Najeriya Ta Doke Burkina Faso

Posted February 11th, 2013 at 5:38 am (UTC+0)
Leave a comment

‘Yan wasan Najeriya rike da kofin zakarun Afirka da suka lashe bayan da suka doke Burkina Faso da ci daya da babu, ranar lahadi, 10 Fabrairu a Afirka ta Kudu.


A bayan da ta shafe shekaru har 19 tana fafutukar neman kofin zakarun kasashen Afirka, hakar Najeriya ta cimma ruwa a bayan da ta doke Burkina Faso da ci daya da babu a wasan karshe na gasar a kasar Afirka ta Kudu.
Sunday Mba, shi ne ya jefa ma Najeriya kwallonta a minti na 40 da fara wasan nan.
Rabon da Najeriya ta lashe wannan kofi tun 1994.
A lokacin da aka hura tashi daga wannan wasa, dubban ‘yan Najeriya, kama daga Lagos har zuwa Abuja, Enugu, Kaduna da Calabar, sun kwarara kan tituna su na murnar wannan nasara.
A Lagos, jama’a bdake murna sun yi ta harba irin kayan wasan wutar nan da ake kira Knockout.

Magoya bayan Najeriya su na murnar doke Burkina Faso da ta yi

Chelsea Ta Zamo Kulob Din Turai Ta Wannan Shekara

Posted September 11th, 2012 at 6:27 pm (UTC+0)
1 comment

Kungiyar Kwallon kafa Ta Chelsea Ta Ingila

‘Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea su na murnar lashe kofin zakarun kulob-kulob na Turai lokacin da suka koma gida Ingila, 20 Mayu 2012.


Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta Ingila ta sake cin moriyar lashe kofin zakarun kolob-kulob na Turaoi da ta yi kwanakin baya. A wannan karon, Gamayyar Kungiyoyin Kwallon Kafar Kasashen Turai, ta zabi Chelsea a zaman Kulob Din Turai Ta Wannan Shekara.
Roberto Di Matteo ya jagoranci ‘yan wasan nasa zuwa ga nasara kan Bayern Munich ta Jamus, kuma a filin wasan ‘yan Bayern, a wasan karshe na cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai.
Wannan sabon kambi da suka samu, ya kara jaddada irin yabon da suka sha a bayan da suka lashe kofin Zakarun Kulob-Kulob na Turai na farko a tarihin Chelsea.
Jiya litinin aka mikawa Chelsea wannan sabon Kambi na Kulob Din Turai Ta Shekara a wajen babban taron bayar da lambobin yabo na Gamayyar Kungiyoyin Kwallon Kafar Turai a Geneva a kasar Switzerland.
A wasannin lig-lig na Premier a Ingila, ‘yan wasan na Di matteo ba su taka rawar kirki ba domin su ne suka zo na 6 a bara.
Amma, Gamayyar ta fada cikin wata sanarwa cewa ta yi la’akari da “irin gagarumar nasarar da Chelsea ta samu a shekarar kwallo ta 2011-2012 a cikin gida da kuma a nahiyar ta Turai.”
Chelsea tana cikin Gamayyar Kungiyoyin Kwallon Kafar Turai (European Club Association) ko ECA a takaice, wadda ta maye gurbin wasu kungiyoyin hadakar kkwallon kafar Turai G14 da European Club Forum wadanda aka rushe su a 2008.
Wannan sabuwar lambar yabo, wani labarin en mai kyau ga Chelsea wadda a bana ta fara wasannin lig-lig na Premier da nasarori zalla.

Manchester United Ce Ta Daya A Duk Fadin Duniya

Posted July 18th, 2012 at 4:30 am (UTC+0)
Leave a comment

Magoya bayan manchester United su na jinjina ma 'yan wasansu a lokacin da suke shiga fili domin wani wasan sada zumunci da New England Revolution ranar 13 Yuli, 2011 a garin Foxboro dake Jihar Massachussetts a Amurka. manchester United ta lashe wasan da ci 4-1.

