Maraba Da Zuwa Dandalin Tamaula

Posted February 20th, 2012 at 4:07 pm (UTC+0)
29 comments

Didier drogba ke kokarin shan kwallo

Ba tare da dogon sutrutu ba, kuma ba tare da na cika ku da surkulle ba, ina son in yi muku marhabin zuwa ga wannan sabon dandalin, inda ni da ku za mu rika musanyar miyau kan tamaula.
Tamaula kama daga kan kananan kulob-kulob namu a gida Najeriya, har zuwa Premier League na Najeriya zuwa ga kungiyar kwallon kafa ta kasa da na kasashen Afirka.
Kai har da kulob-kulob na Turai, don kwanakin baya na ga wani aboki na yana zumudi sosai kan wata kungiyar da yake goyon baya a Ingila (ba zan fadi sunanta domin kada in fusata ‘yan saho nata dake karanta wannan).
Idan akwai wani labari da dumi-duminsa na kwallon kafa, daga ko ina ne a duniya, za ku iya shigowa cikin zauren nan, ku sheke ayarku (idan dai ba kungiya ta ce ta sha kashi ba).
Amma ban da zare idanu. Ban da kuma ashar, Mu tattauna cikin tsanaki, wanda bai ji dadin sakamakon kwallon ranar ba, to sai yayi ma kansa kiyamullaili, ya sha Panadol Night ya je yayi barci, watakila kafin gari ya waye zai mance, ya komo mu ci gaba da muhawara.
Maraba, daga Ibrahim Alfa Ahmed.

29 responses to “Maraba Da Zuwa Dandalin Tamaula”

 1. Mohammed 'Dan India says:

  A yayin da kungiyar Arsenal ta tabbatar wa kocin ta Arsene Wenger cewar mukamin sa na nan daram-dam daga nan har zuwa akalla shekaru 2 masu zuwa,shi kuwa kocin Chelsea zai buga wasan sa na gobe ne da Napoli a cike da fargaba.Ganin cewar tun bayan da ya karbi jagorancin kungiyar sai dada komawa baya ta ke yi har ma ta kai ga yanzu mastayi na 4 a tebirin Premier na neman kubuce mata abin da a ka dade ba’a gani ba a kungiyar.Kuma sanin kowa ne cewar Mai gidan sa Abramovic ba ya bari ta kwana,muddin dai bai gani a kasa ba to dole ne gatarin sa ta sari koci…….

  • Ibrahim Alfa Ahmed says:

   Kai, kai kai, ni kuma ji nayi cewa Roman Abramovich mai kungiyar ta Chelsea ya tabbatarwa shi Andre Villas-Boas cewa yana bayansa, koda yake an ce akwai ‘yan wasan da suka kalubalanci manajan nasu a wajen wani mitin. Mu jira mu ga wasan da zasu yi na Firimiya da Bolton ranar 25, watau asabar mai zuwa.

   • Mohammed 'Dan India says:

    Kafin nan sai ka lalli na gobe tukuna tsakani Chelsea da Napoli.Domin ka san cewar shi Abramovic ba abin da ya fi so ya ga kungiyar ta ciyo illa Champions legue kuma idan ka na iya tunawa kan gaba na sanadiyyar korar Mourinho kenan domin ya ci kofina a barkatai a Ingila amma Champions ta gagare shi.Maganar AVB kuma lalle akwai tension tsakanin sa da ‘Yan wasa kuma an yi ta jita-jitan cewar ba ya samun goyon bayan su dari bisa dari inda ya mai da martanin cewar muddin idan ya na da goyon bayan Abramovic to hankalin sa kwance…..

    • Ibrahim Alfa Ahmed says:

     Zamu ga yadda za ta kaya!!! Ba ka jin cewa sayen Fernando Torres da Chelsea ta yi, kudinta bai biya? Ga Drogba ya fara gajiya.

