rabin lokaci, shi ya ba City nasara a kan United, amma kuma, amma kuma wannan rana ce da ‘yan wasan City suka mike tsaye suka nunawa duniya cewa su fa ba kanwar lasa ba ce.
An shiga wasan United tana gaba da maki 3 a saboda haka idan da United ce ta lashe wasan, to kusan za a ce ta lashe Premier League ta bana ke nan.
Amma yanzu su na da maki 83 kowaccensu, sai dai Manchester City ce a kan gaba a bambancin rarar kwallayen da ta jefa a raga guda 8. Ma’ana: idan har City zata doke Newcastle da Queens Park Rangers a sauran wasanninta biyu da suka rage, ita ce Zakara a bana.
Irin bukukuwan murnar da ‘yan Manchester City suka yi a filin wasan na Etihad a Manchester babu kama hannun yaro.
Mutane da yawa sun yi imani da cewa bana dai, shekarar ‘yan Manchester City ce a wasannin lig-lig na Premier na kasar Ingila.
Magoya bayan Manchester City

Magoya bayan Manchester City

Chelsea ta Yi Waje Rod Da FC Barcelona A Gasar Zakarun Kulob-Kulob Na Turai

Posted April 25th, 2012 at 3:26 am (UTC+0)
3 comments

Didier Drogba dan kasar Ivory Coast yana murna tare da sauran 'yan kungiyarsu ta Chelsea bayan da suka yi kunnen dokin da ya ba su nasara a kan kungiyar FC Barcelona, talata 24 Afrilu, 2012 a filin wasa na Camp Nou, a Barcelona, kasar Spain.

Didier Drogba dan kasar Ivory Coast yana murna tare da sauran 'yan kungiyarsu ta Chelsea bayan da suka yi kunnen dokin da ya ba su nasara a kan kungiyar FC Barcelona, talata 24 Afrilu, 2012 a filin wasa na Camp Nou, a Barcelona, kasar Spain.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi waje-rod da kungiyar dake rike da kofin zakarun kulob-kulob na Turai, FC Barcelona, daga gasar ta bana, ta kuma samu kaiwa ga wasan karshe bayan da suka tashi da ci 2-2 daren talata a filin wasa na Camp Nou dake Barcelona. Duk da cewa an kori dan wasan Chelsea daga filin, suka rage saura 10 kawai.
Wannan ya sa Chelsea zata wuce da ci 3-2 idan an hada da nasarar da ta samu a karawarsu ta farko.
Da farko, kamar FC Barcelona zata kai labari a bayan da Sergio Busquets ya jefa mata kwallo a minti na 35 da fara wasa, sannan Andres Iniesta ya kara na biyu a minti na 44.
A minti na 37 da fara wasa, an kori dan wasan Chelsea John Terry daga fili saboda ketar da alkalin wasa yace yayi ma dan wasan FC Barcelona mai suna Alexis Sanchez.
Ramires ya ramawa Chelsea kwallo daya ana dab da zuwa hutun rabin lokaci.
An ba dan wasan Barcelona Lionel Messi bugun fenariti, amma sai ya kasa sakawa cikin raga a bayan da Didier Drogba yayi keta ma Cesc Fabregas.
Fernando Torres ya tabbatrwa da ‘yan Chelsea nasara a wannan karawa a lokacin da ya jefa kwallo na biyu a minti na 90 da wasa.
Chelsea, wadda ba ta taba lashe gasar zakarun kulob-kulob na Turai ba, zata jira wadda zata yi nasara a karawar da za a yi larabar nan a tsakanin Real Madrid da Bayern Munich.
Za a yi karawar karshe ranar 19 ga watan Mayu a birnin Munich na kasar Jamus.

Fabrice Muamba Yace Bai Ji Zafin Komai Ba A Lokacin Da Ya Fadi Ya Suma, Zuciyarsa Ta daina Bugawa

Posted April 23rd, 2012 at 2:50 am (UTC+0)
Leave a comment

Dr Andrew Deaner, a hagu, Fabrice Muamba na kungiyar BoltoN a tsakiya, sai kuma Dr. Sam Mohiddin (Dama) wanda ya jagoranci likitocin da suka kula da Muamba a lokacin da yake kwance a asibiti yana jinyar ciwon zuciya. Dr. Deaner dake hagu, shi ne likitan da ya garzaya cikin filin wasa a lokacin da Muamba ya fadi a filin White Heart Lane lokacin da kungiyarsa ke kwallo da Tottenham.