Magoya bayan manchester United su na jinjina ma ‘yan wasansu a lokacin da suke shiga fili domin wani wasan sada zumunci da New England Revolution ranar 13 Yuli, 2011 a garin Foxboro dake Jihar Massachussetts a Amurka. manchester United ta lashe wasan da ci 4-1.


Kamar yadda duk mai karanta wannan zai iya sani, kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta yi hasarar kambun Premier League na wannan shekara a ranar karshe ta wasannin lig-lig na Ingila, a lokacin da abokiyar hamayyarta Manchester City ta tsamo kitse a wuta a kan ‘yan wasan Queens Park Rangers a watan Mayu.
Amma har yanzu, kungiyar Manchester United ce take rike da wani da wani kambun: na Kungiyar Wasa Da Ta Fi daraja A Duniya Baki daya!. Kamfanin Forbes yayi kiyasin cewa a yanzu, darajar kungiyar Manchester United ta kai ta Dala Miliyan dubu biyu har ma da karin miliyan 230.
Kungiyar Wasa da ta zo ta biyu a duk duniya, ita ce Real Madrid ta kasar Spain, wadda aka kiyasta darajarta a kan Dala Miliyan dubu 1 da miliyan 880.
Da ma dai kungiyar Manchesater United ba bakuwa ba ce wajen rike wannan kambu na wadda ta fi daraja a duk duniya.
A bayan kudaden shiga da take samu na ‘yan kallo da telebijin da wasunsu, Manchester United tana samun wasu kudaden shiga kamar haka:
1. Kamfanin Inshora na Aon yana biyanta Dala miliyan 31 a shekara domina sa sunansa a jikin rigar ‘yan kwallon Man U.
2. A bara kamfanin DHL Express ya kulla yarjejeniyar sanya sunansa a jikin rigar furatis na Man U a kan dala miliyan 62 kowace shekara. Wannan shi ne karon farko da wani kamfani ya sayi damar sanya sunansa a jikin rigar furatis na kwallon kafa a Ingila.
3. Man U na samun abinda bai kasa dala miliyan 39 ba kowace shekara daga kamfanin NIKE wanda ke sayar da riguna da huluna da sauran abubuwan dake dauke da suna da tambarin Manchester United.
Wayne Rooney (dama) da Michael Carrick (hagu) dukkansu na kungiyar Manchester United kafin wasansu da kungiyar New England Revolution ta Amurka

Wayne Rooney (dama) da Michael Carrick (hagu) dukkansu na kungiyar Manchester United kafin wasansu da kungiyar New England Revolution ta Amurka

Zinedine Zidane Zai Koyar Da ‘Yan Wasan Faransa?

Posted July 4th, 2012 at 4:52 am (UTC+0)
Leave a comment

Zinedine Zidane, mai bayar da shawara ga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid (a dama) tare da kwach na kungiyar Jose Mourinho, lokacin wani taron 'yan jarida a Lyon ta kasar Faransa tun watan Fabrairun 2011. (Associated Press)

Zinedine Zidane, mai bayar da shawara ga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid (a dama) tare da kwach na kungiyar Jose Mourinho, lokacin wani taron ‘yan jarida a Lyon ta kasar Faransa tun watan Fabrairun 2011. (Associated Press)


Shugaban Hukumar Kwallon kafa ta Faransa yace Zinedine Zidane yana daya daga cikin mutanen da watan watarana zasu koyar da kungiyar kwallon kafa ta kasar, amma dai a yanzu kam ba shi zai maye gurbin Laurent Blanc wanda ya ajiye wannan mukami kwanakin baya ba.
Zidane yana daya daga cikin ‘yan wasan Tamaula da Faransawa suka fi karramawa, kasancewarsa yana cikin kungiyar kasar da ta lashe kofin duniya a 1998 da kuma kofin kasashen Turai na Euro a 2000. Yanzu dai shi ne darektan wasanni na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.
Zidane mai shekaru 40 da haihuwa, yana karatun difloma kan gudanar da harkokin wasanni a makarantar koyar da harkokin wasanni dake Limoges.
Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa, Noel Le Graet, yace yayi imani Zidane yana da kwarewa da hazakar zamowa mai koyar da wasanni na kungiyar kwallon kafar Faransa a nan gaba.
Le Graet, ya ci gaba da cewa, “babban abu ne cewa Zinedine Zidane ya bayyana sha’awar yin aiki tare da kungiyar kwallon kafa ta kasa ta Faransa a nan gaba, kuma idan hakan ba zai yiwu yanzu ba, yana kwadayin koyar da kungiyar ta kasa ko da nan da shekara goma ne.”
A yanzu dai kungiyar kwallon kafa ta Faransa, wadda aka fi sani da sunan Les Bleus ba ta da mai koyar da wasa a bayan da Laurent Blanc yayi murabus daga kan wannan mukami a karshen mako na sama. Ga shi kuma an fara shirye-shiryen gudanar da wasannin share fage na zuwa gasar cin kofin duniyar da za a yi a Brazil a 2014.