     • Mohammed 'Dan India says:

      Har ‘i zuwa yanzu ba ma ni kadai ba kowa ma ya yi mamakin irin makudan kudaden da a ka zuba wajen sayen Fernado Torres daga Liverpool kuma sai ga shi kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.Daga farko an yi ta hasashen cewar ‘Dan wasan zai farfado ya fara cin kwallaye idan ya murmure ya saje da kungiyar,amma kuma sai a ka ga akasin hakan.Wasu har sun fara hasashen za’a sayar da ‘Dan wasan sai kuma ga AVB ya shigo inda ya ci gaba da cewar ya na goyon bayan cewar ‘Dan wasan na bukatar lokaci kadan ya fara taka rawar gani amma kuma har yanzu shiru ka ke ji.’Yan wasa irin su Drogba kuma kamar yadda ka ce ya fara gajiya daidai lokacin da kungiyar ke neman yin offloading din sa,ko da ya ke na ji a na zancen cewar shi Drogba na son ya kara akalla shekara 1 a kungiyar………..

     • Ibrahim Alfa Ahmed says:

      Watau ka san sai na tuna yadda kungiyarmu ta Washington Redskins (kwallon zari-ruga suke yi, amma wai su na ce FOOTBALL!!!) ta rika barin kudi tana sayen ‘yan wasa mafi tsada, amma a banza. Aka wayi gari kowane dan wasa idan alkadarinsa ya karye, sai ya nemi zuwa Washington don kawai ya cika aljihu. Kullum kungiyar Washington Redskins ita ce kashin baya. Samun dan wasa mai kyau kamar Fernando Torres na da kyau, amma ka samu dan wasan da zai dace da sauran ‘yan wasa ina jin ya fi muhimmanci.

 2. Mohammed 'Dan India says:

  Ganin matsayin kungiyar kwallon kafar Real Madrid yanzu haka a kan tebirin la liga ta kasar Spania inda har ta baiwa abokiyar hamayyar ta Fc barcelona maki daya-daya har goma,to babu shakka ko an ki ko an so mutane za su yi ta tunanin cewar wannan karon Madrid ce za ta zama zakara.Na’aam ni ma ina cikin masu tunanin hakan ganin yadda Mardrid ta taso a wannan kakar tun daga fara gasar har zuwa yanzu da karfin ta ta ke buga wasa,amma kuma ba nan gizo ke saka ba domin kuwa akwai akalla wasanni kusan 13 ko 14 da su ka rage kafin karkare gasar.Daga karshe ba ni da tsammanin Real Madrid za ta sha kashi har sau 3 ko 4 kafin karshen gasar,haka zalika ba ni da tsammanin barcelona za ta lashe wasannin ta gaba daya ba tare da ta sha kashi ko ta buga kunnen doki ba ganin cewar a wannan kakar wasa ta sha kashi akalla sau 2 ta kuma buga kunnen doki har kusan sau 3…..

  • Ibrahim Alfa Ahmed says:

   Hmmmm, Dan Indiya ka kalli kwallon FC Barcelona da Valencia kuwa? Ka ga yadda Lionel Messi ya zuba kwallaye 4 shi kadai? Kuma ka san valencia fa ba kanwar lasa ba ce, domin ita ce ta 3!! To, za dai mu ga abinda zai faru

   • Mohammed 'Dan India says:

    Kwarai kuwa na kalli wasan daga farko har karshe,hasali ma har an gayyace ni kallon wani film na Nikolas cage”Ghost Rider 2″amma daga baya sai na fahimci cewar akwai wannan babban wasa sai na baiwa wani tikitin.Kuma idan ka lura da shafin ku na facebook da ka ga inda na yi posting da safe na ce FOURTRICK sai Sarki mai abin..wato ina nufin messi kenan…..

 3. Mohammed 'Dan India says:

  Shan kashin da Arsenal ta yi da kwallaye 4 ba ko 1 a hannun Ac Milan a gasar cin kofin zakarun Turai a makon da ta shige,shin a na iya cewa kalame da gargadin da Clarence Seedrof ya yi ne kafin su tunkari Arsenal na cewar sun shirya tsaf domin kawo karshen kungiyoyin Premier a gasar cin kofin zakarun Turai ne ya yi tasisiri,ko kuwa dai tsoro da shan jinin jikin sa da kocin Arsenal ya yi tun kafin fara wasa inda ya yi ta korafe-korafe kan filin wasa ne ya jawo musu wannan gagarimin koma baya da a ka jima ba’a ga irin sa ba a kungiyar ta Gunners?????ko kuma a kwai wani abin na daman da ya jawo wa Arsenal faduwa a hannun Milan da kuma shan kashin da ta yi a hannun Sunderland a gasar Fa abin da ke nuna cewar a wannan shekara mai yuwa Arsenal ta tashi a tutar babu inda ko kofin shayi ba za ta ci ba,haka kuma matsayi na 4 ma sai ta yi da gaske kafin ta samu……..