Dr Andrew Deaner, a hagu, Fabrice Muamba na kungiyar BoltoN a tsakiya, sai kuma Dr. Sam Mohiddin (Dama) wanda ya jagoranci likitocin da suka kula da Muamba a lokacin da yake kwance a asibiti yana jinyar ciwon zuciya. Dr. Deaner dake hagu, shi ne likitan da ya garzaya cikin filin wasa a lokacin da Muamba ya fadi a filin White Heart Lane lokacin da kungiyarsa ke kwallo da Tottenham.


Fabrice Muamba ya bayyana cewa bai ji zafin komai ba a lokacin da zuciyarsa ta tsaya ta daina bugawa lokacin da yake wasa ma kungiyarsa ta Bolton Wanderers a watan da ya shige.
An sallami Muamba daga asibiti tun ranar litinin da ta shige, kuma ya fara kokarin murmurewa a bayan da zuciyarsa ta daina bugawa har na tsawon minti 78 lokacin da suke gwabzawa da kungiyar Tottenham.
Muamba ya fadawa jaridar “The Sun on Sunday” cewa, “ban ji zafin komai ba, ban kama kirji na ba, haka kuma ban ji kirjin nawa ya daure kamar yadda muka saba gani a cikin fim idan mutum ya samu ciwon tsayuwar zuciya ba. Na ji jiri, amma ba irin jirin da ak saba ji ba, sai na ji kamar ina gudu a cikin jikin wani mutum dabam. Daga nan sai na fara ganin abubuwa su na zamowa bibbiyu, kamar dai a mafarki. Na hangi ‘yan wasan (Tottenham) Spurs su na gudu a can nesa, sai na ga Scott Parker ya zamo mutum biyu, haka ma Luka Modrics.”
“Abu na karshe da na ji, shi ne mai tsaron bayanmu Dedryck Boyata yana ta yi mini ihun cewa in yi sauri in koma baya in taimakawa masu tsaron baya. Bai san abinda ke faruwa da ni a lokacin ba, kamar yadda ni ma ban sani ba. Haka kawai sai na ji ina yin kasa zan fadi, sai na ji kara har sau biyu a lokacin da kai na ya fadi ya bugi kasa, daga nan sai duhu kawai, ban sake jin komai ba…”
Muamba ya shafe fiye da makonni 4 a asibiti, amma har aka sallame shi ba a san abinda ya sa zuciyarsa ta daina bugawa ba.
A yanzu an sallame shi a bayan da akab sanya masa wata karamar na’urar da zata maido da bugawar zuciyarsa idan har ta sake tsayawa nan gaba.
“Ido na biyu a lokacin da aka dasa mini wannan na’ura,” in ji Muamba mai shekaru 24 da haihuwa. Na’urar ba zata bukaci sauyin batur ba sai bayan shekaru 10.
“Abin da ya faru gare ni, wata mu’ujiza ce. Koda na rayu, ana tsammanin kwakwalwa ta zata samu illa. Ina fata zan samu sukunin sake buga kwallo a nan gaba. Amma abinda ya fi duka wadannan shi ne na rayu, kuma in ci gaba da nuna kauna da soyayya ga iyali na. babu shakka, na yi babbar sa’a.” In ji Fabrice Muamba

Sabon Salo, Sabon Yayi

Posted April 2nd, 2012 at 5:51 am (UTC+0)
15 comments

Cristiano Ronaldo na Real Madrid yana nuna cinyarsa a bayan da ya jefa kwallo a ragar 'yan wasan kungiyar Osasuna ranar asabar 31 Maris, 2012, abinda ya sa har sauran 'yan wasan Real Madrid suka rika kwaikwayon wannan sabon salo ko yayi nasa.

Cristiano Ronaldo na Real Madrid yana nuna cinyarsa a bayan da ya jefa kwallo a ragar 'yan wasan kungiyar Osasuna ranar asabar 31 Maris, 2012, abinda ya sa har sauran 'yan wasan Real Madrid suka rika kwaikwayon wannan sabon salo ko yayi nasa.


