Chelsea Ta Kori Andre Villas-Boas
Posted March 4th, 2012 at 4:23 pm (UTC+0)
2 comments
Ina cire hula ta ma Mohammed Dan Indiya, domin tun ranar da na fara rubutu a wannan dandalin, yayi mini hasashen cewa Chelsea zata kori Andre Villas-Boas.
Yau ina tashi ke nan sai na yi ta ganin sakonnin cewa a karshenta dai Roman Abramovich ya kori Villas-Boas, kuma ya maye gurbinsa da mataimakin manaja Roberto Di matteo, tsohon dan wasan ita Chelsea din, wanda zai jagoranci kungiyar har zuwa karshen shekara.
Tun lokacin da Abramovich dan kasar Rasha ya sayi Chelsea a shekarar 2003, kungiyar ta lashe Premier sau 3, ta lashe kofin FA (kalubalenka na Ingila) sau 3, ta kuma lashe lig-lig na Turai sau biyu.
Amma ba ta taba lashe kofin Zakarun Kulob-Kulob na Turai ba, kofin da aka ce shi mai kulob din ya fi kwadayin lashewa a kan komai.
Babban abinda ya kara fusata Ambramovich shi ne cewa yanzu Chelsea ta koma ta 5 a teburin Premier bayanda ta West Bromwich Albion ta doke ta jiya asabar, kuma a karon farko tun 1979.
Wannan shi ne karo na 8 cikin shekaru 9 da kulob din Chelsea zata shiga cikin kasuwar neman manaja.
Kaico, Rwanda Ta Gagari ‘Yan Super Eagles
Posted February 29th, 2012 at 5:46 pm (UTC+0)
Anya kuwa abinda ya faru game da gasar cin kofin kasashen Afirka ta Cup of Nations da aka kammala kwanakin baya, ba zai sake faruwa ga Najeriya ba a gasa ta gaba a 2013 ba?
Duk da cewa an buga wannan wasa ne a Kigali, babban birnin Rwanda, zaton kowa ne cewa Najeriya zata yi kaca-kaca da ‘yan wasan Rwanda wadanda ake kira WASP. Amma abin sam bai yiwu ba.
Wannan kuma shi ne karon farko da Stephen Keshi yake jagorancin kungiyar ta Super Eagles zuwa wata gasa ta zahiri.
Wai shin menene ra’ayinku a game da wannan abin kaico? A rubuta mana ra’ayi a kasa.
Manchester City ko Manchester United?
Posted February 24th, 2012 at 9:22 pm (UTC+0)
Maki biyu kadai ya raba tsakanin kungiyoyin kwallon kafa guda biyu dake sama a wasannin Premier League na Ingila, makwabtan juna kuma ‘yan gari guda Manchester City da Manchester United. Ga shi an riga an buga kimanin kashi biyu cikin uku na wasannin.
A zane a takarda, sai mutum ya ga kamar Manchester United ba zata iya share maki biyu da ‘yan City suka ba ta rata da su ba. Misali, idan aka dubi wasanni shida dake tafe na kungiyoyin biyu, United zata kara da kungiyoyi biyu dake cikin guda 10 na saman wannan rukunin Premier, watau Norwich City da Tottenham, yayin da City zata kara da guda ce kawai watau Chelsea. Amma ba ta nan take ba.
An san Man U da bayarda mamaki a wasu lokutan. Kuma ga shi City tana fama da matsalar Carlos Tevez, koda yake Roberto Mancini ya furta cewa shi ba ya da matsala da dan wasan gaban, kuma zai iya komowa cikin mako biyu ko uku.
Af, ga shi kuma dukkansu biyu zasu sake haduwa a gasar cin kofin kasashen Turai ta Europa League, wasan da manyan kungiyoyi irinsu a can baya suke rainawa.
Hausawa suka ce ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.
A wanne kuke: Manchester City ko Manchester United?
Me Naira Miliyan 62 Zai Yi Maka?
Posted February 22nd, 2012 at 6:31 pm (UTC+0)
Zai iya gina maka tankin kifi, idan kai ne Thiery Henry.
Idan da ni ne nake da wannan kudi haka, to da abinda zan fara yi shi ne in yi ritaya daga aikin jarida, in fara noma ko in kafa wata masana’anta inda mutane masu yawa za su samu aikin yi.
Amma wannan ba shi ne tunanin shahararren dan kwallon nan na Faransa, Thiery Henry ba, domin ya ware wannan kudi ne za a gina masa tankin ajiye kifi na kallo a cikin gidansa.
Jaridar “The Daily Mail” ce ta ke cewa Henry zai gina sabon gida, mai hawa 4, kuma daya daga cikin sabbin abubuwan da za a yi masa, shi ne wani tankin gilashi na ajiye kifi, mai tsawon kafa arba’in daga kasa zuwa sama, kuma mai fadin kafa 15.
Watau tankin kifin zai taso tun daga hawan farko har zuwa hawa na hudu a wannan gida.
Kudinsa, Dala dubu 400, ko Naira Miliyan 62!! Cafdi
A bayan Naira Miliyan 62 na gina wannan tanki, Henry zai rika kashe sama da Naira miliyan 3 a kowace shekara wajen kula da wannan tankin kifi da kuma kifaye guda 300 da tankin zai iya dauka. Hmmm
Kudi na gwamna masu gida rana.
Idan da kai ne, me za ka yi da wannan kudi Naira miliyan 62?
Zakarun Kulob-Kulob Na Turai
Posted February 21st, 2012 at 4:09 pm (UTC+0)
A yau talata, Chelsea da Napoli, sai kuma Real Madrid da CSKA Moscow.
Gobe laraba, Inter Milan da Marseille sai kuma Bayern Munich da Basel.
Ga abinda na ji wasu kwararru su na fada:
Napoli zata ci wasan yau talata da yake a gidanta ake yi, amma Chelsea zata ci zagaye na biyu kuma ita zata haye zuwa gaba.
Real Madrid zata lashe wasanta na yau duk da cewa a Moscow ake wasan a gidan ‘yan CSKA, kuma zata wuce zuwa gaba.
Inter Milan zata kashi gobe laraba a hannun ‘yan Marseille, kuma ba zata kai labari ba, ‘yan Marseille su zasu zarce.
Bayern Munich zata doke Basel na Switzerland a yau da kuma zagaye na gaba, ta wuce zuwa ga wasanni na gaba.
Ni dai a taya ni duba hanya, wai makaho na son yin tsegumi. Na dai san tun da aka fara gasar zakarun kolb-kulob na Turai na bana, kwallaye biyu kawai aka jefa a ragar ‘yan Real Madrid a lokacin da ake rukuni-rukuni.
Babu wanda aka fi neman kassarawa a fili lokacin wasannin kamar Franck Ribery na Bayern Munich wanda aka yi ma (foul) har sau 23.
Daga cikin kungiyoyi 16 da suka rage, Chelsea ce kawai ba ta aikata laifi da yawa ba a zagayen rukuni-rukuni na gasar, inda aka hura mata wusur na laifi (foul) sau 61 kawai.
Ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare. Akwai wanda zai yi mini karin haske kan wannan gasar?