Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta Ingila ta sake cin moriyar lashe kofin zakarun kolob-kulob na Turaoi da ta yi kwanakin baya. A wannan karon, Gamayyar Kungiyoyin Kwallon Kafar Kasashen Turai, ta zabi Chelsea a zaman Kulob Din Turai Ta Wannan Shekara. Roberto Di Matteo ya jagoranci ‘yan wasan nasa zuwa ga nasara kan Bayern […]
Chelsea Ta Zamo Kulob Din Turai Ta Wannan Shekara
Wariyar Launin Fata – Ingila Ta Ce Zata Janye Daga Wasa Idan Aka Ci Mutuncin ‘Yan Wasanta Bakaken Fata
Kyaftin na kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila, Steven Gerrard, yace lallai idan har ‘yan kallo ko ‘yan wasan kasa suka kuskura suka nemi cin mutuncin ‘yan wasansu bakar fata, to ko ana tsakiyar wasa ne zai sa ‘yan kungiyar su fita su bar fili a wajen gasar cin kofin kasashen Turai, EURO 2012. Kasashen […]
Laifin Bayern Munich Ne – Ba Gwanintar Chelsea Ba
Dan tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa zai buga. Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta kasar Jamus ita ta jefa kanta cikin ukubar bakin ciki da radadin zuciya, bayan da ta watsar da babbar damar da ta samu ta yin abin tarihi a gasar cin kofin zakarun Turai, kuma a cikin filin wasanta, […]
Manchester City Ta Tsamo Kitse A Wuta
Magoya bayan kungiyar Manchester City sun fara kuka, duniya ta rikice musu ana dab da tashi daga wasan da suka yi da Queens Park Rangers a filin wasa na Etihad dake birnin Manchester. A can Sunderland kuwa, magoya bayan Manchester United sai murna suke yi, ‘yan wasansu kuma har sun fara layi su na jiran […]
Allah Ya Jikan Rashid Yekini, Mun Yi Rashi
Duk wani masoyin Najeriya da kwallon kafa a Najeriya da Afirka, ba zai taba mantawa da Rashid Yekini ba. Rashid Yekini, ya rasu ranar jumma’a a Ibadan, yana da shekaru 48 da haihuwa. Babu wani dan kwallon da ya taba jefa ma Najeriya kwallaye kamarsa, inda a cikin wasanni 58 da ya buga ma kungiyar […]
Sabon Salo, Sabon Yayi
A ranar asabar 31 Maris 2012 ne kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta yi kaca-kaca da kungiyar Osasuna da ci 5 da 1, a karawarsu ta wasannin lig-lig na Spain. Cristiano Ronaldo dan kasar Portugal shi ya jefa kwallaye biyu daga cikin guda biyar din. Kwallon farko, irin kwallon nan ne da ake kira […]
Ana Farautar Kwadi Sosai A Koriya…A Dalilin Park Ji-sung Na Manchester United
Wai me ya hada dan wasan Manchester United da kashe kwadi da ake yi yanzu sosai a kasar Koriya ta Kudu? Da alama akwai. Tun lokacin da tsohon Kyaftin na Koriya ta Kudu, kuma dan wasan tsakiya na Manchester United, Park Ji-sung, ya rubuta cikin littafin tarihin rayuwarsa a 2006 cewa lokacin da yake yaro, […]
Kaico, Rwanda Ta Gagari ‘Yan Super Eagles
Anya kuwa abinda ya faru game da gasar cin kofin kasashen Afirka ta Cup of Nations da aka kammala kwanakin baya, ba zai sake faruwa ga Najeriya ba a gasa ta gaba a 2013 ba? Duk da cewa an buga wannan wasa ne a Kigali, babban birnin Rwanda, zaton kowa ne cewa Najeriya zata yi […]
Me Naira Miliyan 62 Zai Yi Maka?
Zai iya gina maka tankin kifi, idan kai ne Thiery Henry. Idan da ni ne nake da wannan kudi haka, to da abinda zan fara yi shi ne in yi ritaya daga aikin jarida, in fara noma ko in kafa wata masana’anta inda mutane masu yawa za su samu aikin yi. Amma wannan ba shi […]
Zakarun Kulob-Kulob Na Turai
Yau da gobe sai Allah in ji Hausawa. A yau talata, Chelsea da Napoli, sai kuma Real Madrid da CSKA Moscow. Gobe laraba, Inter Milan da Marseille sai kuma Bayern Munich da Basel. Ga abinda na ji wasu kwararru su na fada: Napoli zata ci wasan yau talata da yake a gidanta ake yi, amma […]