A ranar asabar 31 Maris 2012 ne kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta yi kaca-kaca da kungiyar Osasuna da ci 5 da 1, a karawarsu ta wasannin lig-lig na Spain. Cristiano Ronaldo dan kasar Portugal shi ya jefa kwallaye biyu daga cikin guda biyar din.
Kwallon farko, irin kwallon nan ne da ake kira “Makami mai cin dogon zango” domin tun daga nesa ya sako ta har cikin raga.
Amma babban abinda ya fi burge jama’a ‘yan kallo da sauran ‘yan wasa shi ne a lokacin da shi Ronaldo yake murnar jefa wannan kwallo, sai ya ja wandonsa sama, yana nuna ma jama’a cinyarsa, watau kamar yana fadin cewa irin karfin dake jikin cinyar tasa ta shige misali.
Wannan abu ya burge sauran ‘yan wasan Real Madrid, domin kamar yadda za a gani cikin bidiyo dake kasa, a bencinsu ma sai sauran ‘yan wasan suka fara kwaikwayon wannan abu da Ronaldo yayi, su na nuna cinyarsu domin fadawa duniya cewa su fa ba kanwar lasa ba ne.

ban Kwana Da Birgit Prinz

Posted March 27th, 2012 at 7:46 pm (UTC+0)
Leave a comment

Birgit Prinz ta Jamus tana ban kwana da 'yan kallo a bayan wasanta na karshe na ban kwana yau talata, 27 maris 2012 a tsakanin kulob dinta FFC Frankfurt da kungiyar kwallon kafar mata ta kasar Jamus. Sau uku Birgit Prinz tana zamowa zakarar kwallon kafar mata ta duniya.

Birgit Prinz ta Jamus tana ban kwana da 'yan kallo a bayan wasanta na karshe na ban kwana yau talata, 27 maris 2012 a tsakanin kulob dinta FFC Frankfurt da kungiyar kwallon kafar mata ta kasar Jamus. Sau uku Birgit Prinz tana zamowa zakarar kwallon kafar mata ta duniya.


A yau talata, 27 Maris 2012 masu sha’awar tamaular mata a duniya suka yi ban kwana da daya daga cikin mashahuran masu buga kwallon mata, Birgit Prinz ta Jamus, wadda sau uku tana zamowa zakarar kwallon kafar duniya ta FIFA.
Prinz, mai shekaru 34 da haihuwa, ta lashe kofin duniya na mata har sau biyu a kungiyar kwallon kafar mata ta Jamus.
Dubban jama’a, cikinsu har da shugaban hukumar kwallon kafa ta Jamus, suka cika filin wasa na Frankfurt a yau talata, a lokacin da Prinz ta yi wasanta na karshe. Gaba daya filin ya mike tsaye ana tafa mata, lokacin da ta bar wasa ana kusa da tashi.
Prinz ta samu zuwa gasar cin kofin duniya har sau biyar, inda ta jefa kwallaye har 14. Marta ta kasar Brazil ce kadai macen da ita ma ta jefa kwallaye 14 a raga lokacin gasar cin kofin duniya.
A wasanni har 214 da Prinz ta buga ma kasar Jamus, ta saka kwallaye 128 a raga.
Har ila yau, ta taimakawa kasar Jamus wajen lashe kofin zakarun Mata na Turai sau biyar, tare da lambobin Tagulla 3 a wasannin Olympics.
Birgit Prinz rike da furannin da aka ba ta jim kadan kafin wasanta na karshe yau talata, 27 Maris 2012 a Frankfurt

Birgit Prinz rike da furannin da aka ba ta jim kadan kafin wasanta na karshe yau talata, 27 Maris 2012 a Frankfurt

Dukkan ‘Yan Kwallo A Turai Sun Karrama Fabrice Muamba

Posted March 24th, 2012 at 6:15 pm (UTC+0)
2 comments

Fabrice Muamba na Bolton Wanderers, wanda ke kwance a asibiti bayan harbin zuciya. 'Yan wasan kwallon kafa a duk fadin Turai su na karrama shi tare da yi masa addu'ar samun sauki

Fabrice Muamba na Bolton Wanderers, wanda ke kwance a asibiti bayan harbin zuciya. 'Yan wasan kwallon kafa a duk fadin Turai su na karrama shi tare da yi masa addu'ar samun sauki


