A bayan da ta shafe shekaru har 19 tana fafutukar neman kofin zakarun kasashen Afirka, hakar Najeriya ta cimma ruwa a bayan da ta doke Burkina Faso da ci daya da babu a wasan karshe na gasar a kasar Afirka ta Kudu. Sunday Mba, shi ne ya jefa ma Najeriya kwallonta a minti na 40 […]