 4. Tamola yanzu babu gwani… Yaro yana doke babba hankali kwance!

  • Ibrahim Alfa Ahmed says:

   Hafizu ka yi bayani domin mu karu!

   • Mohammed 'Dan India says:

    Ato Ibrahim sake fada masa dai….mai yuwa ji ya ke kowa ya zama kofi mam’nua ne,yayin da su Barcelona ke lashe illahirin kofin da ka sani na gida da waje,sannan a ce tamaula babu gwani???

 5. haruna irani m/fashi says:

  hahaha arsenal bana ba kofi sai ayi hakuri sabi da kunsan kofin na manyane mai kare kama karanka damisa ta danno up man united duniya

 6. kai!yan arsenal dai ba labari bana

 7. saifullahi sani wada says:

  yau fa akeyinta yen premire sunkama hanyar zuwa gida baki dayan su,akarshe kowa yagama tankade da rairaya abarwa barcelona

 8. saifullahi sani wada says:

  tabbas tamola tacaja abin dabam mamaki wai napoli ta lallasa chelsea ayau

 9. har yanzu barcelona nada damar lashe gasar bana, ayidai mugani ga fili ga mai doki

 10. Watau kimanin sama da shekaru da dama ba a taba fidda ingilan club ba, a gasar zakarun turai, tun karan farko sai awannan shekarar wani kalubale ne da magoya bayan manyan club din ingila suka fuskanta… Uwa uba masu dogon zango basu samu damar daukar ko….

 11. haruna irani m/fashi says:

  kura uwar kare manchesta karen koda na spain ne ku makiya sai kuyi hakuri duniya tasan ba.a himu iyawaba

 12. haruna irani m/fashi says:

  mukam yan man.united musan koda aka fiddamu daga champion fifa tafimu jin haushi sabida tafimu asara

 13. haruna irani m/fashi says:

  mukam yan man.united musan koda aka fiddamu daga champion fifa tafimu jin haushi sabida tafimu asara sabida wasannin bazasuyi armashiba

 14. Mohammed 'Dan India says:

  Super eagles ta kasa kai labari a wasan share fagen zuwa gasar cin kofin Afirka a shakar 2013 a Afirka ta kudu inda ta tashi canjaras tsakanin ta da kasar Rwanda.Wato dai da alama har yanzu ba ta sake zani ba bayan alkawarin da sabon Koci Stephen keshi ya yi wa Najeriya na samar da sabuwar kungiyar Super Eagles sabuwa fil a yayin da ya sake kwaso mana kwashi kwaraf tsoffin ‘yan wasan da su ka kasa tabuka komai a baya irin su odemwingie,Yobo,Taiwo,Yakubu da sauran su…….Super Eagles dai tashin ta kuma sai dai wani ikon Allah……..

 15. haruna irani m/fashi says:

  agaskiya hukumar kwallon kafa ta najeriya mungaji datara muna bakin cikin da kukeyi dolene anemo couch farar fata in anaso acigaba sabida neman kudi saida kudi siyasiya yakasa keshi mezai iyayi wayau baya saida taba gari

  • Ibrahim Alfa Ahmed says:

   Malam Haruna, kana jin cewa samun coach farar fata shi ne zai warware matsalar Najeriya a fagen kwallo? Najeriya ta yi masu koyar da wasa turawa masu dan karen yawa, amma im ban da irinsu Otto Gloria da Clemens Westerhoff, sauran duk shirirta ne, a gani na, kuma a ra’ayi na. Ka manta da Jo Bonfrere ne, ko Berti Vogts ko Lars Lagerback, ko Bora Milutinovic da sauransu?

 16. Hum matsalar Najeriya a rushe duk ma’aikatan hukumar kwallan kafar kasar kawai… Inba haka haryau gidan jiya za a koma

 17. Bala dahiru hassan says:

  Ina labarin kungiyan kwallon kafa na voa hausa flamingo f.c Bauchi ne?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

About

Shafin Tamaular Duniya

Dandalin wadanda ke sha’awa, kuma suka san abinda zasu iya fada kan kwallon kafa. Yaro ba ya wargi!!

Categories

Calendar

February 2012
M T W T F S S
    Mar »
 12345
6789101112
13141516171819
20212223242526
272829