Wariyar Launin Fata – Ingila Ta Ce Zata Janye Daga Wasa Idan Aka Ci Mutuncin ‘Yan Wasanta Bakaken Fata

Posted June 11th, 2012 at 6:54 am (UTC+0)
2 comments

'Yan wasan Ingila su na motsa jiki a Donetzk, Ukraine, kafin wasan da zasu buga da Faransa litinin da maraice

'Yan wasan Ingila su na motsa jiki a Donetzk, Ukraine, kafin wasan da zasu buga da Faransa litinin da maraice


Kyaftin na kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila, Steven Gerrard, yace lallai idan har ‘yan kallo ko ‘yan wasan kasa suka kuskura suka nemi cin mutuncin ‘yan wasansu bakar fata, to ko ana tsakiyar wasa ne zai sa ‘yan kungiyar su fita su bar fili a wajen gasar cin kofin kasashen Turai, EURO 2012.
Kasashen dake daukar bakuncin wannan gasa, Poland da Ukraine, duk sun yi kaurin suna a saboda rahotannin cin mutuncin wasu jinsuna da nuna zunzurutun wariyar launin fata.
A lokacin da ‘yan wasan kasar Netherlands suke motsa jiki kafin wasansu na farko a wurin wannan gasa, an yi ta zagin bakaken fata a cikin ‘yan wasansu ana ce musu birai.
A ranar asabar ma, dan wasa daya tak bakar fata dake cikin ‘yan wasan kasar Czech, Theodor Gebre Selaisse, an yi ta muzanta shi a lokacin da suek bugawa da kasar Rasha.
Ingila ta ce ba zata yarda da wannan. Babban abinda ya fi damunta ma shi ne daga cikin ‘yan wasan kasar su 23, guda 8 bakar fata ne. Iyalansu da dama sun ki tafiya wurin kallon wasan saboda rahotannin cewa ana muzantawa wasu jinsuna a kasashen da ake gudanar da wannan gasa.
A yau litinin, Ingila zata kara da Faransa a Donetsk a kasar Ukraine, kuma kyaftin na Ingila Gerrard yace sun zauna sun tattauna matakan da zasu dauka idan aka nuna musu wariyar launin fata.
Kyaftin na kungiyar kwallon kafa ta Ingila, Steven Gerrard, wanda yace idan aka kuskura aka muzantawa 'yan wasansu bakar fata a gasar cin kofin kasashen Turai, EURO 2012, to zasu fita su bar filin wasa domin kasashen dake daukar nauyin gasar, Ukraine da Poland sun yi kaurin suna wajen cin mutuncin wasu jinsuna a fagen tamaula.

Kyaftin na kungiyar kwallon kafa ta Ingila, Steven Gerrard, wanda yace idan aka kuskura aka muzantawa 'yan wasansu bakar fata a gasar cin kofin kasashen Turai, EURO 2012, to zasu fita su bar filin wasa domin kasashen dake daukar nauyin gasar, Ukraine da Poland sun yi kaurin suna wajen cin mutuncin wasu jinsuna a fagen tamaula.