Ba kasafai ake samun abu guda dake hada kan ‘yan wasan Tamaula na Turai baki daya ba, im ban da irin wannan tsautsayi da ya abka kan Fabrice Muamba na kungiyar Bolton Wanderers, mai wasa a Premier League na Ingila.
Mahaifin Muamba da wasu ‘yan’uwansa sun bayar da sanarwa su na godewa ‘yan kallo, da ‘yan wasan Tamaula da ma’aikatan asibiti a saboda tallafi da goyon bayan da suka nuna musu. Muamba ya fadi kasa haka kwatsam kafin a tafi hutun rabin lokaci a yayin da Bolton ta ke buga wasan kwata fainal na kofin kalubalenka da Tottenham ranar asabar da ta shige.
Har yanzu tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafar Ingila ta ‘yan kasa da shekara 21 yana cikin matsanancin hali a Asibitin Kirji na London. An ce sai da ma’aikatan jinya suka shafe mintoci 78 su na aiki a kansa da injin sake tayar da zuciya kafin zuciyar tasa ta sake bugawa da kanta. An ce yayi magana da likitoci ranar litinin.
Mahaifinsa, Marcel Muamba, yace Muamba yana murmurewa duk ad cewa har yanzu yana cikin matsanancin hali, kuma ya roki jama’a da su ci gaba da yi masa addu’a.
A duk fadin nahiyar Turai, ‘yan wasan Tamaula sun sanya rigunan nuna jimami ga Muamba wadanda a jiki aka rubuta “Allah Kawo Sauki Fabrice” ko kuma “Get Well Soon fabrice” a turance.
'Yan Kungiyar Tottenham Hotspur sanye da rigunan addu'ar samun sauki ga Fabrice Muamba kafin karawarsu ta ranar Laraba 21 Maris 2012.

'Yan Kungiyar Tottenham Hotspur sanye da rigunan addu'ar samun sauki ga Fabrice Muamba kafin karawarsu ta ranar Laraba 21 Maris 2012.


Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tana cikin wadanda suka ware lokaci musamman domin jimamin wannan abu da ya samu Muamba. Shi ma shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, Sepp Blatter, yayi magana da shugaban kungiyar Bolton, ya kuma nemi da a rika sanar da shi halin da Muamba yake ciki.
Kungiyar Bolton ta ce irin sakonnin fatar alherin da ta rika samu, ta ke kuma kan samu daga magoya bayan kungiyoyi dabam-dabam a fadin duniya, abin ya shige misali.

Idan Kai Ne Yaya Zaka Yi? Fadi Gaskiya!

Posted March 17th, 2012 at 5:38 pm (UTC+0)
8 comments


Na san watakila mafi yawan masu karanta wannan ba su san wata gasar da ake kira “Coppa Italia Dilettanti” a kasar Italiya ba. Ni ma dai ban sani ba, a gaskiya, sai da na kalli wannan bidiyon.
Ita dai gasar, gasa ce ta cin kofin kulob-kulob masu buga kwallo a rukuni na 6 da na 7 a kasar Italiya, watau rukunonin Amatuwa.
A cikin wannan bidiyo ana karawa ne a tsakanin kungiyar Torres da Termoli. Ana dab da tashi daga wasan, sai alkalin wasa ya ba ‘yaa Termoli bugun fenariti a lokacin da dan wasanta Vittorio Esposito ya fadi a cikin shatin yadi 18. Shi kuma da ya ga cewa ba taba shi aka yi ya fadi ba, sai kunya ta kama shi, da aka ba shi bugun fenariti sai kawai ya je ya buga ta can wani wurin dabam, bai ma yi kokarin jefawa a raga ba.
‘Yan Torres sun yi murnar wannan, amma kuma sun yi bakin cikin cewa duk da haka an cire su a wannan gasar ta bana.
A karawarsu ta farko ma, Termoli ta yi wani abin ban dariya ga ‘yan kallo a lokacin da dan wasanta Fabio Cifani ya lura cewa mai tsaron gida na Torres ya fito, saboda haka tun daga kusa da tsakiyar fili sai ya auna kwallo sama ta je ta shiga ragar ‘yan Torres, kamar yadda yake a bidiyo na kasa.
Wai shin idan kai ne yaya zaka yi da bugun fenaritin nan? A yi mana sharhi a kasa, ko a gefe daga dama.

