Manchester City ko Manchester United?

Posted February 24th, 2012 at 9:22 pm (UTC+0)
5 comments

David Silva na Manchester City (dama) yana kokarin kwace kwallo daga kafar Wayne Rooney na Manchester United a karawar da suka yi na gasar cin Kofin FA a filin wasan Etihad dake birnin Manchester, Ingila, ran Lahadi 8 Janairu 2012.

David Silva na Manchester City (dama) yana kokarin kwace kwallo daga kafar Wayne Rooney na Manchester United a karawar da suka yi na gasar cin Kofin FA a filin wasan Etihad dake birnin Manchester, Ingila, ran Lahadi 8 Janairu 2012.


Maki biyu kadai ya raba tsakanin kungiyoyin kwallon kafa guda biyu dake sama a wasannin Premier League na Ingila, makwabtan juna kuma ‘yan gari guda Manchester City da Manchester United. Ga shi an riga an buga kimanin kashi biyu cikin uku na wasannin.
A zane a takarda, sai mutum ya ga kamar Manchester United ba zata iya share maki biyu da ‘yan City suka ba ta rata da su ba. Misali, idan aka dubi wasanni shida dake tafe na kungiyoyin biyu, United zata kara da kungiyoyi biyu dake cikin guda 10 na saman wannan rukunin Premier, watau Norwich City da Tottenham, yayin da City zata kara da guda ce kawai watau Chelsea. Amma ba ta nan take ba.
An san Man U da bayarda mamaki a wasu lokutan. Kuma ga shi City tana fama da matsalar Carlos Tevez, koda yake Roberto Mancini ya furta cewa shi ba ya da matsala da dan wasan gaban, kuma zai iya komowa cikin mako biyu ko uku.
Af, ga shi kuma dukkansu biyu zasu sake haduwa a gasar cin kofin kasashen Turai ta Europa League, wasan da manyan kungiyoyi irinsu a can baya suke rainawa.
Hausawa suka ce ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.
A wanne kuke: Manchester City ko Manchester United?

5 responses to “Manchester City ko Manchester United?”

  1. Manchester united uwa ma ba da mama tabbas in ka saba ma sai ka daure.gaba gaba dai man-u

  2. Mohammed 'Dan India says:

    Kowa na iya lashe wannan gasar cikin su 2.Kai har ma da Tottenham kada mu cire tsammanin ita ma ta na cikin jerin masu iya lashe wannan gasa ganin cewar maki 7 ne kawai ke tsakain ta da Manchester City wato 5 kenan a tsakanin ta da United.Sabida haka ni a nawa ra’ayin su su ukun ne ke da damar lashe wannan gasa domin komai na iya sakewa a saura wasanni 12 da su ka rage.Ni ba na la’akari da wace kungiya ce za’a kara da ita a gida wace ce kuma a wajen gida,domin mun ga inda Manchester ta bi Arsenal har gida ta mata ci 7,mun kuma ga inda Manchester City ta bi United har gida ta tsira da maki ukun,mun kuma ga Blackburn ta ci united a old trafford yayin da Aston villa ta bi Chelsea har gida ta yi mata dukan kawo wuka.Zance cewar Manchester City na fama da matsalar Teves kuwa ni ban dauke hakan a matsayin matsala ba domin kungiyar ta riga ta nuna cewar ko da Teves ko babu shi za ta ci gaba da murza leda fiye da yadda a ke zato.Ko da ya ke yanzu Teves ya amsa kuskuren sa ya kuma ba da hakuri inda a ke sa ran nan ba da jimawa ba zai dawo taka wa kungiyar leda……

  3. Hum malam ibrahim ai basan maci tuwo ba, sai miya takare! Alamun kiba kuma tana ga mai karfi…… Kuma wasa tsakanin city da united fa, yatakaya ne? Kuma ga city nada matsalar shigowa emirates ga uwa uba masu masassarar dare !

  4. Bello Yerima says:

    Ha ba wake maganan manchester city, saura musu wasa biyu,don kwace goruba a hanun kutura bashi da wahala.

  5. Bala dahiru hassan says:

    Ai masu iya magana nacewa idan giya tayi tsami sai manyan mashaya man u ba kanwan lasa bane aci gabada wasa za’agane maci towo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

About

Shafin Tamaular Duniya

Dandalin wadanda ke sha’awa, kuma suka san abinda zasu iya fada kan kwallon kafa. Yaro ba ya wargi!!

Categories

Calendar

February 2012
M T W T F S S
    Mar »
 12345
6789101112
13141516171819
20212223242526
272829