Gerrard yace idan har suka ga irin wannan muzanci, abinda zasu fara yi shi ne zasu tsayar da wasa su yi magana da alkalin wasan a kai. Idan ba su gamsu ba zasu fice daga filin.
Wasu shahararrun wasan Tamaula ma, kamar Ruud Gullit, tauraron kwallon kafa dan kasar Netherland wanda ya lashe kofin na Euro ma kasarsa a 1988, ya tofa albarkacin baki yana mai cewa, “Idan haka ya faru, bai kamata ‘yan wasa su rufe baki su ci gaba da wasa kamar yadda ya faru a zamaninmu ba. Idan har aka ci mutuncin wani saboda jinsinsa ko launin fatar jikinsa, wannan dan wasa yana da ikon ficewa daga cikin filin.”
Shi ma wani babban dan siyasa na Ingila, Douglas Alexander, yayi kira ga Gerrard da ‘yan wasan na Ingila da kada su ji tsoron tsayar da wasa, kuma in sun ga ficewa daga fili ita ce mafi a’ala, to ya kamata a goyi bayansu idan sun yi.”
Amma kuma babban abinda aka fi tsoro shi ne cewa irin wannan cin zarafi na wariyar launin fata watakila sai idan an zo wasa a tsakanin Ingila da mai masaukin baki Ukraine a wasa na karshe na rukuninsu.
Ingila ma ta tura karin kwararru kan harkokin tsaro domin tabbatar da lafiyar ‘yan wasanta, bakake da farare.

Wace Manchester Eden Hazard Zai Zaba?

Posted May 28th, 2012 at 1:45 am (UTC+0)
Leave a comment

Eden Hazard na kungiyar Lille a Faransa, na daya daga cikin 'yan wasan tamaula da ake zawarcinsu sosai yanzu haka a nahiyar Turai.

Eden Hazard na kungiyar Lille a Faransa, na daya daga cikin 'yan wasan tamaula da ake zawarcinsu sosai yanzu haka a nahiyar Turai.


Har yanzu Eden Hazard na kungiyar Lille dake neman sabon kulob bai bayyana inda ya fi so ya dosa ba, amma masu zawarcinsa sun yi yawa, cikinsu har da kungiyoyin kwallon kafa guda biyu dake birnin Manchester: City da United.
Ita ma sabuwar zakarar tamaula ta nahiyar Turai, Chelsea ta Ingila, tana cikin masu zawarcin Hazard.
Amma duk da haka, dan wasan baya na Manchester United, Patrice Evra, yace idan har Hazard yana neman ya shiga sahun kungiyar da zata samar masa da kofi ne nan gaba, to ya doshi Manchester, amma kuma ba Manchester City ba, Manchester United!
Evra ya ce, “Ni ba babansa ba ne, amma idan yazo shi Manchester ina tabbatar masa cewa zai lashe kofuna. Amma fa idan ya shiga Manchester da nake ba daya Manchester shudiya ba.”
Manchester City da Manchester United duk sun gabatar masa da tayin yazo yayi musu wasa.
Har yanzu dai Hazard bai fadi inda ya fi son zuwa ba, sai dai yace yana so ne ya koma kungiyar da zata ba shi sukunin taka rawar da ya fi so a fagen tamaula: watau dan wasan tsakiya kuma mai kai farmaki.
Watau mai rarraba kwallo a gaba!
Hazard ya ce, “na jefa kwallaye 20 a raga lokacin wasannin lig-lig (na Faransa), na kuma kasance wanda ya fi bayarda kwallon da ake jefawa a raga fiye da kowane dan wasa a lig. Babu ta yadda zan iya bayarda irin wannan gagarumar gudumawa idan mai koyar da wasa namu na Lille bai canja mini matsayi a fagen kwallo na koma inda na fi so ba.”
yace abinda yake nema ke nan yanzu a duk kulob din da zai je, domin kwadayinsa da ma ya rika buga matsayi na 10 a fili, ya kuma sanya riga mai lamba 10. Yace wannan batu yana daya daga cikin abubuwan da zai nazarta kafin ya yanke shawarar kungiyar da zai yarda ya buga ma kwallo.