Manchester United Ta Yi Tuntube

Posted March 9th, 2012 at 8:42 pm (UTC+0)
2 comments

Dan wasan Manchester United, Javier Hernandez, a tsakiya, ya murtuke fuska da bacin rai a bayan da kungiyar Athletic Bilbao ta jefa kwallo na biyu a karawarsu ta lashe kofin Europa League a filin wasan Old Trafford na Manchester a kasar Ingila, alhamis 8 Maris, 2012.

Dan wasan Manchester United, Javier Hernandez, a tsakiya, ya murtuke fuska da bacin rai a bayan da kungiyar Athletic Bilbao ta jefa kwallo na biyu a karawarsu ta lashe kofin Europa League a filin wasan Old Trafford na Manchester a kasar Ingila, alhamis 8 Maris, 2012.


Kowa ya dauka cewa Manchester United zata doke Athletic Bilbao ta kasar Spain cikin sauki a karawar da suka yi ta gasar cin kofin Lig-Lig na Europa.
Musamman da yake a Old Trafford aka buga wasan, inda aka ce kungiyoyi da dama su na fuskantar sanyin jiki idan sun shiga. Kamar sun shiga ramin kura!
‘Yan wasan Athletic Bilbao sun yi kaca-kaca da ‘yan wasan baya masu kare gidan Man U, ba kamar yadda kungiyoyi suke zuwa wannan fili da sanyin jiki ba.
Wayne Rooney dai ya burge ‘yan Man U, domin shi ya jefa musu dukkan kwallayensu biyu. Kuma an ce a kullum kafarsa tana dada sajewa da ta Chicarito Hernandez, wadanda Sir Alex Ferguson ya fara sanyawa tare a gaba.
yanzu wasa zai koma kasar Spain a ranar 15 ga watan nan. Anya Manchester United zata kai labari? Idan ‘yan wasan Athletic Bilbao suka ga dama, zasu rika yin wasan neman a tashi kunnen doki ne kawai.
Anya kuwa Man U zata iya hayewa a wannan kofin na Europa wanda idan suka lashe zasu sa Sir Alex Ferguson ya zamo ya taba lashe dukkan manyan kofunan Turai guda uku?
Ina ra’ayinku kan wanna?

Ana Farautar Kwadi Sosai A Koriya…A Dalilin Park Ji-sung Na Manchester United

Posted March 7th, 2012 at 5:14 pm (UTC+0)
10 comments

Tsohon kyaftin na kasar Koriya ta Kudu, kuma dan wasan tsakiya na Manchester United, Park Ji-Sung

Tsohon kyaftin na kasar Koriya ta Kudu, kuma dan wasan tsakiya na Manchester United, Park Ji-Sung


Wai me ya hada dan wasan Manchester United da kashe kwadi da ake yi yanzu sosai a kasar Koriya ta Kudu?
Da alama akwai.
Tun lokacin da tsohon Kyaftin na Koriya ta Kudu, kuma dan wasan tsakiya na Manchester United, Park Ji-sung, ya rubuta cikin littafin tarihin rayuwarsa a 2006 cewa lokacin da yake yaro, mahaifinsa yana kamo kwadi ya tatse masa ruwansu yana sha domin ya samu kuzari a filin kwallo, yanzu kwadi sun fara karewa a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Yonhap na Koriya, ya ambaci wani jami’in kungiyar kare kwadi mai suna “Frogs Friends”, Park Wan-hee, yana fadin cewa sun lura da cewa daga lokacin da gwarzon dan wasan ya fadi wannan kalami, an fara samun masu farautar kwadi a boye cikin kasar.
Abin har ta kai ma kungiyar “Frogs Friends” ta fito tana kira ga dan kwallon da ya fito yayi tur da shan romon kwadi, ko mutane zasu komo cikin hayacinsu su daina farautarsu.
Dabara dai ta rage ga mai shiga rijiya.

About

Shafin Tamaular Duniya

Dandalin wadanda ke sha’awa, kuma suka san abinda zasu iya fada kan kwallon kafa. Yaro ba ya wargi!!

Categories

Calendar

April 2024
M T W T F S S
« Feb    
1234567
891011121314
15161718192021
22232425262728
2930