Showing Archived Posts

Najeriya Ta Doke Burkina Faso

Posted February 11th, 2013 at 5:38 am (UTC+0)
Leave a comment

A bayan da ta shafe shekaru har 19 tana fafutukar neman kofin zakarun kasashen Afirka, hakar Najeriya ta cimma ruwa a bayan da ta doke Burkina Faso da ci daya da babu a wasan karshe na gasar a kasar Afirka ta Kudu. Sunday Mba, shi ne ya jefa ma Najeriya kwallonta a minti na 40 […]

Allah Ya Jikan Rashid Yekini, Mun Yi Rashi

Posted May 7th, 2012 at 4:22 am (UTC+0)
20 comments

Duk wani masoyin Najeriya da kwallon kafa a Najeriya da Afirka, ba zai taba mantawa da Rashid Yekini ba. Rashid Yekini, ya rasu ranar jumma’a a Ibadan, yana da shekaru 48 da haihuwa. Babu wani dan kwallon da ya taba jefa ma Najeriya kwallaye kamarsa, inda a cikin wasanni 58 da ya buga ma kungiyar […]

Kaico, Rwanda Ta Gagari ‘Yan Super Eagles

Posted February 29th, 2012 at 5:46 pm (UTC+0)
4 comments

Anya kuwa abinda ya faru game da gasar cin kofin kasashen Afirka ta Cup of Nations da aka kammala kwanakin baya, ba zai sake faruwa ga Najeriya ba a gasa ta gaba a 2013 ba? Duk da cewa an buga wannan wasa ne a Kigali, babban birnin Rwanda, zaton kowa ne cewa Najeriya zata yi […]

Maraba Da Zuwa Dandalin Tamaula

Posted February 20th, 2012 at 4:07 pm (UTC+0)
29 comments

Ba tare da dogon sutrutu ba, kuma ba tare da na cika ku da surkulle ba, ina son in yi muku marhabin zuwa ga wannan sabon dandalin, inda ni da ku za mu rika musanyar miyau kan tamaula. Tamaula kama daga kan kananan kulob-kulob namu a gida Najeriya, har zuwa Premier League na Najeriya zuwa […]

About

Shafin Tamaular Duniya

Dandalin wadanda ke sha’awa, kuma suka san abinda zasu iya fada kan kwallon kafa. Yaro ba ya wargi!!

Categories

Calendar

September 2024
M T W T F S S
« Feb    
 1
2345678
9101112131415
16171819202122
23242526272829
30