Laifin Bayern Munich Ne – Ba Gwanintar Chelsea Ba

Posted May 21st, 2012 at 5:47 am (UTC+0)
4 comments

Anatoliy Tymoshchuk na Bayern Munich, a tsakiya, tare da sauran 'yan kungiyar cike da bakin ciki a bayan da Didier Drogba ya buga fenaritin da ya ba Chelsea kofin zakarun kulob-kulob na Turai a Munich, asabar 19 Mayu 2012.

Anatoliy Tymoshchuk na Bayern Munich, a tsakiya, tare da sauran 'yan kungiyar cike da bakin ciki a bayan da Didier Drogba ya buga fenaritin da ya ba Chelsea kofin zakarun kulob-kulob na Turai a Munich, asabar 19 Mayu 2012.


Dan tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa zai buga.
Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta kasar Jamus ita ta jefa kanta cikin ukubar bakin ciki da radadin zuciya, bayan da ta watsar da babbar damar da ta samu ta yin abin tarihi a gasar cin kofin zakarun Turai, kuma a cikin filin wasanta, a gaban magoya bayanta.
Bayern ta yi sakaci ta bar Chelsea ta rama kwallo ana saura minti biyu rak a tashi, sannan ta jefar da bugun fenariti a lokacin da aka yi karin lokaci, ta kuma zo ta jefar da wasu fenaritin guda biyu, ta bar kofin ya sulale daga hannunta.
Wannan lamarin ya faru ne a filin wasan ‘yan Bayern Munich, watau Allianz Arena, wanda aka zaba don buga wannan wasa fiye da shekara guda da ta shige, tun ma ba a san ko su wanene zasu buga ba. Idan da Bayern ta yi nasara, to da ta zamo kungiyar farko da zata lashe kofin zakarun kulob na Turai a cikin filin wasanta. Tun da aka kirkiro wannan gasa shekaru 20 da suka shige, babu kungiyar da ta taba yi.
Roberto Di Matteo na Chelsea yace, “idan wasa yayi zafi, komai na iya faruwa, tilas ka matsa lamba a kan abokiyar karawarku don ka ga abinda zai faru.”
Kowa ya san kungiyoyin kasar Jamus a zaman babu wanda ya kai su juriya da daukar matsi ba tare da nuna zafin kai ba. Kai, ba a taba doke kungiyar kwallon kafa ta kasar Jamus a bugun fenariti ba yau fiye da shekaru 30.
Amma ‘yan kungiyar Bayern sun karaya a lokacin da bai kamata su karaya ba. Kada a mance kungiyar ta yi hasarar kofin wasannin lig-lig na Bundesliga, da kuma kofin kalubalenka na kasar jamus. Ga na Turai ma ya sullube mata, a gaban magoya bayanta, a filinta, a garinta, kuma a kasarta.
'Yan wasan Chelsea su na fareti, yayin da Didier drogba ke rike da kofin zakarun kulob-kulob na Turai, bayan da suka doke Bayern Munich ranar asabar.

'Yan wasan Chelsea su na fareti, yayin da Didier drogba ke rike da kofin zakarun kulob-kulob na Turai, bayan da suka doke Bayern Munich ranar asabar.


ba dai zan cika ku da surutu ba. A karshe, haka ‘yan wasan Bayern suka zube a kasa, su na cikin tsananin bakin ciki da kukar zuci, ganin yadda wannan kofi ya shiga hannunsu ya sullube tun kafin su rike shi.

Manchester City Ta Tsamo Kitse A Wuta

Posted May 13th, 2012 at 11:16 pm (UTC+0)
1 comment

'Yan wasan Manchester City su na murna dauke da kofin zakarun wasannin lig-lig na kasar Ingila, bayan da suka doke Queens Park Rangers, yau lahadi 13 Mayu 2012.

'Yan wasan Manchester City su na murna dauke da kofin zakarun wasannin lig-lig na kasar Ingila, bayan da suka doke Queens Park Rangers, yau lahadi 13 Mayu 2012.


Magoya bayan kungiyar Manchester City sun fara kuka, duniya ta rikice musu ana dab da tashi daga wasan da suka yi da Queens Park Rangers a filin wasa na Etihad dake birnin Manchester.
A can Sunderland kuwa, magoya bayan Manchester United sai murna suke yi, ‘yan wasansu kuma har sun fara layi su na jiran a zo a mika musu kofin zakarun wasannin lig-lig na Premier.
A daidai lokacin, kungiyar Queens Park Rangers tana gaban Manchester City da ci 2-1. Kuma idan aka tashi a haka, mafarkin Manchester City na lashe kofin lig a bana, sai dai a mafarkin kawai.
Amma mutum yana nasa, Allah Yana nasa. Babu wanda ya san cewa a she a cikin mintoci 5 da aka kara na bata lokaci, manchester City zata jefa kwallaye har guda biyu, zata lashe wannan wasa, kuma reshe zai juya da mujiya: magoya bayanta za su barke da murna, yayin da magoya bayan United za su shiga cikin bakin ciki.
Da farko dai Edin Dzeko ya jefa kwallo da kai a lokacin bugun kwana, daga nan kuma ana saura dakikoki kadan a hura tashi baki daya sai Sergio Aguero, surukin Maradona, ya jefa kwallon da watakila a duk rayuwarsa bai taba jefa mai muhimmancin wannan ba. Ga ‘yan City dai wannan kwallon ya fiye musu komai a duniya a yau din nan.
Jefa wannan kwallo ke da wuya sai aka hura tashi, fili ya rikice, duniya ta koma fari fat ga ‘yan City, yayin da ta yi duhu wuluk ga ‘yan United har ma da ‘yan wasan United da manajansu Sir Alex Ferguson, wadanda shirinsu na amsar wannan kofi ya koma mamaki mai tsanani na yadda aka yi har City ta komo ta lashe wannan kwallo nata da QPR.
Wannan shi ne karon farko da City ta lashe kofin wasannin lig-lig na Ingila a cikin shekaru 44. Tun ma da wasannin suka koma Premier League, ba ta taba lashewa ba, kullum sai dai ta kalli makwabtanta ‘yan United su na murna.

Wannan rana ce mai muhimmanci ga manajan ‘yan Manchester City, Roberto Mancini, wanda aka yi ta rade-radin cewa masu kungiyar larabawa zasu kore shi idan ba su lashe kofin nan ba. Dalili shi ne irin makudan kudaden da suka kashe kan kungiyar domin farfado da ita.
Da ma kwararru suka ce lashe kofin farko shi ne mawuyaci, kamar yadda ‘yan City suka gani. Watakila na biyu da na ukun su na iya zuwa da sauki fiye da yadda suka gani a bana.
Manajan Manchester City, Roberto Mancini, rike da kofin zakarun wasannin lig-lig na English Premier da 'yan wasansa suka lashe yau lahadi, 13 Mayu 2012 a filin wasa na Etihad dake Manchester.

Manajan Manchester City, Roberto Mancini, rike da kofin zakarun wasannin lig-lig na English Premier da 'yan wasansa suka lashe yau lahadi, 13 Mayu 2012 a filin wasa na Etihad dake Manchester.

Up Yaya Toure – Sir Alex Ferguson Ma Ya Mika Wuya, Ko Kusan Hakan

Posted May 8th, 2012 at 1:36 am (UTC+0)
2 comments

Yaya Toure na Manchester City yana murnar daya daga cikin kwallaye biyu da ya jefa a ragar 'yan wasan Newcastle United a wasan da suka buga ranar lahadi, 6 Mayu, 2012 a filin wasa na Sports Direct Arena, Newcastle, wanda ya gusar da City ga lashe kofin lig-lig na EPL na 2012.

Yaya Toure na Manchester City yana murnar daya daga cikin kwallaye biyu da ya jefa a ragar 'yan wasan Newcastle United a wasan da suka buga ranar lahadi, 6 Mayu, 2012 a filin wasa na Sports Direct Arena, Newcastle, wanda ya gusar da City ga lashe kofin lig-lig na EPL na 2012.

Idan ba wata kaddara daga Ubangiji ba, babu abinda zai hana Manchester City doke Manchester United wajen lashe kofin wasannin lig-lig na bana a kasar Ingila.
Shi kansa manajan United, Sir Alex Ferguson, cewa yayi, “watakila hannayensu biyu na kan wannan kofi a yanzu haka.”
Tauraron ‘yan wasan Manchester City shi ne Yaya Toure, wanda a ranar lahadi 6 Mayu 2012, ya jefa kwallaye har biyu a ragar ‘yan wasan kungiyar Newcastle United, ya kawar da duk wata tababar da ake yi cewa bana taurarin City ne suke haskakawa.
Yanzu abinda ya rage kawai shi ne City ta doke kungiyar Queens Park Rangers wadda ke can baya a wasan karshe da zata buga ranar lahadi mai zuwa. Idan ta yi haka, zata lashe kofinta na farko tun 1968.
Idan City ta doke QPR, to United zata bukaci lashe wasanta na karshe da ‘yan Sunderland da ci 9 da babu, domin ta kawar da yawan kwallayen da City ke da shi a ragar abokan karawarta, abinda ake ganin zai yi wuya.
Hausawa suka ce ba a san ma ci tuwo ba sai miya ta kare.

 

Allah Ya Jikan Rashid Yekini, Mun Yi Rashi

Posted May 7th, 2012 at 4:22 am (UTC+0)
20 comments

Rashid Yekini, lokacin da ya jefa ma Najeriya kwallonta na farko a gasar cin kofin duniya a 1994.

Rashid Yekini, lokacin da ya jefa ma Najeriya kwallonta na farko a gasar cin kofin duniya a 1994.


Duk wani masoyin Najeriya da kwallon kafa a Najeriya da Afirka, ba zai taba mantawa da Rashid Yekini ba.
Rashid Yekini, ya rasu ranar jumma’a a Ibadan, yana da shekaru 48 da haihuwa.
Babu wani dan kwallon da ya taba jefa ma Najeriya kwallaye kamarsa, inda a cikin wasanni 58 da ya buga ma kungiyar Super Eagles, ya jefa kwallaye har 37.
Amma babban abinda mutane suka fi tunawa a game da Rashid Yekini, wanda aka haifa ranar 23 ga watan Oktoba, 1963 a Kaduna, shi ne irin rugawa da gudun da yayi ya shiga cikin ragar ‘yan kasar Bulgariya, ya rike raga yana ihu da iyakar karfinsa, a bayan da ya jefa ma Najeriya kwallonta na farko a gasar cin kofin kwallon kafar duniya a 1994 a Amurka.
haka kuma, Rashid Yekini, shi ne dan Najeriya na farko da aka taba zaba a matsayin zakaran kwallon kafa na nahiyar Afirka a 1993, kuma shekara daya bayan wannan, ya taimakawa ‘yan Super Eagles na Najeriya suka ciwo kofin zakarun kasashen Afirka.
Shi ne dan wasan da ya fi jefa kwallaye cikin raga a wasannin lig-lig na kasar Portugal a 1993-1994 a lokacin da yake buga wasa ma kungiyar Vitoria Setubal. A shekaru 4 da yayi a wannan kulob, Rashid Yekini ya jefa kwallaye 90 cikin raga.
Yayi wasa a kasashe da dama kafin ya zo yayi ritaya a kungiyar Julius Berger ta Najeriya a 2003.
A bayan fage, Rashid Yekini mutum ne mai shiru-shiru, wanda bai cika shiga harkar da ba tasa ba. Abin koyi ga kowa.
Allah Ya jikan Rashid Yekini, Ya sa mutuwa hutu ne gare shi, amin summa amin.
Marigayi Rashid Yekini

Marigayi Rashid Yekini

About

Shafin Tamaular Duniya

Dandalin wadanda ke sha’awa, kuma suka san abinda zasu iya fada kan kwallon kafa. Yaro ba ya wargi!!

Categories

Calendar

September 2024
M T W T F S S
« Feb    
 1
2345678
9101112131415
16171819202122
23242526272829
30